*MIJIN KANWATA..*!
_(k'addarata)_*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️**Page 5*
*Garki_Abuja*
8:00amDa asuba Jirgin Airline Daya Daukosa Daga Garin na ikko wato Lagos ya Saukesa anan Babban Filin Jirgin Nnmadi Azikiwe International Airport Dake garin na Abuja Hajiya Zabba"u ya Kira da kanta tazo Filin Jirgin ta Daukesa zuwa Gida wanka kawai yayi a Shashensa,sallar asuba ma agida yayi Lokaci ya Kure sai dai yaran su ka Tashi sukaji Labarin dawowar Alhaji Aliyu.
Koda ya Tafi yayi kwana Dya wajen Hajiya Zabba"u ita keda shi kafin Hajiya Falmata,shiyasa Hajiya Zabba"u ke ta Faman kai da kawo Tsakanin Shashenta da nashi Barayin Taci kwalliyanta Kamar ba ita ta Haifi Zaratan ya"yan nan nata ba.
Hajiya Falmata da suke Kira Hajiya karama sai da safen ta shigo yimai Sannu da zuwa Tana Zaune Adaya Daga Cikin Rantsatsun kujerun Falon nashi Shi kuma yana Zaune kan kujera maizaman Mutum Biyu Hajiya Zabba"u na Gefensa.
Gabansa kuma Katuwar Darduma ce Shake da Kayan karyawansa Daman bai Cika cin abinci a saman Dining ba tun aladaun gargajiya na Masarautar Kargi yafi Sabawa ya Zauna akasa ya Tankwashe Kafa ya wanke Hannunsa yaci Abinsa sai ya koshi.
Yaran sun zo sun gaishesa Tun da Safe sun tafisu Shirya ne zasu shiga makaranta.
Kallon Hajiya Falmata yayi yana Fadin"Hajiya karama ina yaran nan suke ne..?Suzo mu yi Breakfast kafin su Fita makarantar..!
Ta muskuta kafin tace"Ai yanzu zaga gansu..Suna ta Murnan yau zasu yi Breakfast da Abbabsu..!
Hajiya zabba"u na gefe batace komai ba Daman ita haka take bata cika Saka baki ba in Yana ma Falmata mgana tafi so akomai itace agaba Kuma ta samu wannan Mtsayin agidan sai dai ba"a Zuciyar Alhaji Aliyun ba Dukkansu ba wacce bata da Mtsayi mai Girma acikin Zuciyarsa.
Ba Dadewa sai ga yaran sun shigo Sadiya ce da Saddiqa suka Fara shigowa Cikin Shirinsu kamar koyaushe ashekaru bazasu gasa 19 ba Tsawonsu Daya sai dai Saddiqa tafi Sadiya Jiki Saboda Jikin Hajiya Falmata Dayake Tana da Tsawo da Kiba.
Sun shigo ba Dadewa sai ga Sadiq shima ya shigo sak kamar Sulaiman sai dai shi yana dan Haske kadan sannan ya Dauko Doguwar Fuskar Mahaifiyarsa Kamarsu Daya da Saddiqa sai dai ita bambamcin Mace shi kuma Namiji ne..
Dukkansu sai da suka gaida iyayan nasu kafin su zauna cin Abinci suna yi Sama sama Abba na Hira da ya"yan nashi iyayen na Gefe basu saka Musu Baki ba Har suka kamallah suna gamawa Hajiya Zabba"u ta kwalama yar aikin Bangaranta Kira wanda Tazo dasu Daga Masarautar Kargi Dama aka"ida Duk wacce aka aurar da ita Tana Samun kyautar Hadimai Biyu da zasu rika mata Hidima Har Karshen Rayuwarta.
Ita tazo ta kwashe abun da sukayi amfni Dashi ta kuma Nannade Darduman ta Fice dashi.
Kallon ya"yan nashi yayi Daya bayan Daya kafin yace"Yau Lokaci Daya kuke da lecture..!?
Sadiya tace"Ni wani Assigment zan shiga nayi subbmiting Sadiq ne suke da lectures..!
Dayake Dukkansu suna Shekarar Farko ne a Jami"ar Abuja Base University..!
Ya gyada kansa yana kallon Sadiq da yake ta Miyau miyau da baki alamun yana son mgana yasa yace"Yan Biyu kyautar Allah..!
Dariya sukayi dukkansu kafin yace"Naga kana ta Motsi da baki ne Abubakar Meka ke so..?
Kansa ya Shafa kafin yace"Abba Dama..Dama kan mganar Motar mu ne ta Ta Tsufa Ko Sadiya..?
kai Sadiya ta daga kafin Tace"Eh Wlh Abba..Ka fa sauyama su Hajiya Sabbin Motoci mu bandamu..!
