🅿️1️⃣0️⃣
Cikeda madaukakin farin ciki y qarasa d motarsa zuwa unguwar tudun Yola Dan ganin yafi kusa d sauran gidajensa.
D kansa y bude get din y shiga kasancewar b me gadi a gidan sedae akwae dukkan abin bukata kamar dae sauran gidajensa.
Library dinsa dake gidan y shiga y Adana abin d y dauko kana y shiga bedroom dinsa yayi wanka smn yai Alwala y tada sallah Dan it's already 4am har m d wasu mintuna.
Nafila yayi kana y dau Qur'an y a Fara karatu har aka Kira sallah snn y rufe y tashi yai rakaatanul fajr Kamar yadda manzan Allah (S.A.W) y koyar snn yai sallar asuba.
Wani irin nannauyan bacci n y ke dibarsa Dan d qyar y qarasa azkar dinsa snn y kwanta.
Bashi y tashi b se after 11am, a hanzarce y shirya snn y nufi library dinsa Dan Duba abinda ya dauko jiya Wanda in har y dace to fa tabbas y Fara shawo kan matsalolinsa.
Wani box n n karfe me sheqi ssae d zanen tsuntsu a jiki, sedae zanen a karkace yke Dan hk y Fara jerashi cikin nutsuwa Dan hkn shine mabudin akwatin.
Ajiyar zuciya y sauke bayan y Gama jerawar snn yai basmala y bude a hankali.
Babu komai aciki se wata nannadaddiyar takarda , wani irin bacin Rai ne y saukomasa ganin be Sami nasasar samun abinda take bukata b.
Sosae yake kokarin controlling zuciyarsa domin wani irin bugu take Kamar wadda zaat Faso kirjinsa t fito, idanunsad sukai jajir y runtse snn cikin daddar muryarsa y fara karanta suratul Yusuf.
A hankali a hankali mood dinsa yake daidaita har y koma normal Wanda yasan badan karatun b Baya tunanin akwae abinda ze daedaeta shi hk d sauri.
Seda yakai har suratul saffat snn y tsaya yayi addua snn y tashi y koma dakinsa.
Kamar Wanda aka zabura y miqe daga kan bed din d y zauna, d sauri y kawo jakarsa d y shigo da ita jiya y fito d wata Yar qaramar naura yai pressing wani madanni, Nan d Nan wata jar danja t Fara blinking.
"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun" shine abinda y ambata yane dafe kansa. Y akai hankalinsa be bashi hkn b se ynx?
D sauri y dauki jakar tashi tareda daura wani madaidaicin agogo kana y koma library din y dauki box din nn y fita daga gidan batareda yasa takalmi b shiga motarsa y fita a guje.
Gudu yake kamar Wanda ze tashi sama har ya iso dajin nn.
A gurguje y shiga gidan y zauna kana y Kira spy Dina dake matsayin dreban alhaj Isa y zo y dau motarsa y tafi d ita.
💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖
Gaba daya jinta take kamar Bata d lpy kwana biyun Nan Wanda Bata Raba dayan biyu rashinsa ne a cikin gidan y haifar Mata d kewarsa.
Juyi t sakeyi akan gadon tana sake matse pillow din d ta rungume, idanunta a lumshe kamar me bacci sedae ba baccin takeyi b, jitake kamar shi t rungume Wanda hkn yasa take sake kankame pillown hannunta duk bayan second daya.
A hankali t karfafawa kanta gwiwa t miqe t shiga toilet Tai wanka Dan yau wuni guda takasa komai se tunanin da Wanda hkn yasa har qarfe 2 n Rana Amma batayi wanka b.
Kayan Shan iska t dauko ta saka kana t koma t kwanta kasancewar tana fashin sallah.
Lissafi take yau saura 4 days y dawo Wanda ganinsu take Kamar 4 yrs saboda nisa.
Tarasa y akai y shiga zuciyarta haka d yawa duk kuwa d ba kasancewa suke a waje daya b sedae in yazo dubata, Wanda ko yazo din b wani fira suke b illa tambayar lafiyarta d yakeyi.
