4

75 7 0
                                    

Cikin daren Hammad bai iya bacci ba, ya tashi yayi kyakkyawar alwala ya fara kai kukan shi ga Allah. Cikin sujud yana kuka yana rokon Allah mafita saboda ya san Allah ne kadai zai iya kare shi daga mummunan kaddarar dake shirin samun sa.
Humaid ne ya farka ya ga dan uwan na shi zaune bisa darduma yana azkhar idon shi jajir irin yanda bai taba gani ba, ya sauko daga kan gadon yazo ya zauna kusa da shi yace "kayi hakuri Hammad, Allah na sane da komai kuma ba zai barka hakanan ba. Kai mutumin kirki ne wanda ni shaida ne akan hakan, kana kokarin tsare hakkokin Allah Kuma..." "A'a Humaid, kada kace haka. Allah da zuciya yake dubi, na kasa cire tunanin da ace bani da lalura da watakila na aikata abin nan da suke zargi na da shi maybe shi yasa Allah ya hada ni da fasikar mace" Humaid din ne ya girgiza kai yace "haba Hammad, kada ka bari wannan musibar ta illata imanin ka, wallahi Allah ba azzalumi bane, shi mai rahama ne da jin kai. Ko da ace baka da lalura, kuma kayi niyyar fasikanci to ba zai rubuta maka zunubi ba har sai ka aikata sa'annan kuma ya baka damar tuba sa'annan in ka tuba ya yafe maka. So banga dalilin da zai sa ka rinka irin wannan tunanin ba har ka yanke tsammani da rahamar Allah besides..." Ya kalle shi yana dan murmushi kasakasa yace "ni ban yarda cewa ma lalura ce da kai ba kawai dai kana da taste ne da har yanzu baka samu wacce tayi daidai da shi ba." Hammad ya balla mai harara yace "Kai har wani abin dariya ka gano a cikin wannan lamarin, da ace kaine a cikin ta da ba zaka samu amusement a ciki ba, yanzu fa yara ma a teenage years din su sun san me ake ji da nufi da sha'awa na opposite sex dinsu sai kuma ni da shekaru na da experience ace ban san me hakan yake nufi ba, ai da ji ma kasan ba lafiya ba"
"amma ai babu wani likita da ya tabbatar da hakan Kuma baka taba attempting son ka tabbatar din ba despite yanda nake ta fama da kai. Idan ka yarda mukaje asibiti zasu tabbatar mana da lalurar ce ko halittar ka ce haka Kuma zasu san abin yi akai"
"kamar yanda kace ne Humaid kar in yanke zato da rahamar Allah, wani hani akace baiwa ce, ni yanzu gara in ta zama a haka in dai har wannan yarinyar ce matar da zan rayu da ita, don nayi imani iya abin da take nema kenan a wajena kuma bazata samu ba da yardar Allah"
Humaid din ne ya fashe da dariya yace "dadina da kai akwai theatrics, koda yake akwai gaskiya a maganar taka, duk macen da ke son ka don Allah ba zata yi cikin wani ta kulla ma sharrin ba, kuma In Sha Allah ba da ita zaka rayuwa ba at least not forever, wata rana gaskiya zai bayyana kuma ka samu mace daidai kai ka aura ku yi rayuwa happily."
Maganar ta sa Hammad dariya wanda shine dariyarsa ta farko tun da mummunan lamarin ya same shi, yace da Humaid din "yanzu waye ke wasan dramar abokina?"
"Ba gashi na sa ka dariya ba"
Dariyar suka kuma yi dukkan su.

***          *******             *****

Gabbannin asubahi ne gidan ya rikede da kururuwar Haj. Uwa inda take ta neman a kawo mata dauki. Humaid din ne ya fara jiyo muryar nata duk da bai fahimci abin da take cewa ba amma yasan ba lafiya ba, yayi sauri ya jawo jallabiya ya dora ya fita yana fadin "bari in duba inga me ke faruwa" duk da ya san bai zama lallai Hammad din wanda ke cikin sujjada ya ji shi ba.
Duk ilahirin gidan sun fito ana tambayar Haj. Uwa abin da ya faru amma sai ihu take tana nuna sashin nata. Alh. Idris ne ya daka mata tsawa da cewa "ki nutsu ki fada mana menene" Nan dai tayi shiru ta fara magana cikin in'ina "nna ffito ne zan shshiga kiccin in sha ruwa shine nagga Safnah kwance a kasa cikin jini ta mut..." Ko kafin ta ida maganar tata Alh. Sufyanu ya wuce ta yana fadin "Idris dauko makullin mota" ya shige side din nata ya iske Safnar kwance bata san inda take ba, bai tsaya jiran komai ba ya ciccibo ta ya fito da ita daidai lokacin da Alh. Idris din ke kokarin bude mota. Humaid ya karbi key din ya bude suka saka ta cikin motar ya fara kokarin tada motar.
Haj. Rahina tace ma Haj. Uwa "ki tashi ki bi su in yaso mu ma biyo baya"  sai a lokacin Haj. Uwar ta mike ta shige bayan motar in da aka kwantar da Safnar, Alh. Idris ya shige gaba suka kama hanyar asibiti.

