💐💐S͆A͆N͆A͆D͆I͆N͆ B͆E͆S͆T͆Y͆ 💐💐
L͆a͆b͆a͆r͆i͆/R͆u͆b͆u͆t͆a͆w͆a͆✍️R͆A͆B͆I͆'A͆T͆U͆ A͆H͆M͆A͆D͆ M͆U͆A͆'Z͆U͆
(R͆U͆B͆B͆Y͆)G͆a͆j͆e͆r͆e͆n͆ l͆a͆b͆a͆r͆i͆
(S͆h͆o͆r͆t͆ s͆t͆o͆r͆y͆)M͆y͆ w͆a͆t͆t͆p͆a͆d͆ l͆i͆n͆k͆👇🏻
https://www.wattpad.com/1190086089?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
💐💐💐💐💐💐💐💐Dᴇᴅɪᴄᴀᴛᴇᴅ ᴛᴏ
Mʏ ʟᴏᴠᴇʟʏ ᴍᴏᴍ (Hᴀᴊ Rᴜᴋᴀɪʏʏᴀ), Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ᴍɪᴋɪ ʟᴀғɪʏᴀ ᴅᴀ ɴɪꜱᴀɴ ᴋᴡᴀɴᴀ ❤️❤️
Sᴘᴇᴄɪᴀʟ ɢɪғᴛ ᴛᴏ
Kᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ
Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ʜᴀᴅᴀ ᴋᴀᴡᴜɴᴀɴ ᴍᴜ ᴀ ᴅᴜᴋ ɪɴᴅᴀ ᴍᴜᴋᴇ 🤗
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
💓💓 ∂σи'т ¢αяє fσя тнσѕє ωнσ αяє ιgиσяιиg уσυ
¢αяє fσя тнσѕє ωнσ αяє ιgиσяιиg σтнєяѕ fσя уσυ
✍️
яυвву💓
PⒶⒼⒺ 4️⃣Da kyar Raudah ta iya koma wa ɗakin ta, ko Arya da ta ke ma ta magana a falon Mommy bata kula ba, so kawai ta ke ta ƙira Noor ta mai rashin mutunci, ɗan kawai yaga tana son shi , shine zai fara hadata da iyayen ta, har ya sa Abba ya ɗake ta, to ba zata saɓu ba bindiga a ruwa.
Haka dai ta yi ta kullawa da warware wa har ta isa ɗakin, ko kallon gaban ta ba ta yi ba,tsabar takaici da baƙin ciki, waya ta dauka ta na kiran Noor amma har wayar ta tsinƙe bai ɗaga ba, hakan ba ƙaramin ƙular da ita ya kuma yi ba, bata gaji ba ta ci-gaba da kira amma still bai dauƙa ba, sai da ta ƙira shi wajan sau goma sannan ta hakura, number Besty ta ƙira ringing biyu ya daga
"Hello sarauniyar ya kike?" Jin tana shesheƙar kuka ne ya hana shi ƙara sa maganar da ya yi niyya tuni ya rikice da faɗin
"Haba baby what's wrong kike kuka? Ko wani abu na miƙi? Dan Allah ki fada min" ganin Raudah taƙi dena kukan yasa Dee fadin "gani nan zuwa gidan tunda ba za ki faɗa min ba"
Da sauri Raudah ta ce ,"a'a ba sai ka zo ba zan faɗa maka"Duk yadda suka yi da Abba Raudah ta faɗa ma Dee, ajiyar zuciya ya sauke yana faɗin
" Wlh Raudah ban da kin nace da rabuwa ki ka yi da Nuru, mutum sai ɓakar zuciya da baƙin hali kamar kafuran farko, Ni wlh taurin kan shi ne ma na ke jiye miƙi""To ya ka ke so nayi ne Besty" ni fa ba wannan bane damuwa ta, babbar damuwa ta maganar da Abba ya min ne, cewa fa ya yi wai bani ba kai, kuma kafi kowa sanin bazan iya rabuwa da kai ba" ta ci-gaba da shesheƙar kuka
"To kiyi hakuri ki dena kukan mu yi magana ta fahimta, idan ina jin kukan ki har jijiyar ƙaina tashi ta ke yi" da kyar da kalamai masu ɗadi da ratsa zuciya Besty ya rarrashi Raudah ta dena kukan,
"Ko kefa" ya faɗa cike da tsokana
Murmushi ta sakar mai sauti kamar ta na tare da shi, dama tasan shi ne zai saka ta farin ciki, ɗan ba shi da burin da ya wuce hakan a ko da yaushe, in ta tsinci kan ta a damuwa, to wannan fa aikin Besty ne ya yi ƙoƙarin samar mata da farin ciki komai wahalar shi, shi yasa Raudah ba ta shayin fada mai ko mene ne ya same ta ko ya ke damun ta, abokin shawarar ta ne babu abinda ta ke iya boye mishi, ta riga ta sabar ma da ƙanta fada ma Besty damuwar ta ko farin cikin ta...