Abba na Dariya yace"Ai ni bani na Siya musu ba Saraki ne ya Sauya musu..!
Hajiya Zabba"u ta kalli Sadiya Tana Fadin"Ke yanzu da mu kike gasa..?
To anki a sauya muku ai taku ba abunda Tayi ai batayi Shekara ba..!
Hajiya Falmata na gefe batace komai ba Sai dai tana kallon su da Sauraran abunda ke Faruwa Daman bata da Hayaniya Tana da kamewa bata Cika Shiga mgana ba sai anSakota.
Sadiqa ce tayi Zaraf tana Fadin"Allah Hajiyarmu tafi shekara fa..Tun Sanda aka Siya miki wannan Motar taki Bakar 4matic din nan..!
Sadiya ta karbe da Fadin"Eh Wlh Abba..Mudai don Allah a sauya mana mun gaji da yawo da ita..!
Kansa ya Girgiza yana Fadin"Ni fa ba Ruwana ku samu yayanku ku gayamai shi ya sauyamin Mota ya Sauyama Iyayenku kuma in yaga Chanchantar hakan sai ya sauya muku..!
Hajiya ta kallesa Tana Fadin"To meyasa kai bazaka ka Sauya musu ba Abbansu..!?
Kansa ya shafa kafin yace"Ni ai bani da kudi sosai kamfanin da Saraki ke Kuladashi na kaduna yafi Tara Riba da Nasarori ai yama Fini kudi shi da Har ma"aikatan Sarrafa Madara da Yughourt yake dashi ai yafini Samun kudi yanzu..!
Ya karishe mganar yana yar Dariya Dattajone mai kima da Sanin ya kamata Kamar Sulaiman sai dai bambamcin Shekaru ko kadan Sulaiman baya Kama da Hajiya Zabba"u yafi kama da Mahaifinsa Matan sun fi Dauko Iyayensu mata.
Sadiq ne yace"Nima Abba Kasuwanci zan karanta Ina so na zama irin Yaya Saraki wata rana..!
Kafin yayi mgana Hajiya Zabba"u ta karbe da cewa"Sai ku Taru duka awaje Daya Sadiq..?ni nafi maka Sha"awan ZAma Soja Wlh.!
Saddiqa ta kyakkyalce da Dariya ita da Sadiya suka Hada baki suna Fadin"R.I.P bro..!
Baki ya Tura yana Fadin"Hajiyarmu nidai A"a..Wlh kashe su ake kamar Kiyashi..!
Wannan karon Gabadayansu suka Saka Dariya Harda Hajiya Falmata Da bata saka baki cikin mganar ba In Zata yi Shaidan Hajiya Zabba"u Zata bada Shaidar bata da kabilanci Bata Taba Nuna bambamci Tsakanin ya"yansu Kansu ahade yake Daga manyan Har yaran abu Daya Zata Shaida Tana da Zafin Kishi da nuna Isa da Iko kankomai ita ceja gaba ta wannan bangaran ta Sakarmata Tunda Daman itace Babba sai dai ta Bangaran kula da Miji bata sakarmata ba Itama Tana iya bakin kokarinta Sannan Rashin Hayaniyarta da kawaicinta yasa Alhaji Aliyu yake matukar sonta da Girmamata ba Domin Darajan Mahaifinta ba sannan Ta gaji Dukiya sosai Duk da haka bata da isa ballatana Dagawa Tana Sauki kan Lamuranta da baka isa kaji sun yi wani Sabani da hajiya Zabba'u ba sai abunda ba"a rasa ba,Shiyasa kaf Zuru"ar Maimartaba suke Martabata Hajiya Falmata ta kai ya ta kuma Chanchanta a Sara mata DAta iya Hakurun Zama da Hajiya Zabba"u kowa yasan Tana da Fada sannan a Tsaye take kan al"marinta ita da ya"yansu da Mijinta Halinta Daya Shine Gabadaya ya"yansu take Tsaye kansu sau tari kowani mtsala ne Daga Gidajen auransu Sai daga baya Hajiya karama ma take jin wani abu ya Faru sun Kira Hajiyarsu ta magance komai Tana da kyakyawan Zuciya ta wannan Bangaran.
Gaddama dai ta Sarke suna ta magiyan a sauya musu Mota Abba kuma yace su Tambayi yayansu Wannan karon Hajiya karama Tayi mgana tace"To ku tambayi yayan naku mana..!
Sadiya tace"Tabdi..Hajiya karama kema fa kinsan Halinsa Komai nasa sai ya Tsarashi ya Duba..!
