3

95 4 2
                                    

Cikin tsananin fushi Hammad ya shiga dakin shi ya fada kan gado, a daidai wannan lokacin ba zai iya tantance irin abin da ya ke ji cikin ranshi ba. Shi dai kawai yana jin duk duniya ba abin da ke masa dadi, ya tashi zaune ya rike kanshi yana kara maimaita inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, a haka Humaid ya iske shi. Shi ma Humaid din cikin jimamin al'amarin ya zauna gefen dan uwan na sa, duk su biyun sun yi shiru ba mai cewa komai don kowanne da abin da yake tunani duk da dai kusan abu guda suke tunawa wato mafita. Sai dai dukkan su sun san cewa babu wani mafita a garesu face hukuncin da iyayen nasu suka yanke wanda dukkan ba mai yiwuwa bace a garesu. Humaid ne ya fara magana "Yanzu meye abin yi?" "Babu! Allah ne kadai zai kawo min mafita, duk yanda yayi dani daidai ne tun da Ya san gaskiyata" Hammad din ya fada a lokacin da ya kwanta rigingine ya rufe idon shi duk da ba bacci yake ji ba. Humaid ya kwanta gefen shi yana mai cewa "shi kenan. Kayi ta addua ni ma kuma zan taya ka, Allah ya iya mana" duk su biyun suka amsa da amin, Humaid ya gyara kwanciya; ranar a dakin Hammad din ya kwana.

***** ***** ***** *****

Safna ce tsaye daga bakin kofar hotel room din, tun da ta shiga bata karasa cikin dakin bama balle ta zauna dan bata son ta dauki lokaci mai tsawo a hotel din gudun kar wani da ya santa ya ganta plan din ta ya wargaje.
Shi ko Nuhu na kwance rigingine a kan gadon dakin daga shi sai gajeran wando, hannun shi daya a karkasin kanshi ya daga dayan yana kiran Safna, yace "zo mana sugar, kin san yanda nai missing dinki a kwanakin nan amma sai wani basarwa kike, ko laifi nayi ne ba 'ai missing dina ba?" "a'a, kawai dai sauri nake ne shi yasa. ka ga ya kamata nai takatsantsan gudun kar a san halin da nake ciki a gida" cewar Safna wacce har a lokacin take tsaye bakin kofar dakin.

Nuhu ya mike ya kamo hannun Safna ya jawo ta bakin gadon ya zaunar da ita tare da kamo fuskarta yace "Sugar, ban fa gane maganar da kike bafa. Tun kafin in tafi na fahimci akwai abin da ke damunki wanda kika kasa fada min, na dauka canjin yanayi ne kafin in dawo zaki warware amma gashi na dawo maimakon ma haka sai wani sabon canjin ma nake gani daga wurin ki. Wai me yake faruwa ne, sugar, ko wani laifin nayi miki, ko kina son wani abun ne, wa ya taba min ke, hmm?"

Safna tai murmushi har dimples dinta suka nuna, tana jin dadin irin so da kulawar da Nuhu ke nuna mata, asalima dalilin da yasa kenan har yanzu suke tare saboda duk a cikin samarin ta babu wanda ke nuna mata kwatantacin wannan kulawar. Da a ce tana iyawa da ta hakura da plans dinta akan Hammad wanda bai ma san yanda ta kwana ko ta tashi ba duk da dai shi din dan uwanta ne amma sam bai damu ba, ance zuciya tana son mai kyautata mata; to in dai haka ne mai yasa tata zuciyar ta kasa son Nuhu, ta kwallafa rai akan Hammad wanda kwatakwata bai kyautata mata?Sau da yawa tana comparing din guys din biyu amma sai ta ga zuciyarta ta fi zuwa gurin Hammad, yanda kyan shi da tsaruwar shi take, ga gayu da iya kwalliya ga ilimi sannan uwa uba halayyar kwarai; duk inda a ka duba guy din yayi duk da dai Nuhu shima ba baya ba wajen kyau da tsaruwa amma kuma shima daidai misali yana da ilimi amma ita kanta tasan halayyar su ta banbanta.

To amma ance kaso mai sonka kuma Nuhu shi ke santa ba kamar Hammad ba da yake nuna mata tsantsar kiyayya a fili kodayake wata kila hakan ce ta sa zuciyar ta ta nace akan shi. It might be zuciyar tata ta dauki hakan a matsayin wani challenge ne kasantuwar ita mace ce mai kyau wanda kuma ta san da shi take kuma alfahari da amfani da shi, ta saba da samun yanda take so a lokacin da take so a wurin maza dan haka hadin kan da ta kasa samu a wurin Hammad ne yasa take maitarsa kuma taci alwashin samunsa ko ta halin kaka dan haka. wannan plan din ta dade ta tsara shi tun ba yanzu ba dan haka ba zata bari conflicted feelings dinta ya rusa mata shi ba.

