https://chat.whatsapp.com/EYIYhgb3RyPKaig0QHrOxR
*EWF*
GIDAN AURE NA
🎪🎪*Ƙarƙashin jagorancin Grps guda Huɗu! masarautan Mata 1/2. SBL TSK! EXQUISITE WRITERS FORUM.... Zai cigaba da zuwa muku kullum Insha Allah*
Labarin Sameerah.
Season 1
BABI NA BIYAR.Mai_Dambu.
Idanuna ne suka cika da kwalla, na sunkuyar da kai kasa ina wasa da hannuna.
"Hmm, na san ba zaki yarda dani ba, amma wallhi zanyi gyaran mota ta ce, kuma.." wayar shi ce tayi kara, kamar mara gaskiya ya dauki wayar yana faɗin.
"Kiyi hakuri mana ai nace zan baki"
Ya kashe wayar bayan ya zuba min ido, yaga har lokacin kaina a sunkuye yake.
"Meerah" rabon da ya kirani da wannan sunan shekaru goma sha ɗaya baya, d'ago kai nayi ina kallon shi.
"Nasan ba motar zaka gyara ba."Na fada ina kallon shi, rike zanin gadon sa nake zaune a kai nayi ina jin wani abu na taso min, amma haka na sunkuyar da kaina ina sauke ajiyar zuciya.
"Eh haka ne, kudin inda zata kama gurin da." Yadda na d'ago kai na kalle shi ya sashi had'iye maganar. Riko hannuna yayi tare da cewa.
"Nasan nayi laifi Please kiyi hakuri. Insha Allah zan gyara And ki bani last chance ma gyara halina, don Allah ki taimaka min na fita kunya." Kai na a sunkuye ban ce cikan ka ba. Ganin yana ta bani hakuri naki magana, ya sashi sauka a bakin gadon ya zube gwiwar shi a kasa, yana me rike hannuna duk biyu, yana share kwalla. Wallahi ban san lokacin da kwalla suka cika min idanuna ba, na bude baki zan mishi magana yace min."Ki yarda dani wallahi ba zan kuma ba" kallon shi nayi tare da cewa.
"Yanzun idan."
"Wallahi Tallahi ba zan kuma ba na rantse da Allah ba zaki kuma, samun matsala dani ba, ki yarda dani" baki daya kura mishi ido nayi ina son bashi ina tsoron bashi, baki daya na shiga rud'ani, asalima kudin ba nawa bane kudin Mommy ne, idan na dauka na bashi tazo tana bukata ya zanyi da ita? Baki daya na rasa mafita, haka nayi ta jin shi yana rantse rantsen shi har ya gaji ya mike tare da barin d'akin. Ban bashi ba kuma ban tsayar da magana daya ba. Ina zaune a gurin har kusan karfe ɗaya. Tashi nayi na shiga ban daki nayi alola sannan na fito. Na shimfid'a abin sallah, nayi kamar yadda na saba kullum. Sannan na zauna ina addu'o'in. Haka kawai naji a raina na bashi. Ban yi addu'a akan haka ba, ban nime zabin Allah akan shi ba, kawai zuciyata ce tayi na'am da haka, a hankali na mike tare da jan drowe side bed, na ciro kudin a hankali dubu tamanin da biyar ne. Akan ranar Monday zan kai banki, kirga kudin nayi sannan na cire dubu Hamsin na fito har falo. Dakin shi na nufa yana zaune ya zabga tagumi. A hankali na isa gefen shi na ajiye mishi kudin na fita. Bin bayana yayi da idanu, a hankali ya dauki kudin tare da sauke ajiyar zuciya yana jin lallai ya taki Sa'a dan bai san yadda zasu kare da Hajjo ba.Lokacin da na koma daki na fashe da kuka, tare da jin wani abu ya tokare min kirjina, kwanciya nayi tare da saka filo a kirjina ina kuka me mugun cin rai. Haka nayi barci a wurin sallah farko na farka, na shiga ban daki nayi alola, ina fitowa Faruq ya shigo cikin shirin shi, zai tafi Kaduna domin daurin auren shi. Dauke kai nayi ina me daukar hijab dina, ban san ya akayi ba sai jin shi nayi ya rungume ni ta baya, sosai ya rungume ni. Tare da cewa.