Sadiq yace"Zamu sha Jira ne..Sai mun shigar da Korafin ya Duba ya ga Yuyuwar haka sannan..!
Saddiqa tace"Ai ban taba ganin Dan akida irin Yaya Saraki ba..Kasuwanci yake yi sosai Fitar kudi da shigarsu Duk yana Tsarene..!
Yana kallonsu yana Dariya kafin yace"Haka ake kasuwanci..in baka San komai Daki Daki ba..To watarana zaka kwana aciki..!
Ku tashi ku tafi zan yi mgana Dashi Za"a Sauya muku Sabuwar Mota ya"yan Abba..!
Da Murnansu suka Mike Suna Jin Dadi Sallama sukayi ma iyayen kafin su Fice Direba guda Abba ya Daukan musu Duk da Sadiq ya iya Driving ammh Sulaiman yace yayi kankanta da tuka Mota yanzu sai ya kara Girma Dayake yaran sun samu Sa"a karatu suna da kananun Shekaru suka Fara Jami"a.
Bayan Fitan yaran ne Hajiya Falmata ta Mike Zata fita Yace ta koma ta Zauna yasa ta koma ta zauna ammh Hajiya Zabba'u bata so ba tana so tayi mganar zuwaanta Kargi ne yasa tadan Dakuna Fuska Kadan Kafin ta gyara Zama ganin tana son mgana Dashi yasa Hajiya karama ta maida Hankalinta kan Talabijin din Dake kafe a bangon Dakin.
Domin ta basu daman suyi mgana Tunda ba Huruminta bane..
Sai da ta bari Hankalin Hajiya karama baya Kansu kana ta karkato tana kallonsa Kafin tace"Abbansu ina son zuwa Kargi gobe..!
Yana Danna wayarsa ne saboda akwai Sakon Dayake jirane yaji mganarta Cikin mamaki ya Dago yana kallonta Kafin yace"Ikon Allah..Anyi wani abu ne..?ido na cikin Ido Take kallonsa kafin tace"Sai an yi wani Mutum zai je Gidansu..?ina so naje na gaida Takawa ne da Su Fulani na kwana Biyu ban je ba..!
Kai Tsaye yake kallonta yasan Halinta bata abu babu Dalili.
Cikin Son Tabbatar da Zarginsa yace"Kuma Gobe goben nan..?
Kai ta gyadamai kafin tace"Eh in na samu yarda nake so agoben zan Dawo Abbansu..!
Kai ya Jinjina Kafin yace"Ki bari Weekend sai mu tafi Dukkanmu Har da yara..!
Ranta ya Fara baci Fuska ta Sauya kafin tace"A"a nidai gobe nake son zuwa..Wannan Hutun karshen makon Hutawa nake so nayi agida kusai ku Tafi kaida yaran da Hajiya karama..!
Mirmishi Saman lebe yayi yasani DamanWlh akwai abunda ta Shirya Haka Kurum Zabba'u bazatayi Shuru na wannan Lokacin ba Tana Shirya wani abun koma Menene bari ya Bita Sannu Sannu har ya Fahimci me take Shiryawa..!
Tuna haka yasa ya Kada kansa Kafin yace"Shikenan ku shirya ku tafi keda Falmata..!
Wani Sororo ta kallesa Takaichi yasa ta ta kasa mgana Hajiya Falmata Dataji sunanta kamar Daga sama ta Maido hankalinta kansu ammh batace komai ba.
Hajiya Zabba"u ta daga bakinta Tana Kokarin Saissaita Fushinta Tace"Abbansu ai batace zataje ba..Ni kadai nayi Tambayar..!
Kai Tsaye yace mata"Nasani..Laifi ne in kunje Taren..?ai itama ta kwana Biyu bataje sun gaisa da Maimartaba dasu Fulani ba..!
Takaichi ya hanata mgana ita fa akwai abun da zai kaita ba wata gaisuwa ba Hajiya karama ce ta Gyara Zama Tana Fadin"Abbasu daka bari Weekend din sai mu tafi da yara..!
Hannu ya Daga mata kafin yace"Nagama mganata Tare zaku tafi..In kuma baku yarda ba..Sai dai ku fasa Dukkanku ku jira mutafi Tare Karshen Satin nan nagama Mganata..!
Daga haka ya Mike Dauke da Wayarsa ya shige Cikin Bedroom dinsa ko Waiwaye dukkansu da kallo suka Bisa Hajiya Karama Tace"Hajiyarsu ki bari zan kara mai mgana..!
Mikewa Tayi Dauke da Wayarta Tana Fadin"Ki barsa..Ki Shirya akan Lokaci bana so mu kwana..!
