5

67 6 0
                                    

Da sassafe Safeenah ta tashi tai wanka ta kammala shirin ta sannan ta kama ma Nanah aiki suka hada breakfast. Bayan sun gama karyawa ne tai sallama da jama'ar gidan suka fita da Nanah wacce za tai mata rakiya park.
Tai sa'a kuwa motar ta kusa cika dan mutum uku suka rage motar ta tashi, nan dai ta biya direba kudi suka shiga motar ita da Nanah suka cigaba da hirar su kafin a samu ragowar cikon mutanen.

Daga gefen su kadan hayaniya ta kaure tsakanin wasu mutane wanda duk ya janye hankalin jama'a, mutumin sai fada yake kamar zai ci babu ana ta bashi hakuri amma fir ya rufe ido sai hargowa yake. Nanah ce ta ja dan karamin tsaki tace "kai wannan mutumin mafadaci ne kuma bai da hakuri, mutane a taru haka ana baka hakuri ai ko menene ka hakura ka kyale" Safeenah tace "ai kin san mutane kowa da irin na sa halin, yanzu haka in zaki bincika sai ki ga ba wani abu bane da ya taka kara ya karya"
Suna nan dai zaune wasu mata suka zo su biyu zasu shiga motar, shi conductor bai san ba da Nanah za ai tafiyar ba sai yace masu wurin mutum daya ya rage, su kuma suka ce tafiyarsu daya don haka ba zasu raba hanya ba. Driver na zuwa ya iske suna wannan kawai sai ya hau conductor da fadan don meye zai ce ba wuri bayan ga seat nan a baya na mutane biyu, kowa a tashar ya san halin direban da fadan tsiya hakan ne ma yasa conductor yai shiru yana jin shi har ya gama sannan ya fada mishi cewa mata biyu ke zaune bayan shi yasa yace ba wuri, ai ko sai ya sake hawa ya nufi wajen motar yana fadin "kaji yarinya zata raina min wayau, ta ban kudin mutum dayan sannan ta dauko wata 'yar iskar su shige min mota" haka yai ta masifa har ya karasa inda motar take ya samu su Safeenah ya hau su da fada, in da yake shiga bata nan yake fita ba.

Ita ko Safeenah mamaki da takaici ya hana ta cewa komai sai Nanah ce ma ke kokarin fahimtar da shi yanda abin yake amma kiri-kiri ya ki fahimta. Safeenah da taga abin ba na karewa bane sai cewa tayi ta fasa shiga motar ita ma a bata kudin ta, haka dai rigimar ta karu har mutanen cikin motar suka sanya baki akan duk suyi hakuri rashin fahimta ne. Haka dai aka samu aka kashe wutar conductor ya fara shirya kaya cikin boot. Safeenah ta juya su kai sallama da Nanah suna masu kewan juna da mamakin irin hali na mai motar don sun gano shine wanda yai hayaniyar dazu. Aka shirya kaya tsaf kowa ya shiga ya zauna direba ya tayar da mota suka kama hanya.

Safeenah ta dauko littafin du'a din ta ta fara karantawa tare da yin addu'ar Allah ya sauke su lafiya. Bayan ta kammala ne tana kokarin maida littafin cikin jakarta ne ta jiyo muryar direban yana fada, tai murmushi a zuciyarta tace,
yanzu kuma ko da wa yake? Oho!
Yanzu abin nashi dariya ma yake bata, mutum gaba daya komai nashi fada, Allah ya kyauta. Ta dauko headphones din ta ta saka a kunne ta lumshe idanuwanta, a hankali tunanin irin kewar su Nanah da aunt din ta da zata yi, duk da dai gida zata je kuma tayi kewar gidan sosai ga kuma dokin komawa amma hakan bai hana ta jin kewar in da ta baro ba domin cikin kankanin lokaci sun zame mata wani jigo a rayuwarta especially ma Nanah. Yarinyar 'yar shekara sha bakwai amma ta na da girmama na gaba da ita ga hankali da hangen nesa. A wannan zamanin da kawaici da dattako suka karanta za a dade ba a samu irin su ba, gashi dai ba dangin ta bane amma sun rike ta da amana.

Lokaci daya taji marar ta ta juya wanda yasa hankalin ta tashi, ba wai ciwon da ke yi bane yasa mata tashin hankalin sai fargabar period din ta da zai iya zuwa. Sam ta sha'afa da cewa it's the time of the month da zata zama cautious to avoid any embarrassing situations. Yanzu gashi tana tsakar hanya cikin commercial vehicle abin na so ya kawo mata problem, ta daga ido sama irin na mai neman dauki a zuciyarta tace,
Ya Allah ka dube ni ka rufa min asiri ka kawo min yanda zanyi.

Ta cigaba da sauraron wakar ta lokaci lokaci tana dan muskutawa na rashin yarda da kai, shi yasa fa ita bata son periods din ta, duk sai ta zama uncomfortable especially in ba a gida take ba dan ko fita bata fiye son yi ba a irin lokutan sai wanda ya zama tilas.

Motar ce ta fara rage gudu a hankali har ta tsaya gefen titi. Safeenah ta dago dan ganin abin da ya tsaida su tana mai fatan ba motar ce ta baci ba, bata fahimci komai ba hakan yasa ta cire headphones din ta daga kunne daidai lokacin da direban ke cewa "kowa ya yi harkarsa ya dawo kar a bata min lokaci ehe! Don yau nake son juyowa don haka mintuna..."

Alhamdulillah cewar Safeenah da murna cikin ranta, don jin dadi ma bata saurari abin da direban ke cewa ba ta fara bincika hand bag din ta, dake kowani lokaci bags din ta basa rasa sanitary pads a ciki irin wanda take ajewa saboda tsaro; yanzu ma da confidence ta dubo pad din sannan ta mike a tsarge don tunanin ko ta yi staining.
Da taga komai normal sai ta fito daga motar tana waigen inda zata samu ta saka pad din, sai dai garin da suka tsaya karamin kauye ne mai tsirarrun gidaje jifa-jifa, haka dai ta nufi wanda yake mafi kusa don ta roki masu gidan su bata kewaye da ruwa.
Gidan da take son shiga babu laifi akwai dan tafiya daga inda motar ta su take don haka ta tafi cikin sauri har ta isa tai sallama, matar gidan tsohuwa mai kirki ta amsa tana murmushi amma da alama bata gane Safeenar ba. Safeenah ta durkusa ta gaida ta sannan ta fada mata abin da ya kawo ta, matar tace "a'aha! Ba komai ai bari na dauko miki butar" ta dauko buta mai girma irin namba biyar dinnan ta mika wa Safeenah ta karba tana godiya "da kin zaga lungun nan kinga kofar kewayen" cewar matar.

Sai da ta kammala kimtsa kanta sannan ta fito tai wa matar godiya hade da sallama ta fito daga gidan ta nufi in da motar ta tsaya, sai dai abin mamaki shine tun daga nesa bata hangi motar ba, ita dai ta san ba ta yi nisan da motar ta bacewa ganin ta ba amma gashi yanzu babu mota babu alamar ta.

A/N
Tabdijam! Ko ina motar taje?
See you guys next time.
And pls do vote, comment and share.
Thanks

Tarayyar JiniWhere stories live. Discover now