"Nagode sosai kin fitar dani kunya." Ban ce kome ba, wani irin yanayi na shiga baki daya ya manta da hakkina da yake kan shi ya samu abinda yake bukata ya juya zai tafi. Kamar nayi mishi magana sai kuma na fasa, na kyale shi yayi tafiyar shi sai a lokacin na samu kwarin gwiwar kuka sosai. Mata dubu nawa suke cikin matsala kamar Ni? Mata nawa suke zubda hawayen akan maza? Shin Ni daya ce ko akwai wasu matan a duniya? Me yasa duniya bata fahimtar halin da muke ciki? Idan har mace tayi kuskuren ba a duba halin da aka cillata. Wani hucin kuka na sake tare da kallon dakin babu kowa, har ya tafi abin shi domin ina jin mahaifiyar shi tana cewa.
"Allah ya tsare a gaishe da Hajjo, Allah bada zaman lafiya"
"Amin, Amin" ya fada tare da barin gidan, da sauri. Haka na wuni a d'akina domin ko aiki ban samu zuwa ba, na dai turawa abokan aikina bani da lafiya, ina nan zaune wajen karfe sha daya naji ana ta rangad'a gud'a. Wai ana can an daura aure, ni na zata ranar Asabar ce ashe wai juma'a ce, a raina na musu fatan zaman lafiya sannan na cigaba da uzurina. Ban san me yasa nake son nayi nesa da Faruq. Ko dan haka sauran matan da aka musu kishiya suke ji ban sani ba. Sai dai naji wani abu ya tokare min kirjina. Bana jin dadin kaina bana jin dadin yadda rayuwata take tafiya.Ban kuma sarewa da dangin mijina ba, sai da Gwaggon tasallah ta zo har bakin kofar d'akina tace min.
"Ke Samirah haka ake a garin ku? Ai kyayi hakuri ko b'oye halin ki idan yaso daga baya sai ki nuna musu halinki na mugun kishi, sakarai kowa a cikin gidan fadar mugun halin ki yake ke kam baki ji dadin ki ba."Yadda take fadar abin da yake bakinta ya sani sunkuyar da kaina kasa har ta gama ta sake labulen kofar, kwalla ne ya zubo min. Ina zaune har wajen karfe sha biyu, na tashi nayi girki. Bayan na gama nayi wanka tare da shiryawa cikin atamfar English me yakuwa, na fito falona da na kuma gyara shi na saka turaren wuta yar Maiduguri. Na zauna a wurin na saka cin abinci, kai na a sunkuye. Fitowar Amir daga dakina ya sani mik'ewa nayi nufi ban daki da shi na mishi wanka na saka mishi kayan shi, sannan na fito da shi falo na bashi abinci har.
Karfe biyu daidai, Yahanasu ta dawo dasu Nuratu, nan ta kalle ni tare da cewa.
"Aunty Suna ta bikin su"
"Eh." Na bata amsa a takaice,
"Ammyn wai Abba zai yi aure ne?" Nimrah ta tambaye ni, murmushi nayi tare da shafa kanta na ce.
"Maza yan matan Ammyn su tafi su saka kaya, amma make sure kun watsa ruwa." Na fada ina shafa kan su,Yarana suna da matukar fahimtar abu, amma wannan karon na hanasu fahimtar me Ubansu yake min, kuma naki yardan su ki Ubansu duk da wani lokaci ina jin suna fadar yadda suke kewar mahaifin su, haka ya sani kara jin tausayin sun. Haka zasu tashi suma mazajen su. Suna basu wahala? Haka zasu taso babu abinda suka sani sai hakuri da bautar miji. Eh mana bautar miji, tunda gashi nan haka nake a gidan Uban su. Dangin shi da shi kan shi sun rufe idanun su, suna azabtar dani da damuwa. Domin idan aka daura damuwa kawai toh haka ya wadatar da matsala ta.
Haka suka yi wunin su, washi gari kuwa ina zaune gwaggo ta shigo.
"Samirah? Auno min shinkafa mudu goma da manja da mangyada. Sannan ki had'a min da kifi ai nasan akwai." Ta fada min. Ban mata musu ba, na nufi store na kwaso mata abincin na kawo mata ban tab'a ba, nace mata.
