💐💐S͆A͆N͆A͆D͆I͆N͆ B͆E͆S͆T͆Y͆ 💐💐
L͆a͆b͆a͆r͆i͆/R͆u͆b͆u͆t͆a͆w͆a͆✍️R͆A͆B͆I͆'A͆T͆U͆ A͆H͆M͆A͆D͆ M͆U͆A͆'Z͆U͆
(R͆U͆B͆B͆Y͆)G͆a͆j͆e͆r͆e͆n͆ l͆a͆b͆a͆r͆i͆
(S͆h͆o͆r͆t͆ s͆t͆o͆r͆y͆)M͆y͆ w͆a͆t͆t͆p͆a͆d͆ l͆i͆n͆k͆👇🏻
https://www.wattpad.com/1190086089?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
💐💐💐💐💐💐💐💐Dᴇᴅɪᴄᴀᴛᴇᴅ ᴛᴏ
Mʏ ʟᴏᴠᴇʟʏ ᴍᴏᴍ (Hᴀᴊ Rᴜᴋᴀɪʏʏᴀ), Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ᴍɪᴋɪ ʟᴀғɪʏᴀ ᴅᴀ ɴɪꜱᴀɴ ᴋᴡᴀɴᴀ ❤️❤️
Sᴘᴇᴄɪᴀʟ ɢɪғᴛ ᴛᴏ
Kᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ
Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ʜᴀᴅᴀ ᴋᴀᴡᴜɴᴀɴ ᴍᴜ ᴀ ᴅᴜᴋ ɪɴᴅᴀ ᴍᴜᴋᴇ 🤗
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
💓💓ѕмιℓє ιи fяσит σf ρєσρℓє ωнσ нαтє уσυ… υя нαρριиєѕѕ кιℓℓѕ тнєм…✍️
яυвву
PⒶⒼⒺ 7️⃣
Abba ne ya umarci Mommy da ta bar Raudah ta ƙara sa uzurin ta, tunda ai dole zata fito a bayan gidan komai daɗewa, badan Mommy ta so ba ta shige cikin gida ba tare da ta ce uffan ba. Bin bayan ta Abba ya yi da kallo mai ma'anoni daban_daban, shi dai yana jin daɗin yadda Mommy ta ke tsaye a kan tarbiyyar gidansa, a kullum yana ƙara gode ma Allah da ya ba shi mata ta gari, ba kamar wasu matan ba da za kaga suna goyon bayan ya'yan su idan sun yi laifi, wasu iyayen ma idan an ma yaran su faɗa ko an hukunta su, koda kuwa mahaifin su ne ko yayun su, kai koda wani ne daban sai kaga sun ji haushi ko su nuna ran su bai so ba, wasu marasa hakuri ma sai sun mayar da martani.Saleem dake tsaye har yanzu shima ya bi Abba da Mommy ciki ɗan daga shi sai Arya ne a gidan Mubasheer bai dawo ba, su sai karfe biyu da rabi suke tashi saboda lesson ɗin da suke tsayawa yi, tunda a shekarar nan zai zana SSCE.
Dee kam gajiya ya yi da zama a baƙin titi, gashi ya gaji sosai, shi anya ma zai iya zuwa gidan su Raudah yanzu? tashi ya yi jiki a sanyaye ya koma shago da zummar ya kwanta, in yaso zuwa yamma sai ya je gidan su Raudah.
Mahifin Noor na office ya ci karo da sakon Abba'n Raudah, hakan ne ya sa ya yanke shawarar kiran shi a waya, domin maganar ta shi mai muhimmanci ce, amma bai daga ba, ganin ya kira sau biyu bai dauƙa ba yasa ya hakura, ya san idan yaga ƙiran shi zai biyo baya, yanke shawarar kiran Noor ya yi, ringing biyu ya ɗaga wayar
"Assalamu alaikum Baba, Barka da rana"
Daga ɓangaren mahaifin Noor ya amsa cike da jin daɗi, yana son ɗan shi, kasancewar Noor yana da biyayya da sauƙin kai, cikin farin ciki Baba ya ce"Son kana lafiya?".
"Lafiya lau alhamdulillah Baba, ya aiki?".
"To Alhamdulillah, komai na tafiya yadda ake so, amm...dama saƙo ne naga sirikin ka, ya turo min aƙan maganar bikin ku, to amma dai maganar ba ta waya bace, zan shigo a weekend ɗin nan insha'Allah, kai dai ka kasance cikin shiri".
Duk da Noor bai fahimci maganar ba, sai kawai ya sosa ƙeya tamkar yana gaban Baba, cike da ƙunya ya ce
"Allah ya dawo da kai cikin koshin lafiya da aminci Baba".
Sosai mahaifin Noor ya ji daɗin wannan addu'ar da gudan jinin shi ya yi, murmushi ya yi cike da farin ciki ya ke faɗin
"Amen Nuradden, Allah ya yi maka albarka, ka gaishe min da yan gidan , ko da yake kafin nan ma zan kira mahaifiyar taka".
"To shikenan Abba".
Noor ya amsa cikin ƙwantar da kai da nuna tsan_tsar biyayya ga Baban shi, ko wannen su ya ajiye waya cike da kewar junan su, ɗan akwai soyayya da shaƙuwa mai ƙarfi tsakanin iyalan Alh Mukhtar Baba, kan su a haɗe ya ke.
Nuradden shine ɗan su na fari sai Khadijah dake bin shi, sannan Hauwa'u ɗuk matan suna da aure Noor ne kaɗai ya rage ( shima kuma zai amarce da Raudah'n Besty🤣), mahaifiyar su, Mama Hajara mace ce mai dattako da mutunci, tana mutunta kowa, amma fa bata iya ɓoye soyayyar da take wa yaran ta a ko'ina, bata son Abinda zai taba su, duk da haka ba ta lalata yaran ba, ta basu tarbiyya dai_dai gwargwado, ɗuk gidan Alh Mukhtar Baba kowa yafi son Noor, ko dan kasancewar shi kaɗai ne namiji, shi yasa ake ma bikin shi tanadi na ban mamaki...
Sai da Raudah ta share wajan mintuna arba'in a toilet sannan ta iya fitowa, a hankali ta ke taƙawa tamkar wacce ta yi nakudar yan uku, Arya ce kaɗai a kofar kitchen da alama wani abin ta ke yi, ɗauke kai ta yi daga kallon Arya ta nufi hanyar shiga parlour'n su, a baƙin ƙofa ta ja ta tsaya jin Muryar Abba da Mommy suna magana
"Tabdijam! Yanzu Abba bai fita ba?, Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, wallahi na san yau ba mai ƙwata na a gidan nan".
Raudah ta faɗa, wasu hawayen baƙin ciki na zubowa a Idanun ta, jin an rangaɗa sallama ne ya sa ta juyo da sauri ɗan ganin waye
Ai kuwa da gudu ta karasa shigewa cikin parlour'n tamkar wacce ta ga mala'ikan mutuwa, ganin wanda Abba ya kira, ta san yau za taci ubanta.....
VOTE
COMMENTS
SHARE
✍️
BADAWEEYERH
YOU ARE READING
SANADIN BESTY
Non-FictionZama da wan da ku ka mayar da juna besty zama ne na amana, soyayya, tausayi da kuma tsan_tsar kulawa ta hakiƙa wadda akasarin wanda kuke soyayya ba lallai bane a samu irin wannan kulawar daga gare shi, besty ne mai tsayawa ya fahimci damuwar da ake...