🅿️2️⃣6️⃣
Bismillahir Rahmanur Raheem.
________________📖 karkarwa jikin sa ya fara yayinda yake nuna TV ɗin da hannun sa saidai ya kasa kuma cewa komai.
Tsayar da recording ɗin Haneefa tayi kana ta miƙe ta ruƙo Imam dake tsaye har lokacin jiki na rawa, be mata musu ba ya faɗa jikin ta tare da ƙanƙame ta kamar zai ɓalla ta yana sakin tagwayen ajiyar zuciya a jejjere.
A da zargi ne yake yi akan kisan mahaifinsa sai dai yanzu ko bai ƙara sa kalla ba ya tabbatar da su ne suka kashe masa mahaifi, runtse idanun sa yayi, bawai mutuwar ce ke damun sa ba har lokacin, a'a, tuno cewa a hannun wannan azzaluman baban sa ya rasu shi ne damuwar sa domin su dai ko gawar sa ba su sami gani ba.
A hankali ya zare ta daga jikin sa ya koma ya zauna tare da ɗaukar remote yai pressing play button, itama komawa tayi ta zauna suka kuma zubawa TVn ido.
Alh khaleel ne ya saka ƙafa ya dungure fuskar Alh Ahmed Al~Araby kana cikin wata murya me cike da izza da mugunta ya ke faɗin
"Ƙarshen tika tikin tik! Yau dai ga Al~Araby a ƙarƙashin ƙafar khaleel, khaleel ɗin da kace bazaka goyawa baya ya samu kujerar shugaban ƙasa ba saboda shi ɗin mugu ne, mai son kansa mara ilimin addini mara ilimin makamar tafiyar da jama'a....yen...yen...yen se me ma?
Ya ƙarshe yana dukan fuskar Abiey da ƙafarsa wanda take bakin sa ya fashe dan ba wai a hankali yai dukan ba, a'a ya zage iya ƙarfin sa ne dan ya huce haushin sa.
Alh Isah ne ya kece da dariya yana nuna Abiey da bakin sa ke ɗigar jini
"Kalli the mighty Al~Araby dake taƙama da kuɗi da fame Yana Mana gadara da musu yau gashi a ƙarƙashin ƙafar mu, zai mutu a ƙasƙance yayin da zan angon ce da matar gold ɗin sa da ya daɗe yana ɓoye wa ai shi mai wayo, uhmmm, chakwai, kai banga laifin ka ba da ganin ta zatai daɗin juyawa a gado".Wani irin ɗagowa Abiey yayi ya kafe Alh Isah da idanunsa da sukai jajir kana ya fara magana cikin tsananin fusata
"Kar ka fara Isah, na faɗa maka kar ka fara, na rantse da Ubangijin da numfashi na ke hannun sa in har idonka ya sauka kan matata se na ƙwaƙule maka shi".
"Kwantar da hankalin ka, Ni wannan ɗan tatsitsin ɗan naka nake so, da ganinsa zai bada cutar, gashi nan ɗan shila dashi kun san da Ni na fison maza". Chief judge Ezekiel ya faɗa yana wani shafa gabansa cike da salon iskanci.
"Ni dai in kaci matar tasa ka rage ina so, dama na daɗe ina haɗiyar miyau saboda wannan ɗan iskan good for nothing ɗin". Alh Mudi wanda yai maganar ya fashe da dariyar tura haushi ganin yadda Abiey ke kallonsu kamar ze cinye su da ido, su kansu sun san yau da ba'a ɗaure shi ba tabbas da se dai a ƙwace su".
"Alh Isah mai muke jira ne, kasan fa gobe za'a fara zaɓe, ya kamata muyi maza mu ɓatar da wannan matsalar tamu wato mu sheƙe wannan kawai".
Alh Isa ne ya miƙe tare da zare wata ƙaramar kakkaifar wuƙa yai kan Abiey da har lokacin kallonsu yake yi, sai da Alh Isah ya ƙara sa gabansa kafin Abiey ya saki wani tattausan murmushin ya fara magana
"Kuna tunanin in kuka kashe ni kun kawo ƙarshen matsalar ku ko? Kuna tunanin in bani zakuyi mulki san ranku ko, ku kwashi abin da kuke so yayinda talaka bai da yadda za yi daku ko? To tabbas kun kuskure, ku rubuta ku ajiye, na baku nan da shekara goma sha uku kuji daɗin ku, amma daga nan to fa matsalar ku zata fara ne, ina mai tabbatar muku da se kun nemi mafaka da gurin ɓoyo amma kun rasa, Ni bana tsoron mutuwa dan nasan ko ba daɗe ko ba jima se na mutu kuma kanku se kun biyo ni inda zan tafi, abu ɗaya zan jaddada maka Isah kai da mutanen ka, nayi imani ubangiji yana kallon ku kuma bazai bar ku ba sai dai ina gargaɗin ka da babbar murya akan iyali na, wallahi tallahi summa billahi duk ka taɓasu bazaka taɓa jin daɗi ba kuma sekayi nadama babba".
YOU ARE READING
ƘASARMU A YAU! ✅
Romancewace irin rayuwa talaka keyi yayinda shuwagabannin kasar ke tattare duka arziqin qasar zuwa ga kansu kadae tare da iyalensu??? Tabbas rayuwan talakan QASARMU A YAUyana cikin halin matsi da rashin sanin makama. Duka Yan siyasar QASARMU sunayin komae...