https://www.wattpad.com/1145089602?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
*EWF*
GIDAN AURE NA
🎪🎪*Ƙarƙashin jagorancin Grps guda Huɗu! masarautan Mata 1/2. SBL TSK! EXQUISITE WRITERS FORUM.... Zai cigaba da zuwa muku kullum Insha Allah*
Labarin Sameerah.
Season 1
BABI NA TARASun kai awa daya suna buga kofar, babu alamar za a zo a bude musu, kafin Allah ya taimaka Hajjo ta bude kofar ta, domin har sun koma gefe suna kananun magana, da sauri suka iso bakin kofar suka tsaya, tana isowa bakin get din suka kara wani cuso kai, bude kofar tayi suka wani nufo kofar kamar zasu shige da ita, zare ido tayi tare da cewa.
"Malamai lafiya?"Tsilli tsilli suka yi da idanu suna kare mata kallo, musamman yadda ta sha mur, wato ta b'ata rai.
"Mu.. mu.. mu..." Sai aka rasa wanda zai bayyana kanshi gare ta, ya kuma bayyana mata daga inda suka fito sai famar Mu..mu.. suke domin tayi musu mugun Kwarjini."Zan juya ina da abin yi?" Ta faɗa da karfi.
"Hmm! Dama... Dama... Dama.." turo kofar da zata yi suka yi ta maza suka ce.
"Mu yan uwan shine wannan ita ce Kanwar shi Zaliha" suka nuna ta, sai zare ido take kamar wacce tayiwa sarki karya."Ayya! Ku shigo" ta nuna musu hanya, suka shiga cikin gidan suna faɗin.
"Kai Masha Allah" bata hana su ba, suka gama abinda zasu yi sannan suka shiga falonta, anan ma bata yi magana ba, ta wuce dakin ta.
Tun da suka shigo gidan ta wuce d'akinta matar nan bata kuma fitowa ba, sai da Kawayen ta yan bariki suka shigo gidan,tayi ta sauke abinci da manyan kululi suka ci suka yi aniyan, sannan ta kalli su Zaliha ta fita raka Kawayen ta, bayan ta dawo ta samu dan Jumai yayi mata fitsari a kan kafet, ai kuwa ta fara ruwan bala'i, kamar zata cire bakinta zunzurutun masifa da bala'i.
Su kuma tsoron haka ya saka suka cire guri guda, ta kara da cewa.
"Uwar me kuka zo yi? Ko an ce muku ni Sameerah ce za zaku zo ku min sata? Ku je ku tambayi Uwar shi itama ban mata da sauki ba,yan kutumar Uban. Ce muku aka yi ni Sameerah ce sai na ci mutuncin ku"
Yadda take masifar sai da suka rasa yadda zasu yi da ransu, kuma haka ta hana su abinci ta musu koran kare,bayan ta musu barazanar tijara har Zaria.Haka yayi masifar d'aga musu hankali gulmar da suka kunso basu samu idda gaya mata ba, kai haka suka juya babu kwarin gwiwa. A hanya kuwa babu wanda ya iya magana kowa ya bar abin a ranshi, Zaliha ce mai karfin halin cewa.
"Ba mamaki itace sanadin ciwon Gwaggo"
"Eh mana,ga biri yayi kama da mutum" suka fada tare da jinjina al'amarin. Sabuwa tace masu.
"Kenan taji labarin zaman mu da Sameerah kenan?"
"Eh ga zahiri, ai ba a bukatar ƙarin bayani, domin kan tun da ta iya sake magana haka ai bata shigo a banza ba." Inji Iyami,"Hmm! Lallai an daina kiwon dabba yanzun mutane ake kiwo wani munafukin ne ya zo ya gulmata mata, indai haka ne tayi mugun abu domin ta fadi babu nauyi!"
Haka suka yi ta zafin Hajjo basu lura da abin da suke aikatawa ba, gani suke kome suka yi ai daidai ne.
(A wannan zamanin abin da yake faruwa kenan a cikin al'umma, ka rasa gane meye kayiwa mutum ya tsane ka, ya tsani ganinka wallahi babu kome, zunzurutun karfin hassada ce da kyashi wanda ba a niman hanyar dakushe shi! Mace ce take murnan za ayiwa mace Yar uwarta kishiya! Kuma ɗan bakin ciki babu abin da tayi Miki kome ba zunzurutun bakin cikin karta rayu cikin salama da amincin Allah, wai me yasa muke da matsala ne? Kina zaune da mutum amma idan ya ganki shi zai fara bayyana hasaddar shi kan ki, babu gaira babu dalili zaki saka matar Dan uwanki a gaba sai kin raba ta da kwanciyar hankali zaki nutsu? Why? Me yasa baki duba Yaran da ta haifa da dan uwanki? A yanzun sai ka rasa me kayiwa mace ta tsane ka baki kaina bana kanki zaki ga tana fatan ki rasa jin dadi da rayuwar farin cikin.
YOU ARE READING
GIDAN Aure Na..!!?
General FictionLabari ne da ya faru a gaske labari ne ta ya tab'a kowani shashi na rayuwar matan aure yan mata zawarawa, da sauran su( BASE OF TRUE LIFE STORY) KUMA SERIES NOVEL NE