Kauthar 1

934 47 15
                                    

✿✿KAUTHAR!!✿✿

*✪✪°01°✪✪*


Babban dakine mai fadi wanda yaji duk wasu kalolin kayan alatu na adon daki har ma da wasu wadanda idanu basu taba gani ba.
Kwance akan madaidaicin wani Italian bed mai rumfa, matashiya Kauthar ce a kwance tana shakar barcinta cike da kwanciyar hankali. Ta rufe jikinta rikif da bargo mai taushi, idan mutum ba zuba idanu yayi sosai ba, ba zai taba cewa da mutum a kwance ba saboda yadda tabi ta kannande a kan gadon kamar wata mage.

Kofar dakin ta bude, wani yaro dan kimanin shekaru hudu ya shigo dakin a guje, tsalle yayi ya dira a tsakiyar gadon ya fara jan bargon data rufa dashi yana kwala mata kira, "Adda! Adda!!".
Juyi tayi ta kara kudundunewa, ya cigaba da tabata yana kara sautin kwala mata kira.
Dan tsaki taja ta bude idanunta da suka yi alamun ja saboda rashin barci da kuma gajiyar data dauki kwana da kwanaki tana tarata, "menene wai Man, ba na fada maka kada ka shigo min daki ba yau?", ta watsa mishi tambayar tana lumshe idanu cikin muryar data sarke da barci har bata fita sosai.

Ya turo baki gaba, "to ai Daddy ne yace kije!".
A take ta bude idanunta da sauri tare da tashi zaune dangargar akan gado kamar ba ita bace take kwance shame-shame akan gado yanzu-yanzu ba, ta zaro idanu, "daddy kuma? me ya faru ne again?!".
Yayi dan murmushi yana watso mata hakoran bakinshi da babu na gaba guda biyu saboda zubewa da suka yi, "na sani? Nima kawai cewa yayi ince kizo!".

Jiki a matukar sanyaye ta zura kafafunta kasa daga kan gadon, suka sauka akan tattausan rug carpet din dake shimfide malale a gaban gadon. Ta taka cikin tafiyarta ta nutsuwa zuwa gaban wardrobe dinta da take jikin bango ta bude ta zaro doguwar hijabi pink ta dora akan riga da wandon pyjamas dake jikinta. Lukman ya sauka daga kan gadon, ta kama hannunshi suka fita daga cikin dakin Lukman yana zuba mata labarai kamar wani radio mai jini, ita kam kai kawai take gyada mishi a sanyaye. Sam ta kasa samun kuzarin biye mishi suyi wasanni da hirarrakin da suka saba. Duk da tayi kokarin boyewa, amma can kasan ranta tunanin abinda Daddy yake son tattaunawa da ita take yi. Ba abu karami bane zai sanya Daddy ya daga baki ya aika a kirata musamman ba, duk yadda aka yi dai tasan magana ce mai matukar muhimmanci.

Suka bi matakalar bene suka sauka kasan falonsu, gidan shiru kamar yadda yake a kullum, idan ka dauke karan talbijin da kuma alamun motsi da take jiyowa daga can kofar kicin dinsu.
Suka bi wani dan siririn corridor har suka dangana da wata kofa, an dan sakayata. Ta tsaya a jikin kofar tare da kai hannu ta kwankwasa. Wata kamilalliyar murya mai cike da nutsuwa da haiba ta amsa mata. Sai data sauke ajiyar numfashi sannan ta tura kofar ta shiga ciki, kamshi da sansanyan sanyi suka daketa a take, ta juya tana wa Lukman alamun ya shiga shima, suna hada ido ya mata gwalo ya juya a sukwane ya bi ta hanyar da suka fito. Kwafa tayi a ranta tana tunanin abinda zata mishi idan Allah Yasa ta fita daga dakin lami-lafiya ba tare da wani sassa na jikinta, koma ranta sun bar jikinta ba.

Akan kujerar daya saba zama ta sameshi, ya harde kafa daya kan daya saye da farin gilashi na karawa idanu karfi a idanunshi, jaridar daily trust ta safiyar ranar rike a hannunshi yana karantawa.
Ta tsuguna kadan daga gefenshi, cikin murya kasa-kasa kamar wadda take tsoron yin magana ta gaidashi duk kuwa da cewa da asubahi lokacin da suka yi sallar safe kamar yadda suka saba, ta gaidashi.
Cikin muryarshi ta halin ko-in kula ya amsa mata. Daga nan wajen ya dauki shiru kamar babu wasu halittu dake wajen. Bayan motsin karan split babu abinda kake ji a wajen, sai Kauthar dake zubda ruwan zufa da zuciyarta dake bugawa tana tsalle tana gudu kamar dokuna na sukuwa.

Mahaifinta ne shi, amma a kullum kuma a koyaushe, kamar wasu bakin juna haka suke kasancewa. Babu abinda taki jinin ya faru kamar a ce mata yau gashi za a hadasu a waje daya ita da mahaifinta na mintuna biyar kacal.

Sai daya gama busar iska son ranshi kafin ya ninke jaridar hannunshi ya dora akan center table din dake gabanshi. Ya kalleta tare da ambatar sunanta cikin wannan no-nonsense muryar tashi, wadda take sa mutum duk rashin kunyarshi ya saduda ko bai yi niyya ba, "Kauthar!!".

KAUTHAR!! Where stories live. Discover now