SANADIN BESTY PAGE 6

16 1 0
                                    

💐💐S͆A͆N͆A͆D͆I͆N͆ B͆E͆S͆T͆Y͆ 💐💐

 
         L͆a͆b͆a͆r͆i͆/R͆u͆b͆u͆t͆a͆w͆a͆✍️

    R͆A͆B͆I͆'A͆T͆U͆ A͆H͆M͆A͆D͆ M͆U͆A͆'Z͆U͆
         (R͆U͆B͆B͆Y͆)

G͆a͆j͆e͆r͆e͆n͆ l͆a͆b͆a͆r͆i͆
(S͆h͆o͆r͆t͆ s͆t͆o͆r͆y͆)

M͆y͆ w͆a͆t͆t͆p͆a͆d͆ l͆i͆n͆k͆👇🏻

https://www.wattpad.com/1190086089?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
💐💐💐💐💐💐💐💐

Dᴇᴅɪᴄᴀᴛᴇᴅ ᴛᴏ

Mʏ ʟᴏᴠᴇʟʏ ᴍᴏᴍ (Hᴀᴊ Rᴜᴋᴀɪʏʏᴀ), Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ᴍɪᴋɪ ʟᴀғɪʏᴀ ᴅᴀ ɴɪꜱᴀɴ ᴋᴡᴀɴᴀ ❤️❤️

Sᴘᴇᴄɪᴀʟ ɢɪғᴛ ᴛᴏ

Kᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ

Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ʜᴀᴅᴀ ᴋᴀᴡᴜɴᴀɴ ᴍᴜ ᴀ ᴅᴜᴋ ɪɴᴅᴀ ᴍᴜᴋᴇ 🤗

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga  shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

Ku yi hakuri da ni d'an Allah , biki ne ya sha kaina shi ya sa ku ka jini shiru, amma kuna raina a koda yaushe... Luv U oll...

               💓💓∂σи'т ωαѕтє уσυя тιмє ωιтн ρєσρℓє ωнσ ѕєєк               αттєитισи тнєу αяє נυѕт вσяє∂ ωιтн тнєяє ℓιfє.

                           ✍️
                          яυвву

PⒶⒼⒺ  6️⃣

Ganin irin gudun da su raudah su ke yi ne ya sa Abba ya koma wajan motar shi, shiga ya yi shima ya tayar a dari ya bar wajan, ɗan yana da tabbacin gida Raudah za ta je .

Ganin Raudah ta ƙi dena gudun ne ya sa Besty fara yin ihun a tare_ a tare ɗan duk a na shi tunanin aljannun ta ne su ka tashi, ganin babu wanda ya yi yunkurin tare tan ne ya saka shi neman waje ya zauna ɗan shi dai Allah ya gani ba zai iya gudu da aljannu ba, koma mene ne ya je gidan su  kawai.

Abba yana barin wajan gida ya nufa, dama yazo bada sako ne, saukar shi kenan a mota ya ga Raudah da wannan yaron da take cewa ɗan ajin su ne, Abin da ya ƙara mishi takaici shine ganin hannun su manne da juna.

Raudah kam duk nisan wajan nan bata gani ba sai da tayi rabin tafiya, gajiyar da ta yi ne ya sa ta tsugunna a gefen titi tana kuka, wayar ta ce ta ke ta ringing amma ba ta da nutsuwar duba wa balle ta iya ɗauka, yanke shawarar koma wa gida ta yi, d'an haka da sauri ta tsayar da me keke napep, da kyar ta iya faɗa mai inda zata je.

  Ko a cikin keken ma babu abinda Raudah ta ke yi sai kuka, shi dai mai keke ya tsaya yana kallon ikon Allah, ganin budurwa santalelliya son kowa ƙin wanda ya rasa, amma ta zauna tana zubar da hawaye, koma me yake damun ki Allah ya yaye miki yan'mata, ya fada a zuciyar shi.
Raudah kam ba ta ma san ya na yi ba, gaba ɗaya hankalin ta baya jikin ta, addu'a ta ke yi Allah ya sa Abba ya koma kasuwa, babban tashin hankalin ta ma Mommy ce, in dai Mommy ta dawo ba ta same ta a gidan ba to ta kaɗe, ɗan yau ta san mai ƙwatar ta a hannun iyayen ta sai Allah, ƙara sautin kukan ta yi, ba ta biyo ta titi ba, sai ta saka mai adaidaitar bi ta saman layin su, hakan ne ya sa bata ga Abba ba, d'an shi har ya zai yi kwanar shiga gida wani abokin shi ya tare shi, akan wata muhimmiyar magana da za su yi, hakan ya sa Abba ya shiga gidan abokin d'an su tattauna, amma gaba ɗaya hankalin shi na kan Raudah.