Shi ko Hammad bai ma san me suke ciki ba ya dai ji hayaniyar amma sam bai dame shi ba, a cewar shi, shima tashi damuwar bata dame su ba dan me zai damu da tasu. Ya cigaba da ibadar shi har sai da gari ya waye tas sannan yayi wanka ya fito ya shiga cikin gidan don samun abin da zai karya, sai dai bai iske kowa a gidan ba kasancewar duk sun tafi asibiti, dole ta sa ya fito ya nufi side din kakan nashi Alh. Lawal. Ya shiga tare da sallama ya iske shi zaune yana karyawa, bayan ya amsa sallamar ne yace "a'aha! Har kun dawo kenan, yanzu nake son in gama in kimtsa in tafi asibitin, ya jikin nata, me a kace ya sameta?"
To fa! Hammad yayi shiru don bai san me zai ce ba; kai bai mai san abin da ya faru ba. To waye ma ba lafiyan? Kafin ya yanke shawarar ya tambaya ne ko a'a sai Kirrrrrr! Kirrrrrr! Kirrrrrr!
Karan kirar wayar Alh. Lawal ya tsaida shi wanda hakan yayi mishi dadi kwarai kasancewar da kunya ace irin haka ta faru a gida kuma yana gidan bai sani ba saboda bai damu ba; in da mutuwa ce fa, da sai ayi janazar babu shi kenan saboda yana fushi da mutanen gidan wadanda suka kasance iyaye a gareshi sam hakan da yayi bai dace ba; yana cikin yi wa kanshi fadar ne yaji kakan nashi na cewa, "Babban gida ne" hakan tasa ya maida hankalin shi wajen shi don jin abin da ke faruwa "yace an sallamo su ma suna dawowa." "Masha Allah! Allah ya kara lafiya" cewar Hammad duk da bai san waye ba lafiyar ba.
"Idan sun dawo zamu tsaida lokaci ayi a gama, daman idan ta haihu ne za a yi amma yanzu tunda Allah ya sa haka ta faru ka ga bai kamata a ja wani lokaci mai tsawo ba gudun abin da zai je ya dawo" Hammad da ke kokarin zuba ma kanshi abin kari bai san sanda abincin ya zube daga plate din ya komai cikin flask ba saboda karkarwar da hannunsa ke yi. Cikin dimuwa ya kalli kakan nashi yace "ban fahimci maganar ka ba Alhaji" "meye baka fahimta ba a wannan maganar?" Ya dan muskuta tare da ture plate din da ya gama cin abinci gefe ya ci gaba da cewa "Wato Hammad na sani cewa shawarar da muka yanke ni da iyayenka bai yi maka dadi ba amma ka fahimci dalilin mu na yin hakan. Safnah 'yar uwarka ce duniya da lahira kuma a wannan rayuwar kai kadai ne zaka mata wannan rufin asiri ba tare da an samu matsala ba. Na san mun shiga hakkin ka amma kai ma ina so ka sani cewa mun yi hakan ne ba dan mun yarda da abin da aka ce ka aikata bane; a'a, sai dan mu taru mu rufawa juna asiri. A kan haka ne nake rokon ka arziki, ta ci darajar mu da kuma mahaifinta (Allah ya jikanshi), kaji ko Hammadu?"
Tunda Alh. Lawal ya fara magana Hammad yayi shiru yana sauraron shi, ya fahimta sarai abin da suke nufi da abin da suke ji ma tsoro ba dan komai ba sai dan iyayen shi mutane ne masu mutunci da dattako, ba zasu so hakan ta canza ba shi ma kuma ba zai so hakan ba sannan uwa uba ga kanwarshi, ya tabbata matukar wannan lamarin ya fita waje to tabbas zai shafe ta itama dan wasu mutanen basu da adalci, kudin goro zasu masu ba tare da sun banbance ba. Kai ko ta ko ina lamarin zai fi a sirri, kuma tunda iyayen shi suka nemi alfarmar ya rufa musu wannan asirin bai kamata ya gaza ba to amma shi ya zai yi da rayuwar sa? Ya san yana da matsala amma yana sa ran sauki wata rana shin idan time din ya kai ina zai kai bukatar shi.
Kamar kakan ya san abin da yake tunani ya ji shi yana cewa "Nan gaba idan ka ga wacce kake so kana da damar da zaka kara aure, ko nawa kaso."
Murmushi Hammad din yayi wanda kana gani ka san na dacin zuciya ne. In da matsalar take kenan shi a yanda yaso ya zama mijin mace daya tak amma gashi hakan ba zai samu gareshi ba.
"Shi kenan Alhaji, kuyi duk abin da ya dace, babu komai." Tausayi da son jikan nashi ya kara shigar shi, dama shi yana da yakinin cewa Hammad ba zai ki yarda da umarnin su ba musamman idan zai kare mutuncin iyayen shi gashi kuma a wannan karon sun shiga hakkin shi sai dai ba abin da zai iya yi akan hakan face ya mishi addua Allah ya saka mishi kuma ya bashi masu yi mishi biyayya shima.

