SANADIN BESTY PAGE 12

7 0 0
                                    

💐💐S͆A͆N͆A͆D͆I͆N͆ B͆E͆S͆T͆Y͆ 💐💐

 
         L͆a͆b͆a͆r͆i͆/R͆u͆b͆u͆t͆a͆w͆a͆✍️

    R͆A͆B͆I͆'A͆T͆U͆ A͆H͆M͆A͆D͆ M͆U͆A͆'Z͆U͆
         (R͆U͆B͆B͆Y͆)

G͆a͆j͆e͆r͆e͆n͆ l͆a͆b͆a͆r͆i͆
(S͆h͆o͆r͆t͆ s͆t͆o͆r͆y͆)

M͆y͆ w͆a͆t͆t͆p͆a͆d͆ l͆i͆n͆k͆👇🏻

https://www.wattpad.com/1190086089?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
💐💐💐💐💐💐💐💐

Dᴇᴅɪᴄᴀᴛᴇᴅ ᴛᴏ

Mʏ ʟᴏᴠᴇʟʏ ᴍᴏᴍ (Hᴀᴊ Rᴜᴋᴀɪʏʏᴀ), Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ᴍɪᴋɪ ʟᴀғɪʏᴀ ᴅᴀ ɴɪꜱᴀɴ ᴋᴡᴀɴᴀ ❤️❤️

Sᴘᴇᴄɪᴀʟ ɢɪғᴛ ᴛᴏ

Kᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ

Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ʜᴀᴅᴀ ᴋᴀᴡᴜɴᴀɴ ᴍᴜ ᴀ ᴅᴜᴋ ɪɴᴅᴀ ᴍᴜᴋᴇ 🤗

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga  shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

   PⒶⒼⒺ 1️⃣2️⃣

  Ko da Raudah ta shiga gida ɗakin Mommy ta nufa, bata gadon kamar yadda ta ganta dazu, dammm gabanta ya faɗi

"Kar dai a ce Mommy ta tashi bata ganni ba?"  Ta faɗa tana zama a kan stool ɗin da ke gefen gadon, maganganun Besty ne suke yawo a cikin zuciyar ta, da kuma yanayin da ta ganshi, fuskar shi kaɗai zaka kalla kasan baya hayyacin shi, gaba ɗaya tausayi ya bata, ya zama dole su koma kamar yadda suke da, sai su gyara salon su ta yadda babu wanda zai gane suna tare har tayi aure ta bar musu gidan.

Mommy ce ta fito daga toilet, ganin Raudah a zaune ya sa ta ɗan dakata bata karaso ba, karantar yanayin da ta ke ciki ta yi, chan kuma sai ta ce

"Raudah lapiya? Tunanin me ki ke yi"?

Firgigit ta dawo cikin hayyacin ta, murmushin dole ta ƙirƙiro, ta ce

"Ah haba Mommy tunanin me zan yi ina da ke", dariya Mommy ta yi koba komai akwai shaƙuwa mai ƙarfi tsakanin ta da ƴaƴan ta duk da ba ta musu goyon sakalci ba amma dai sun shaƙu sossai, kuma duk wanda ya yi laifi suna hukunta shi dai-dai da laifin shi.

"To ko an fara tunanin rabuwa da mu ne?" Mommy ta tambayi Raudah cike da zolaya

Rau-rau ta yi da idanuwa, kamar zata yi kuka ta ke faɗin

"To ni Mommy ki dena cewa za mu rabu, ba kiji yadda gabana ya faɗi ba, Allah na ji wani iri" ta karashe maganar cike da shagwaba...

Shiru Mommy ta yi bata kuma cewa komai ba, zama Mommy ta yi a bakin gado ta dauko waya tana dannawa, wayar ta kara a kunne jim kaɗan ta fara magana

"Assalamu Alaikum, Hajiya Salimah, fatan kina lapiya"?

Daga chan ɓangaren Hajiya Salimah ta yi murmushi mai sauti sannan ta ce

"Lapiya qlau, Mommy Mubasheer ya gida da yaran?"

"Alhamdulillah, sai dai fa kar ki bari Arya ta ji kina cemin Mommy'n Mubasheer, ɗan ta ce ni Mommy'n ta ce ita kaɗai", Mommy ta faɗa tana dariya

SANADIN BESTYWhere stories live. Discover now