A dai_dai kofar gidan su, Raudah ta ce mai adaidaitar ya sauke ta, sallamar shi ta yi, duk da gaban ta na dukan tara_tara hakan bai hana ta tunkarar gidan ba kai tsaye, da sanɗa ta shiga da saleem ta fara cin karo a bakin pampo ya na wanke hannu, da sauri ta karasa wajan da ya ke ta na tambayar shi

"Saleem, Mommy ta dawo?"

Bai amsa ma ta ba illa ɗaga ma ta kai da ya yi alamar eh

"Na shiga uku Saleem, ta riga ku dawowa" Raudah ta ƙara tambayar shi, duk ta bi ta rikice, har yanzu jikin ta bai bar rawa ba, kasa motsi ta yi jin muryar Mommy kamar daga sama ta na faɗin

"Daga gidan uban wa ki ke"
Tsaya wa ta yi, ta gaza furta komai sai rawar jiki, bata iya bama Mommy amsa ba d'an ta san ko giyar wake ta sha ba zata iya ma Mommy ƙarya ba, ganin ta yi shiru ne ya sa Mommy ta fara nufo wajan da ta ke ai da sauri bakin ta ya fara magana

"Mommy kar ki ƙara so wallahi shagon tela na je, kira na ya yi wai bai ga kayan da na kai ba, kuma ban dade da fita a gidan ba",
Ganin Mommy ta ki ce mata uffan ne ya sa ta ci-gaba da rantaɓa bayanai kamar an kunna rediyo kaduna

"Wallahi Mommy kuma da na je sai na samu ya fita,shi ne na kira shi ya ce na jira shi, shi yasa na dade"

Wata uwar tsawa mai sa yan hanji su kaɗa Mommy ta ma Raudah

"Dan uban ki ni sa'ar ki ce? Ni za ki kalla ki shirya ma karya Raudah? Tun sha daya da rabi na dawo gidan nan ba kya nan, kuma na kira wayar ki baki daga ba, to tukunna ma a ina Abba'n ku ya ganki?"

Ai tuni Raudah ta ji wani gudawa ya taho ma ta, jin  ashe ma daddy ya dawo gidan, to amma ai ba ta ga motar shi s kofar gida ba, ƙila ya ajiye ne a kasuwa ya zo a mashin, ganin gudawar da ta ke rike wa na ƙoƙarin zubo ma ta a wando ne ya sa ta suri butar da ke kusa da Saleem wanda ya tsaya kallon su, ai Raudah ba ta tsaya a ko ina ba sai saman toilet, me Saleem zai yi in ba dariya ba, ana cikin haka sai ga Abba ya shigo gidan, a fusace ya ce ma Mommy

"Mommy'n yara Raudah'n ta dawo kuwa?"

Juyawa Mommy ta yi ta na ma Abba nuni da toilet, sannan ta ce

"Abba ta dawo ina mata magana ta shiga bayi, cemin tayi wai daga shagon tela ta ke", Mommy ta karashe maganar cike da takaici dan ita fa halayen Raudah yanzu sun fara ba ta tsoro".

Abba ya ciro wayar shi yana dannawa, sako ya tura sannan ya dago ya kalli Mommy,  ya ce

" Kwarai daga shagon tela ta ke, amma ita da wannan ɗan iskan yaron da na raba ta da shi jiya, saboda ta nu na min ban isa ba shine ta je wajan shi har su na rike ma juna hannu"

"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun!! Alh!! rike hannu fa? To  Allah ne kaɗai ya san me yaron nan yake aikatawa da Raudah tunda a idon duniya ma sun iya riƙe ma juna hannu, to wa ya san me suke a ɓoye? Tin da dai ba'a shedar yaran yanzu"  kana ganin Mommy ka ga wacce hankalin ta ya tashi, to ba dole ba ace an ga y'ar ka da wani hannun su manne da juna...

Ƙasa hakuri Mommy ta yi, dama Mommy ba sai zuciya ba, dan ba ta iya ɓacin rai ba,  hanyar toilet ta nufa a zuciye, cikin ɓacin rai ta fara buga ƙofar, d'an Raudah da ta shiga sakata ta sa ka ta ciki, bugawa Mommy ta ke da ƙarfi tana ce wa

"Ki bude ki fito, yau sai kin faɗa min abinda kuke yi ke da wannan shegen yaron da ku ka ƙasa rabuwa da juna"

Jin Mommy na buga kofa kamar zata balla ne ya ƙara hautsina cikin Raudah, ai kuwa tana gudawar ta kara taho wa kamar pampo, ta na yi tana rusa ihu tare da magiya...

😂😂 Fan's ɗin Raudah yau fa besty ya ja ma mutuniyar ku gudawa, da alama sai Mommy ta ɓalla ƙofar za ta bude, Ni dai na tafi kiran besty mu kai agaji gwanda mu haɗu mu rarrashi Abba da Mommy kar su dakan ma na matar besty....

VOTE

COMMENTS

SHARE

✍️
BADAWEEYERH

SANADIN BESTYWhere stories live. Discover now