"Kiyi hakuri kin ji Raudah!! insha'Allah ba zamu rabu ba, haba ni da ke ba rabuwa sai dai mutuwa ce za ta raba mu, muna nan tare har da ke har abada" Besty ya faɗa cike da son kwantar ma ta da hankali
Ajiyar zuciya Raudah ta sauke,
"Nima haka na ke fata my Better half, Allah ya ƙauda idon maƙiya""Kaiii!! Raudah Abba'n ne maƙiya?lallai baki da hankali ashe" ya faɗa cike da fushi har ya na hura hanci kamar tana gaban shi
Da sauri Raudah ta ce "a'a bestyna nifa ba da Abba na ke ba, da Noor na ke, ɗan nasan shine ya kai gulma wajan Abba kuma wallahi sai na mishi magana zai gane ya sa an dake Ni" Raudah ta faɗa cike da tsiwa
Dariya Besty ya kwashe da shi, sai da ya yi mai isar shi sannan ya ce
" Kar ki yadda ki mai magana, ki saƙa shakku a zuciyar shi, ko a fuska kar ki nuna mai anyi wannan maganar hakan zai rage mai ƙwarin gwiwar ƙara tarar Abba da irin wannan maganar koda wataran zai ƙara ganin mu tare, sannan maganar haɗuwa kuma zan san yadda za'a yi mu dinga haduwa ba a layin ku ba"Murmushi Raudah ta sake ɗan ta ji daɗin wannan shawarar, kuma ta gamsu da hakan, hira suka ci-gaba da yi har Arya ta shigo ta, dangwarar ma ta da book ɗin assignment ɗin ta tayi ta ce
"Anty!! Mommy ta ce na kawo ki koya min kuma ta ce kar ki yadda ki dake ni"
Sakkowa Raudah ta yi daga kan gadon ta fara koya mata assignment ɗin ba tare da ta ce ma ta komai ba kuma hakan bai sa ta yanke wayar ba...
Misalin ƙarfe takwas da rabi Adnan ya iso kofar gidan su Fadeelah, sauka ya yi a kan mashin ɗin shi, kasancewar layin nasu shiru ne, ba shi da hayaniya sossai, karasa wa ya yi wajan wata barandar da ake kiwon shanu, akwai wani waje ta gefen barandar kamar lungu a inda ake ajiye abincin shanun, wayar shi ya zaro a aljihhu ya kira Fadeelah ya sanar ma ta ya iso.
Bayan minti biyar sai ga Fadeelah ta fito daga gida da wani zumbulelen hijabi, taku taƙe cike da yanga dan dama ita akwai ƙaudi, iyayi, rawar ƙai, uwa uba kuma yanga,
Idanu ya tsira ma ta har sai da ta ce "matsa mana na shiga ƙar wani ya ganni" ai da sauri ya matsa mata ta shige cikin lungun, tana karasa cire hijabin da ke jikin ta, daga ita sai pant da bra, ganin haka ya sanya Adnan sakin murmushi, janyo ta ya yi, ya fara aika mata da sakkoni, sun yi nisa cikin jin dadin su kawai sai ganin hasken wuta suka yi yana nufo wajan da suke da alama za'a shiga wajan abincin shanun ne...Toh fa reader's, 🤣😂 wannan shi ake kira da dirimm babban motsi!!!
Yau fa ƙaryar Adnan da Fadeelah ta ƙare dan nasan zasu daku a wajan nan...
VOTE
COMMENTS
SHARE
✍️
BADAWEEYERH
YOU ARE READING
SANADIN BESTY
Non-FictionZama da wan da ku ka mayar da juna besty zama ne na amana, soyayya, tausayi da kuma tsan_tsar kulawa ta hakiƙa wadda akasarin wanda kuke soyayya ba lallai bane a samu irin wannan kulawar daga gare shi, besty ne mai tsayawa ya fahimci damuwar da ake...