2

139 4 0
                                    

Falon yayi tsit; baka jin karar komai sai fankar sama da ke kadawa. Duk da iskar da take bayarwa bai hana Hammad fidda gumi ba wanda tasa zufa ke barazanar wanke mai duk ilahirin jikinshi. Mamaki da bacin rai ne fal zuciyarsa, hakan yasa take masa wani irin bugu mai radadi.

A daidai wannan lokacin Alh. Lawal ya ci gaba da maganar da yake yi amma kwata-kwata Hammad ya daina sauraron sa, abu daya kawai ke mishi yawo a kwakwalwa 'wai shi yai wa Safnah ciki' to ta yaya? Dan shi ya san ko a ruwa ake sha to ba shi ya bata ruwan ba. Kwatakwata ma tun da suka yi wayau suka mallaki hankalin kansu zai iya kirga haduwar su, to bare wata mu'amala mai karfi ko kusanci da zata kai ga yin ciki. A da dai; lokacin suna yara sun yi tarayyah irin ta kuruciya amma tun da girma ya zo musu ya yanke duk wata alaka da ita especially da ya gane bata da kamun kai, lokuta da dama yakan yi mamakin yanda Safnah ta canza kamar ba wacce ya sani suna yara ba haka zalika lokuta da dama yayi yunkurin yi mata nasiha da ta gyara rayuwarta ta kare mutuncinta ta 'ya mace da martabar iyayenta amma sai ya fahimci tayi nisa bata jin kira, domin shi kanshi fin sau a kirga tayi kokarin jan ra'ayin shi zuwa gareta; ta kan biyo shi har dakin shi da salo iri-iri na yaudara sai dai shi a nashi bangaren; bata taba burge shi ba bare ta bashi sha'awa hasalima bai taba jin irin wannan feelings din ba a rayuwar shi saboda ko a cikin friends in ana hirar 'yan mata ya kan yi wa kanshi tambayar abin da yasa bai jin irin yanda suke ji, yes; akwai wasu matan da kan burge shi, amma bacin haka babu wani feelings da ya kamanci so ko sha'awa da har zai nemi kusanci da su to bare Safnah, yarinyar da samsam bata cikin matan da ke burge shi, to ta yaya zai mata ciki? Idan ma cikin zai yi ai ba zai wa Safnah ba; bacin kasancewarta kanwa a gare shi, sam bata dace da zama uwar 'ya'yansa ba ko da kuwa shegu ne amma ta yaya zai fara sanar da family din su cewa sharri take mai? Ta yaya zai shaida masu cewa ba zai iya yin ciki ba saboda bashi da sha'awa ko na sisin kwabo? Ko da yake ba zai iya fada musu ba domin duk duniya banda dan uwansa Humaid babu wanda ya san wannan larurar tasa, sannan ma fada musu din bai zama tilas yayi amfani ba sai dai ma tonuwar asiri dan bai zama lallai su yarda ba koda kuwa Humaid zai sheda hakan watakila ma suce bakin su daya a kokarin rufe laifin da suke zarginsa dashi.
Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un ya sake maimaitawa a karo na samama, idon shi ja jir da bacin rai da kuncin bakin ciki.

Ya Allah! Kai ne shaida na, Allah ka kawo min mafita a wannan sarkakiyar.

Addu'ar da yake a ranshi kenan yana tunanin wata hanyar da zai bi ya wanke kanshi, kabbarar daukacin jama'ar dake wurin ya tsamo shi daga ramin tunanin da ya fada. Cikin rashin fahimta ya dago kanshi yana kallon baffan sa Alh. Idris, wanda kani ne ga mahaifinsa da yake cewa "wannan shawara ce mai kyau kuma hakan shi ya fi dacewa, sai dai yana da kyau a jira har lokacin da ita Safna zata haifi abin da ke cikin nata kafin a tsaida lokaci" caraf Haj. Uwa, mahaifiyar Safnah ta karbe da masifa tana fadin "dole ai kace haka tunda ba 'yarka bace, to wallahi tallahi ba zai sabu ba. Ba zai yiwu a batan diya sannan a barta da abin kunya ba ita kadai duniya na kallo don ana so a tozarta ni, ehe!"

Cikin takaici Alh. Idris ya girgiza kai, irin wannan tabarar ya tsana a tattare da matar marigayin yayan nasa, yayi amanna tana da kaso a cikin lalacewar Safna domin kuwa sai da uwa ta gari ake samun 'ya'ya na gari kuma barewa ba za tai gudu danta yayi rarrafe ba. Allah shi kyauta ya fada a ransa a fili kuwa sai cewa yayi "to ai kuwa dole hakan za ayi ko da kina so ko baki so domin kuwa baza mu tsallake shari'a mu bi son zuciyar ki ba" ya juya gun Alh. Lawal wanda ke zauna yana jin duk abin da suke fadi ya cigaba da cewa "kamar yanda na fara fadi tun farko ne, dole ne a jira din saboda addini bai hallata aure da ciki ba sannan kuma hakan zai bada damar tantance gaskiyar lamarin ta hanyar gwajin jinin dan da na Hammad" "me kake nufi? Kana so kace sharri ake masa ne ko me da har kake wani zancen tantance gaskiya?" Sai tasa kuka "dan anga kasa ya rufe idon mijina shi yasa ake kokarin danne hakkin marainiyar 'yata..." Nan dai ta cigaba da kuka tana ta maganganun yanda ake nema a tozarta su dan anga ba idon mijinta.
Alh. Lawal ne ya dakatar da ita da cewa " kiyi shiru ki nutsu, duka wannan family din nawa ne don haka ba wanda zan tauye, shi yasa na tara ku dan ayi maslaha mu kuma yanke shawara da hukuncin da ya dace" ya juya gun mahaifin Hammad yace "babban gida baka ce komai ba."