Ji tayi an ja mata hanci cikin sigar wasa wanda hakan ya fiddo ta daga dakin tunanin da ta shiga, ashe fa tambayar ta yayi, mai ma ya tambaya? "nace akwai abin da ke damunki ne babyna?"murmushin dai ta kara yi a karo na biyu ta kamo hannunshi ta rike a nata sannan tace "haba dai, ba komai wallahi, kawai dai daman aure nake son yi" ta fada tana mai kallon kwayar idon shi don son gane abin da yake tunani. Shi ko Nuhu shiru yayi bai ce komai ba yana tunanin in dai Safnah aure take son yi to ya zama mishi dole ya bi ra'ayinta don ba zai iya rasata ba, don haka ya kara kankame hannunta yace "Babu komai, duk da dai bani da ra'ayin aure yanzu Kuma na zaci kema hakan ne a ranki, amma tunda aure kike so shi kenan. Ki fada min yanda kike so ayi?"
Guy din yayi tsananin ba Safnah mamaki, ganin duk da tunanin yayi amma fuskar nashi bai nuna mata abin da take son ganewa ba, kuma ita nata tunanin bai taba kawo ta nan ba, sanin cewa Nuhu kwatakwata bai da ra'ayin aure, a tsawon lokacin da suka dauka tare bai taba nuna sha'awar yin auren ba. Hakan ne ma yasa ta bijiro da wannan maganar saboda tasan idan yaji maganar aure zai ja baya da ita watakila ma ya rabu da ita sai ta samu damar cimma burin ta a kan Hammad.
"Me Kuma kike tunani baby na? Nace in dai abin da ke damun ki kenan to ki kwantar da hankalin ki, ko yanzu kike so inje neman auren ki zani, babu abin da ba zan iya yi a kan ki ba wallahi, ko da kuwa ya ci karo da ra'ayi na"
To fa! Safna ta shiga wani yanayi, duk da dai abin da ya fada din yai mata dadi amma ba abin da take son ji ba kenan. Bata so ta bata ma Nuhu rai, tafi so su rabu cikin maslaha, hakan ne ma yasa ta fara saqa abin da zata fada mishi yanda sam ba zai ga laifin ta ba. Nan da nan ta marairaice fuska ta ce "Na san haka baby, amma Ina so ka fahimci wannan auren ba laifi na bane, infact ba ra'ayina bane, kai tsaye ma zaka iya cewa dole akai min" "kamar yaya?" Nuhu ya tambaya cikin rashin fahimta. "Ka tuna wani cousin dina da muka taba haduwa dashi a wurin shopping? To shine ya ce wai lallai ni yake so zai aura kuma kasan iyayen mu 'yan uwa ne kawai sai suka yanke shawarar mana auren gida." "What! Kawai haka, ke kuma kika yarda? Ai kawai ki nuna musu cewa zamani ya canza ke ma yanzu mai 'yanci ce" Safnah tasa kuka "Wallahi baza su saurare ni ba, kasan ni dad dina ya rasu, daga ni sai mom kuma ita ma bata da wani say akan lamarin." "Yanzu yaya zamu yi kenan, ko visa zan sa dad dina ya mana kawai mu gudu mu bar qasar" Safnah ta zaro ido tare da girgiza kai "hakuri kawai zamu yi for now, in yaso in akayi auren bayan wani dan lokaci sai muke haduwar mu, ai ba abin da zan fasa, nima ba zan iya daukan wani lokaci ba tare da kai ba" "a gaskiya ba zan iya zuba ido wani can ya..." Safnah ce tayi wuf ta rufe masa baki tana fadin "kar ka damu, in dan wannan ne, nima ai ba zan bar shi ba"
Nan dai suka ci gaba da tsara yanda auren zai kasance da yanda za ayi bayan auren, ranar ko sharholiyar da suka saba yi ma basu samu yi ba amma a kasan zuciya kowannen su da abin da yake tsarawa. Ita Safnah tana tunanin yanda zata jawo hankalin Hammad bayan auren, tsara Nuhun kawai tayi dan ya rabu da ita amma ai zancen ma wai babu kusanci ai babu shi, to dan me ta tsara plan din? Ai dan ta samu Hammad din ne yanda take so, da ace ma zai yarda da ita ne da shikenan ba sai sun yi auren bama don itama bata son auren, takurawa ce amma idan auren ne zai sa ta same shi, to ko da tsiya sai ta aure shi. Hakan ne ma yasa da ta fahimci tana da cikin bata fada ma Nuhun ba instead tai makami da shi wajen samun Hammad din.
Shi ko Nuhu tunanin sa akan yanda zai kawar da Hammad din ne gabadaya, kai bama shi ba duk wani wanda zai fito auren Safnar domin ta shi ce shi kadai.

Tarayyar JiniWhere stories live. Discover now