BABI NA SHIDA.

472 51 6
                                    

EWF*
GIDAN AURE NA
🎪🎪

*Ƙarƙashin jagorancin Grps guda Huɗu! masarautan Mata 1/2. SBL TSK! EXQUISITE WRITERS FORUM.... Zai cigaba da zuwa muku kullum Insha Allah*

Labarin Sameerah.
Season 1
BABI NA SHIDA.

      Duk da tana bin malamai amma akan shi taki bin malamai,domin tace babu amfanin kashe Kudinta akan mutumin da bai da alkibla, tana son fakewa da inuwar auren shi. Takara cigaban alamuranta.

       Kamar yadda akewa kowacce amarya haka Faruq ya biyar da ita, babban abin da ya kuma burge ta da shi ba laifi ya iya bada kulawa a gado, dan haka zata rike shi hannu bibbiyu, ba zata yi wasa da shi ba dan kar ya subuce mata, lallai matar shi tayi hakuri ina zata iya daukar wannan shirmen wallahi ba zata tab'a yarda tana Kaduna mijinta yana Zari'a ba, ai alo kuturu alo makaho. Dan haka ta kuma shan alwashin koda zata raba shi da kowa na shi ba zata iya raba shi da matar shi ba, dan taba san kalar wahalar da taci dashi kafin yau da ta same shi a sama ta ka ba, amma sai ta duba taga matar wacce iri ce dan kar ta yi sake kuma ta mata halin uwargidaye.

       A cikin satin amarci sosai aka murza, duk da Hajjo ba budurwa bace, kuma ba a saka ta a layin zawarawa ba, sai dai ta san kan da namiji, ta iya sarrafa shi kamar ya zauce, haka ba karamin dad'i yayiwa faru ba, ya manta da duniyar Sameerah da Yaranta, ya manta da kowa sai ita. Idan ya shigo gida ka'ida ne zai kashe wayar shi, idan kuma ya sake wayar tayi kara toh wallahi zai ga rashin mutunci iya ganin idanun shi. Dan karfafa ce sai a ta iya make shi babu wanda zai kwace shi. Kullum da salo salo na musamman da take mishi haka suka kwashe mako biyu suna jiyar da juna soyayya. Sannan ya koma aikin shi.
**
    Wasa farin girki.
Tun daga ranar da muka yi waya da Faruq na bashi hakuri, yau sati biyu kenan babu shi babu alamar shi, abin tun yana bani mamaki har na daina mamaki,. A cikin gidan kuwa kowa yada min magana yake tare da min kallon me bakin kishi, Aikina da kasuwancin da nake ya sha kaina.  Kuɗin Mommy na had'a mata ina kallon kudin baki daya dubu dari da ashirin ne ya dace na had'a mata, amma gashi nan babu dubu hamsin, saba'in ne baki daya a hannu, baki daya na rasa yadda zan yi. Kuma ban samu albashi ba dan tun wancan satin ya dace na bata Kudinta amma haka bai samu ba, gashi mutane sai tambaya suke akwai kaya ne, ajiyar zuciya na sauke tare da dauko wayata. Na nimo Number shi na kira. Kamar ba zai dauka ba, ya kuma dauka yana dake murya.
"Assalamu alaikum, Barka da rana."
"Waalaikumun Salam, Barka dai"
"Hmm! Dama kan kudin nan ne ko zaka turo min zan had'a mata Kudinta ne" na fada ina jiran me zai ce.
"Sameerah dan kin bani aron kudi shine zaki addabi rayuwata da tambaya? Meye ban miki ba? Meye ban nuna miki ba? Wai me yasa baki da hankali ne, sai kiyi yi abu kamar dabba, wannan ai halin maguzanci ne, ban da jahilci yaushe na tab'a karban aron kudinki har zaki dame ni na dawo miki dashi, wawuya jaka wacce bata san halaccin rayuwa ba, dalla turo min account dinki na dawo miki da kudin tsiyar auren Yar mace kenan!"
"Nagode sosai Faruq" na fada mishi tare da kashe wayar. Nayi shiru kalaman shi suna dawo min kai ban san lokacin da kuka ya kwace min ba, haka na sha kuka na koshi. Shigowar Nuratu yasani goge fuska na.
"Ammyn meke damun ki?"
"Babu kome Baby na?" Na fada mata, bana son damuwar da nake ciki ya shafi Rayuwar Yarana, domin baki daya zai iya sakawa su kalli mahaifin su a matsayin mugu. Soyayyar da suke mishi ta koma k'iyayya.

   Bana son su zarge shi da mara adalci kuma ma asalima bana son su dauki kowani namiji mugu ne irin Baban su. Dan haka na zauna da ita ina mata hira tare da nuna mata wasu abubuwan masu muhimmanci na. Ina kuma gaya mata rayuwa tana da matukar muhimmanci a gare mu musamman idan ka rike hakuri.

        Yadda nake gaya mata girman hakuri da juriya, yasa ta kwantar da kanta a kirjina, a hankali Nimrah itama ta shigo ta kwanta a jikina, sannan can Amir ya shigo shima, a nan muna shantake sai barci. Wani abu da na fahimta shine Yaran ka sun ishe ka farin cikin, dan haka ban kuma bin takan shi ba.

GIDAN Aure Na..!!?Where stories live. Discover now