Sai a lokacin Alh. Sufyanu ya gyara zama yace "ni bani da abin cewa, kamar yanda kace ne dukkan mu daya ne dan haka komai kuka yanke yayi, Allah ya kyauta gaba" matarsa Haj. Rahina wacce tun farkon zaman bata ce komai ba tace "a'a Alhaji, ni a ganina yi musu aure ba shine shawara ba in dai basu suka nuna bukatar hakan ba. Kaddara ce ta riga fata, kuskure kuma anyi shi amma yi musu aure ba zai gyara ba musamman idan basa son junan su sai ya zama an kuma wani, in aka yi rashin sa'a ma har ya shiga zumunci" "nima abin da nake tunani kenan" cewar Haj. Halima matar Alh. Idris
Haj. Rahinar ce ta cigaba da cewa "sannan bai kamata a yanke hukunci farat daya ba ba tare da kwakkwaran binkice ba gudun kar a tauye hakkin wani daga cikin su..." Bata gama zancen nata ba Haj. Uwa ta karbe " Kawai ki fito fili ki fadi abin da kike nufi ba wai ki ta zagaye ba, da kuma ko kai ka haifeshi baka shedar shi balle wanda baka haifa ba" Haj. Rahina da taga abin har da gori kuma ita bata iya hayaniya ba sai tai shiru sai Haj. Halima ce tace "ko wanda baka haifa ba kayi shedar sa in ka yarda da kalar tarbiyar daka ba shi kuma... " "to 'yar iya zance! Wa ya kasa dake da kike neman kwasa? Ko dayake salon maular da aka saba ne dole ku goyi bayan su tunda da kudin su dam mara, ni kuwa ba zan sa ido a cuci diyata dan anga..."

Bata ida ba Alh. Lawal ya daka mata tsawa "ke rufe min baki! Nima rashin da'ar zaki nuna a gaba na? To ahir dinki." Sannan ya cigaba da cewa "Tunda dai abin yana nema ya zama da rigima, to wannan shine abin da na yanke; Hammad zai auri Safnah idan ta haife cikin jikinta."

Jin hukuncin nan Humaid da yai kamar bai wajen ne ya daga wa kakan nasu hannu yana mai neman izinin magana. "Muna jinka Humaidu, akwai abin da kake son cewa ne?" Humaid ya dan sunkwi da kai kafin yace "dama dai kawai ina ganin ya dace a ba Hammad daman kare kanshi ko a ji ta bakin shi, ina da tabbacin Hammad ba zai iya aikata lafin da ake tuhumar shi da ita ba"
Alh. Lawal yayi dan murmushi yace "na fahimce ka Humaidu sai dai ina so ka fahimci hukuncin da na yanke da dalilin hakan. Wato dukkan ku jikokina ne kuma 'yan uwan juna, duk abin da ya samu daya to ya shafe mu gaba daya walau me kyau ko akasin sa dan haka na yanke wannan hukuncin, idan Hammad ya auri Safnah to rufuwar asirin muce duka shi yasa ko bayan ta haife cikin ban yarda ai wasu bincike ba saboda koda babu wannan matsalar shi mai iya riketa ne da danta cikin rufin asiri kuma babu wani can a waje da zai iya hakan ba tare da wata manufa ko matsala ba sai shi da ya kasance dan uwanta. Ina fatan kowa ya fahimta?" Nan duk suka amsa da eh.

Shi ko Hammad ya zama kamar gunki sai dai ya juya ya kalli bakin duk wanda ke magana. Wato har sun gama yanke hukunci ba tare da an bashi damar kare kanshi ba har suna wani cecekuce akai. To in haka ne me yasa aka yi kiran shi, ai da ba'a neme shi ba sun yi abin da zasu yi su kadai. Daya bayan daya yake kallon duk mutanen gurin, duk haushin su yake ji musamman Haj. Uwa da yake da yakinin ta san komai da 'yar tata ta shuka, idan ya rantse ma yace tare suka kulla ya tabbata bazai yi kaffara ba, sannan iyayen shi da suka kasance masu kawaici da kakan nasa mai kokarin rufa asirin iyalansa kai da kowa ma har da shi kansa da kansa da ya na ji yana gani akai masa mummunan hukunci ba laifin sa. Ba tare da yace komai ba ya tashi ya fice daga falon, Humaid ma ya bi bayan dan uwan nasa.
Da daidai da daidai ma matan ke ficewa daga falon kowacce tayi bangarenta suka bar Alh. Lawal da yaran nasa suna zantawa.



Tarayyar JiniWhere stories live. Discover now