SANADIN BESTY PAGE 2️⃣

39 2 0
                                    

💐💐S͆A͆N͆A͆D͆I͆N͆ B͆E͆S͆T͆Y͆ 💐💐

 
         L͆a͆b͆a͆r͆i͆/R͆u͆b͆u͆t͆a͆w͆a͆✍️

    R͆A͆B͆I͆'A͆T͆U͆ A͆H͆M͆A͆D͆ M͆U͆A͆'Z͆U͆
         (R͆U͆B͆B͆Y͆)

G͆a͆j͆e͆r͆e͆n͆ l͆a͆b͆a͆r͆i͆
(S͆h͆o͆r͆t͆ s͆t͆o͆r͆y͆)

M͆y͆ w͆a͆t͆t͆p͆a͆d͆ l͆i͆n͆k͆👇🏻

https://www.wattpad.com/1190086089?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
💐💐💐💐💐💐💐💐

Dᴇᴅɪᴄᴀᴛᴇᴅ ᴛᴏ

Mʏ ʟᴏᴠᴇʟʏ ᴍᴏᴍ (Hᴀᴊ Rᴜᴋᴀɪʏʏᴀ), Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ᴍɪᴋɪ ʟᴀғɪʏᴀ ᴅᴀ ɴɪꜱᴀɴ ᴋᴡᴀɴᴀ ❤️❤️

Sᴘᴇᴄɪᴀʟ ɢɪғᴛ ᴛᴏ

Kᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ

Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ʜᴀᴅᴀ ᴋᴀᴡᴜɴᴀɴ ᴍᴜ ᴀ ᴅᴜᴋ ɪɴᴅᴀ ᴍᴜᴋᴇ 🤗

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga  shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

   Na gode da ganin comments ɗinku, Allah ya bar ƙauna...
Besty yace na gaishe ku🤪

  PⒶⒼⒺ  2️⃣

Ƙo a toilet ɗin ma sai da Adnan ya ƙara rage zafi , ganin hankalin shi ya kwanta ne ya sa tayi wanka ta fita daga toilet ɗin ta koma ɗaki, tana cikin sa ƙaya wayar ta dake ƙan bedside ta fara ringing, ganin sunan Anty baro_baro yasa gaban ta dukan tara_tara, ai ba zata iya dagawa ba, sai yanzu ta tuna da aikan da Anty ta ma ta, shine ta biyewa Adnan suka zo hotel,

"Hubbey ka fito Anty nata kira na, kazo ka kaini inda ta aike ni"

Fitowa ya yi yana goge gashin kan shi da towel, ganin ta ya yi a tsaye, matsawa ya yi kusa da ita ya kamo ƙugunta, ƙara narke masa tayi a jiki sai ta juyo ta ƙarbi towel din ta ƙara sa goge mai jikin shi, yana saka kaya ya ɗauki mulkin mashin din shi suka fice a ɗakin.

A kasuwa ya ajiye ta ya wuce shagon shi bayan ya mata alƙawarin dawowa da daddare, da sauri ta shiga kasuwar, da kyar ta samu abinda Anty ta aike ta saboda yamma tayi, wajan ƙarfe biyar ta shiga gida.

Ai kuwa titsiye ta Anty tayi bayan ta haɗe rai

"Daga ina kike?"

"Daga ƙasuwa nake Anty"cewar Fadeela muryar ta na rawa

"Kasuwar ubanki!!, Awan ki nawa da fita daga gidan nan? Kin tafi yawon ta zubar ɗin ki ko? Wai Fadeelah me kike so ki mayar da kan ki ne? Ga maneman ki na arziki amma kin ƙi yadda, kin nace ma wannan shegen yaron mai kai kamar saman risho"

Ai kuwa ɓaki na zumɓura jin munanan kalaman da Anty take jifan besty Adnan da shi, wallahi banda yayata ce da yau sai na sumar da ɓakin ta.

Murfin kwanon da ke hannun ta ba tare da na lura ba ta buga min shi, ai kuwa sai da bakina ya fashe , ganin jini na zuba yasa na kwalla ihu tare da barin wajan ina tafiya ina ja mata Allah ya isa, ba baƙin da ya fashe bane ya ba ni haushi, a'a bestynah da ta zaga ne ya ƙona min zuciya, wajan rijiya na nufa na wanke bakina, bayan na gama na shige ɗaki abuna, ummahani yar Anty na gani a cikin ɗakin tana wasa da remote, ai kuwa sai da na mangare ta na ce "shegiya da ido kamar malmo, Allah ya isa dukan da babar ki tamin" ai kuwa ta sa kuka ta fita a ɗakin ganin haka yasa ni ma barin ɗakin kar Anty tazo ta kuma min wata masifar.


Raudah ganin shima Noor bashi da niyyar magana yasa ta kashe wayar, ai kuwa ranshi ya baci,

"Ba komai, zaki shiga hannuna ne" Noor ya fada yana dukan table din office ɗin shi.

Ina kashe wayata  na saka riga da skirt na wata jar atampha, ban shafa komai ba kasancewar ni fara ce sol kuma ni ba mai ra'ayin kwalliya bace, ko da yake besty ne ya cusa min ra'ayin nan wai shi yafi son ganin fuska na a haka,  fita nayi zuwa dakin mom, ganin bata gyara ba yasa na gyara mata sa'annan na share dakin , ai kuwa nasha yabo a wajan ta

"Iyeee!! Yau su Raudah anyi abun kai, chab da alama za'ayi ruwan sama da ƙanƙara, yau kece da gyara dakin nan?" Mommy ta fada cike da mamaki

Murmushi nayi ina wasa da zoben hannuna na ce

"Eh mom ya yi kyau ko?"

"Ah sosai ma Allah ya miki albarka", Mommy ta fada, alamun jin daɗin abinda nayi sun bayyana a fuskar ta ganin ƙamar Raudah ta fara shiryuwa.

Ɗaki na koma na saka gyale na, purse na ɗauka na fice a tsakar gida na iske Mommy  na ma ta sallama ɗan zuwa wajan tela, ina fita ƙofar guda na ha motar Noor a waje a hankali na taka har wajan shi ina hu_hura hanci ɗan ban so ganin shi ba, 

"Maye", na furta a raina

Cikin ɓacin rai Noor ya ce;

"Raudah me yasa kika kashe min waya"?

A dage nace mai " tambaya kake ko neman sani?

Bai ƙara yin maganar ba, mun kai minti ɗaya a haka, ganin kamar bai da abin fada yasa na ce " kaga malam!! ni ina da wajan zuwa idan kai baka da shi", 

"Ina zaki je?" Noor ya tambaye ni, ko kafin na bashi amsa na hango bestyna yasha gayu cikin wasu kananun kaya jeans baƙi da jar riga yana ganin motar Noor ya haɗe girar sama da ƙasa ya samu gefe ta tsaya ya naɗe hannu a kirji yana kallona, 

Noor bai ga zuwan Besty ba, ganin ban bashi amsa ba yasa shi faɗin

"Ki shiga na kai ki na ce "

"No ka barshi za mu tafi da Dee dina"

Juyawar da  Noor zai yi sai ganin Dee ya yi a tsaye yana harar shi, ai kuwa a zuciye ya fito daga motar ya nufi inda yake...

Hahahaha fan's din besty yau fa da alama zai sha ɗuka a wajan noor


VOTE

COMMENTS

SHARE

✍️
BADAWEEYERH




SANADIN BESTYWhere stories live. Discover now