"Allah ya maka albarka ya saka farin ciki kaji Hammadu" Hammad bai iya amsawa ba ya tashi ya bar falon ba tare da ya ci abincin ba.

Ko da ya shiga dakin shi kasa zama yayi, zuciyar shi ta kasa nutsuwa. He gets where they're coming from, he really understand; hakan ce ma tasa ya amsawa kakan nashi amma... Kai Ina! ba zai iya ba, ya tashi ya fara hada kayan shi cikin wata karamar akwatin tafiya, zubawa kawai yake ba tare da ya duba abin da yake yi ba.

Humaid ne ya shigo ya ganshi yana ta faman zuba kaya a jaka wacce ta riga ta cika amma bai daina zubawa ba. Yayi sauri ya rike hannun shi yana fadin "Hammad lafiya, me ya faru, ya naga kana hada kaya ina zaka je?" 

"Humaid tafiya zan yi, ba zan iya ba, duk ma abin da zasu yi suyi su kadai amma ba dole sai ina nan ba." "Me kake nufi ne? ban gane ba fa" "na shiga side din Alhaji dazu dan ban ga kowa a cikin gidan ba" ya juya ya kalli Humaid "Ina kaje ne, me ya faru?" "Oh! Nima ban sani ba wannan yarinyar ce wai ta fadi unconscious tana bleeding shine mukai rushing dinta zuwa asibiti, well" ya daga kafadu cikin ko in kula "ta samu miscarriage, mun ma dawo ai an sallameta tunda sun ce ba wani complications. Wait! Kenan in haka ne bud, I think you're off the hook, tunda yanzu babu cikin."
" Shine abin da nake son fada maka, nayi magana da Alhaji dazu," ya girgiza kai yana dariyar takaici "in fact now that I think of it, ya san da miscarriage din amma yayi min maganar da yayi min, dan sai bayan da abba ya kira shi sannan."

"Me ya ce maka?"

"Bayani yayi min na dalilin hukuncin da suka dauka wai duk rufuwar asirin mu ne gaba daya blah blah blah, kuma na amsa mai"

"But why? Me yasa zaka amsa, da baka yi hakan ba da yanzu tunda babu cikin..."
Hammad ne ya katse shi da cewa "it's not about the pregnancy anymore, time din da Alhaji yayi min maganar ai ya san da miscarriage din, ba abin da suka canza. Na amsa ne saboda I can't do anything about it and honestly" ya zauna a bakin gadon "I understand their point of view but it doesn't mean I have to like it or be happy with it."

"And now you regret it"

"No, I can't bring myself to, I mean there's no point really but..."

Ya mike ya zuge zip din jakar tare da doguwar ajiyar zuciya "ba a ace dole sai ina nan za ayi ba, saboda haka ni zan tafi."
"Kace dai zaka gudu, kana ganin zasu yarda ka tafi ne amidst wannan harkar"
"Ai ba wanda zan sallama har su abba, kai ma zai fi kyau ka nuna baka ma san da tafiyar tawa ba" "wallahi ba wanda zai yarda cewa ban san da tafiyar ka ba amma kawai kaje ni zan san me zan ce musu idan sun tambaya. Sai dai fa ka tafi yanzu tun kafin su ankare su kawo matsala."

Hammad ya matso ya rungume dan uwan nashi yace "na gode, what will I ever do without you?" "Nothing at all"
Hammad ya dan naushi kafadar Humaid din cikin wasa yace "careful, kar kan nan naka ya kara girma" suka yi dariya Humaid din yace "ka kira ni in ka kai"
"In Sha Allah, am really sorry man for putting this all on you"
"shut up and leave already. And if its get too much I'll just up and leave myself."
Hammad ya dauki jakar shi ya fita wajen motar shi ya bude ya wurga jakar a gidan baya sannan ya shige motar ya fita daga gidan tare da daga ma Humaid hannu.


A/N

That's it! The 4th chapter, I know it's long overdue so I make it especially long to make up for the wait and I really hope you like it; so do vote, comments nd share.
See U guys on the next update
Thanks.

Tarayyar JiniWhere stories live. Discover now