Lumshe idanunta tayi Dan b abinda take bukata illa yin tozali d kamilalliyar kyakkyawar fuskar sa me cikeda nutsuwa d kamalar d ke tafiya d daukacin tunaninta take Kuma taso Mata d wani irin shauqi.
"Pls k dawo tunkafin marainiyar zuciyata t fashe" t fada a hankali cikin wani irin sauti Wanda ita kanta batasan tana dshi b.
(Lol haneefa f t fola Mana 😝 #team_hanifa)
💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖
Hawayene ke zuba a fuskata b kakkautawa masu cikeda radadi kamar kunar wuta, gaba daya bazaka kalleta kace zata Sami damuwa b in akai Duba d kayan jikinta n dubban daruruwa tareda tanqamemen gidan d take ciki.
Bata tunanin a kwanakin Nan tana samun farin ciki ko misqala zarratin, damuwa ce tsantsa danqare a cikin zuciyarta Wanda in dae kaga wanzuwar murmushi a fuskarta sedae n yaqe.
Hannu tasa ta share ruwan dake gudana akan kuncinta kana ta daga hannunta sama sedae takasa cewa komai se fashewa tayi d wani matsanancin kuka wnada kana ji kasan meyi Yana cikin wani Hali.
Fiyeda minti 30 kafin t samu tayi calming din kanta kana tayi addu'o'i d yawa tareda nemawa Tsohon gwarzon mijinta gafara Kamar yaddata Saba.
Cikeda sanyin jiki t miqe daga kan abin sallar t zare hijab din jikinta kana ta ninke sallayar t maidata maajiyarta.
Gefen makeken bed dinta t zauna tana janyo wayarta Wanda haka kawae taji b abinda takeso samada Jin muryar gudan jininta.
Hannunta t Dora kan numbersa cikeda fargabar data rasa ta mecece sedae can qasan ranta fata take Allah yasa y dauka.
Ringing uku tayi y dauka tareda sallama, nannauyar ajiyar zuciya t sauke Jin daddar muryarsa a kunnenta kana t sassaita kanta Tai Masa magana.
"Imam kana lpy dae ko"
Shiru yayi n wani lkci Yana tuna yaushe rabon data Kira shi tana tambayar lafiyarsa, y mnta lkcin sedae tabbas yayi farin cikin Jin hkn ynx .
"Ina lpy, Ina kwana".
"Lpylao Khaleed, fatan dae baka d wata damuwa". Banbarakwai yaji abun Amma y dake y amasa
"Eh babu komai".
"Masha Allah, Dan Allah Banda sakaci d addua d karatun Qur'an, k ringa hqr d rayuwa domin b lallai n tazomaka yadda k tsammata b, juriya d jarumta suka sance abokan rayuwarka . Mahaifinka mutum ne me tausayi d taimakon nakasa dashi zanyi farin ciki in ka dauki halayyarsa. Abu na karshe k Zama me kula d sanin kanka, bance kazama Mara yarda b sedae be very vigilant don Haka kawae zuciyata ke bani kana cikin ko Kuma zaka iya shiga hadari, fatana Allah y kawo maka taimakonsa y baka nassara akan dukkan maqiyanka. At last kasani mahaifiyarka n matuqar sanka har fiyeda kanta".Tana fadar hkn t kashe wayar cikeda raunin zuciya Dan hk kawae takejin cewa danta Yana cikin matsala.
Hajiya AISHA knn mahifiya g imam Khaleed Ahmed Al~araby.
💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖
Khairert for life 💖
One luv😘.Domin Yin gyara or sharhi 09013101854.
Note_ only watsapp pls
YOU ARE READING
ƘASARMU A YAU! ✅
Romancewace irin rayuwa talaka keyi yayinda shuwagabannin kasar ke tattare duka arziqin qasar zuwa ga kansu kadae tare da iyalensu??? Tabbas rayuwan talakan QASARMU A YAUyana cikin halin matsi da rashin sanin makama. Duka Yan siyasar QASARMU sunayin komae...