🅿️2️⃣0️⃣
'''MANAZARTA WRITERS ASSOCATION''' 📚🖊️
*M.W.A**Kungiya d'aya tamkar da dubu, Masu Nazari da aiki da ilimi, burin 'kungiyar a ko yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da Masoyan ta.*🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________
_________________📖 kashegari da safe da kanta ta kirashi bayan tayi wanka ta na kwance a gado, kallon ɗakin takeyi lungu da saƙo duk da bata kirashi ba saida ta tabbatar ta hautsina CCTV camera din dake ɗakin ta yadda ranar bazata yi wani aiki ba.
Ringing ɗaya ya kashe ya biyo ta, tana kallon wayar na ringing amma bata ɗauka ba har sai da ta mutu ya sake kira.
Sallama tayi masa ya amsa kana ta gaida shi , amsawa yayi yana tambayar ta ya take amma ta bagarar da tambayar taƙi amsawa dan tana ganin meye amfanin wani tambayar ta da zaiyi bayan ya gama wulaƙantata jiya dan haka direct ta Fara maganar abinda yasa ta kirashi cikin ƙasa ƙasa da murya duk kuwa da tana da tabbacin ba wanda zai jita kasancewar ginin irin me ƙwarin nan ne.
"Ka duba wannan vedio ɗin sosai, ina tunanin zamu sami wani abun a cikin sa, naji yana maganar a kashe wani amma ban nutsu naji sunan mutumin da yake batun a kashe ɗin ba sai ka juyowa mana mukuma muyk iya yinmu wajen ganin yazo hannun mu dan da alama ya san wani sirri nasu mai mahimmanci, sannan da wata maganar Flash da naji ana cewa yana hannun baban budurwarka, ya kamata ka san hanyar da zaka bi dan sata ga ɗauko maka shi, ina tunanin wannan sune kawai abinda muka samu yanzu".
Murmushi ne kwance akan fuskarsa tun sadda ta kira sheerah da budurwar sa abinda ya manta rabon sa da yin murmushi kuma me faɗi haka, gyaran murya yayi kafin ta amsata
"Hakan za'ayi, insha Allah yanzu zan bi recording ɗin, maganar Flash kuwa karki damu, budurwata ba me wayo bace sata ta ɗauko shi baze yi wahala ba, kedai aikinki shine ki sata ku koma Abuja a gobe, dan bamu da isasshen lokaci saboda zaɓe da ke zuwa not too long Kuma ya kamata komai ya kasance kafin zaɓe ne, inkuma ba mu samu yadda muke so ba to bayan zaɓe da kaɗan".
"Ba matsala in Allah ya yarda, se anjima".
"Ehm jimana". Ya faɗa mata da sauri jin tana niyyar kashe wayar
"Ɗazu na tambayeki baki amsa min ba, fatan kina lafiya".
"Bacci nakeji, later".
Ta faɗa tana kashe wayar da sauri jin ze wani raina mata hankali, hararar wayar takeyi kai kace shine a gabanta kafin kuma ta duro daga saman gadon ta nufi ƙofa bayan ta saka hijab a jikinta.
Ɗakin sheerah ta shiga inda ta same ta sai lokacin take yin sallahn Asuba, agogo ta kalla wanda ya nuna ƙarfe 8:30am, girgiza kanta kawai tayi ta nemi bakin gado ta zauna tana jiran ta idar.
Gaisawa sukayi bayan ta idar kana ta ɗan mata nasiha sama sama akan barin sallar Asuba har rana ta fito kana ta ɗora da batun da ya kawo ta.
"Babe Ina tunanin fa nan da kwana biyar zan koma ƙasar mu".
Zaro ido sheerah tayi
"Kai haba dai, 3 weeks fa kika ce mun zakiyi"."Nima Haka naso, sai dai Daddy ya Matsa, dama fa da ƙyar ya barni yanzu kuma wai indawo zamuje Morocco gidan su Ammina".
"Au Ammin ki Yar Morocco ce? To Daddy fa?
"Eh Ammina Yar Morocco ce, Daddy kuma ɗan Pakistan ne".
Zuba mata ido sheerah tayi tana ƙare mata kallo a ranta tana ayyana shiyasa take da kyau har haka da yawa yayinda cikin Haneefa ya ke ƙululu na Allah yasa ƙaryarta ta karɓu.
YOU ARE READING
ƘASARMU A YAU! ✅
Romancewace irin rayuwa talaka keyi yayinda shuwagabannin kasar ke tattare duka arziqin qasar zuwa ga kansu kadae tare da iyalensu??? Tabbas rayuwan talakan QASARMU A YAUyana cikin halin matsi da rashin sanin makama. Duka Yan siyasar QASARMU sunayin komae...