"Gasu nan kuyi duk yadda yayi muku." Na juya na bar mata wurin. Jikinta ne yayi masifar sanyi, ganin yadda na ajiye mata kayan ina kwaso mata abin yayi mugun d'aga mata hankali, kasa aiwatar da kome tayi ta juya abinta, dakyar na daure. Ina fita naji suna ta yad'a magana wai nayi mata bakin hali. Ita da kayan D'anta na hanata, ban ce musu kome. Bayan sallah isha na zauna nayi ta kuka. Har na godewa Allah. Karar wayata naji na kalla. Number faruq na gani.
Dauka nayi tare da cewa.
"Lafiya?"
"Hmm! D'azun Gwaggo ta kirani wai kin ki basu abincin da zasu dafa?"
"Umar ka sayo da su ne na basu ko kuma ka sayo na wanda zamu na cin na gida? Idan kuma ɗan a dafa a bikin ne ok.""Hmm! Kiyi hakuri ba wani abu nace ba." Ya fada tare da kashe wayar, haka kawai naji ban kyauta mishi ba, kallon wayar ayi.
*Kayi hakuri!*
Na tura mishi, kusan abinka da namiji sai gashi da zungureriyar sakon shi na fadar na b'ata mishi rai dan naga na bashi aron kudi ne nake mishi rashin arziki ko, toh na turo da account ɗina ya dawo min da kudina.Haka kawai sai naji hankalina ya tashi na fara ƙoƙarin kiran shi na bashi hakuri mutumin nan yaki dauka, kamar nayi kuka ina son na mishi bayanin ai ba da gayya bace amma fir yaki dauka.
**
Kaduna.
Abokan shi har da Dan Ladi suka raka shi, yana ganin kiran Sameerah amma fir yaki dauka, bayan sun gama barkwace Amarya tana can lullube da mayafi, bayan sun gama abinda zasu yi. Suka musu sallama ya raka su ya dawo.Yana kallon yadda take wani cika tana batsewa. Mik'ewa kawarta me suna Ashanty tayi tana faɗin.
"Baby sai hakuri domin kin san da da yanzun daya bane, kuma bai zama dole ki samu yadda kike so ba, sai hakuri.""Hmm" ta fada tare da sunkuyar da kanta, bayan fitar kawarta ya zauna tare da kallonta.
"Kiyi hakuri, wallahi dakyar na samu dubu hamsin din."
"Kasan zaka kunyanta ni a gaban jama'a ka ce min na kama hall din dubu dari biyu, yau badan ina da su Ashanty ba waye zai rufa min asiri nayi danasanin biye maka har maganar aure ta shiga, dama an gaya min cewa ba zaka iya rike Ni ba, tunda Matarka ma baka rike ta ba." Kalaman b'atanci kala kala da maganar banza ta cakka mishi babu iyaka, Allah sarki Ubangiji kenan ba a zalumin sarki bane,sai gashi har da bata hakuri. Haka yayi ta lallabata.Hajjo irin tika tikan matan nan ne masu bin yan siyasa, dan wayewa ta waye sosai, domin ta tab'a harkan kano to Jidda, ta zauna a tafe dake Abuja, matar idanun ta kar yake da duniya, a yanzun ma tana tare da yan siyasa ne, kuma duk abinda take a gaban iyayenta take, ganin tana kara shekaru babu miji, shi yasa da Faruq yazo mata ta hanyar Dan Ladi, tayi maza ta rike shi. Hajjo bata da mutunci, abu daya da taki yi akan Faruq domin kuwa tayi bincike akan shi sosai da kuma matar shi, sai dai yadda taji labarin gidan su, tasha alwashin ba shegen da zai zo mata gida idan kuma yazo mata gida sai taci kaniyar shi.
*Wash yau na gaji dayawa*
YOU ARE READING
GIDAN Aure Na..!!?
Ficção GeralLabari ne da ya faru a gaske labari ne ta ya tab'a kowani shashi na rayuwar matan aure yan mata zawarawa, da sauran su( BASE OF TRUE LIFE STORY) KUMA SERIES NOVEL NE