Daga haka ta Fice Daga Falon Tabita da kallon kafin itama ta kada kanta ta Mike ta Fice Daga Shashen zuwa nata Shashen duk da ta Fahimci Wannan karon bata Bukatar tafiya da ita ammh bata da mafita domin Tunda yace ga yadda Za"ayi hakan shine Zaman Lafiya.
Kamar yadda Hajiya Zabba"u ta alkwari Washegari suka Kama Hanyar Kargi Daga ita sai Hajiya Falmata abayan Mota Direba na Tukansu yaran sukabari da Abbansu agida duk da sunsaka Rigiman sai sun je Abbansu ya Lallasheshi kan Karshen Sati chan dukkansu zasu yi Hutun Karshen makon.
Tafiyar dai gatanan ne ba wani Hira sai dai Sama sama haka Daga karshe ma Hajiya Falmata barci Tayi ta bar Hajiya nata waya da Salame suna kara Kitsa yadda Hajiya Zabba"u zataje ma Maimartaba ta yadda Lokaci Daya zai yarda da mganarsu.
Da wuri suka isa Kargi Saboda Daman sun Fito da wuri Cikin Gida suka Fara Shiga Tunda Maimartaba yana Fada da Jama"arsa sai dai an ta shiga da kayan abincin da suka Shago Booth Dasu.
Dakin Fulani suka sauka kamar koyaushe suka rasa ina zasuSaka su ita da Kilishi,kafin kace me an Cika gabansu da kayan Ciye Ciye da Shaye Shaye,hira ta Tsinke tsakanin Fulani da Hajiya Falmata Daman sun Saba sosai da ita ne kadai suke shan Hira sosai Hajiya Zabba"u ta Natsu tana Jiran Kiran Maimartaba wanda bai nemesu ba sai bayan Sallar azahar an Tafi Hutun Fada Falonsa na Cikin Gida ya Shigo yasa aka Kiramai Matan Dan nashi
Gabadayansu suka je suka gaisheshi ya amsa yana ta saka musu albarka su da ya"yansu da Mijinsu,Hajiya karama bata jima ba tayimai Sallama ta koma Cikin Gida ita kuma Zabba"u ta gyara zama kanta na kasa kamar Mummina.
Ta cikin Rawaninsa yake Nazarinta Kafin yace"Zabba"u meke tafe Dake..?
Maimartaba yana Fahimtar Mutum koda bai yi mgana ba Kanta ta kara Saddawa kasa kafin tace"Ranka ya Dade..Allah ya kara maka lafiya Mganace mai nauyi ke tafe dani ina Fatan Takawa zai tsaya ya Saurari mganata cikin kunnin Basira kuma yayi ma mganata adalci kamar yadda ya Sabama yima ya"yansa da Talakawansa adalci..!
Kansa ya Jinjina yana kallonta Cikin Dan Mirmishin Sarauta yace"Ina Sauraronki Zabba"u...!
Kanta ta kara yar a kasa kafin tafara Fadin"Ranka ya Dade daman kan mganar Saraki ne..!
Tafada kafin ta dan Tsaigaita chan kuma ta Cigaba da Fadin"Ranka ya Dade nasan auran Saraki na Farko n Nuna adawata ammh Wlh Daya baya na Cire komai araina Saboda Marigayiya matar tasa Tana da matukar Kirki..Ban kara cewa komai ba tun awanchan Lokacin har zuwa wannan Lokacin da kuka yankemai Hukuncin Sake auran ita yayar matar tashi..Ranka ya Dade duk da Raina bai so ba,ban kara cewa komai ba.!
Daman ai shiTunda ya ganta yasan Mganarce ta kawota shi yafa ya Rike Zabba"u yakarance sosai bata Shurun Banza.
Bai ce mata komai ba ta kara gyara Zama tacigaba da Fadin"Ranka ya Dade nasan Tun bayan Tarewar yarinyar baku taba Bibiyan wani Hali Saraki yake ciki da ya"yansa acikin Gidansa ba..na Tabbata da ba sai nazo nan ina maka mgana ba da tuni ka Dauki matakin Daya dace!
Cikin Hikimarsa yace"Ina jinki Zabba"u..Mene Hurumina aciki da zan Binciki Rayuwar Gidan Saraki..?
Sai ta Fara matso kwalla Tana Fadin"Ranka ya Dade amin afuwa..Na nayi Bincike sosai kan Rayuwar Gidan Saraki kumin uzuri ni uwace kuma kasan yadda uwa take kan Ya"yanta na kasa Jure ganin Saraki Cikin Halin nan Tun bayan Rashin matarsa..!Tafada Tana Siririn kuka wanda Daman ta Shirya hakan
Kai Tsaye yace mata"Wani irin Hali Gidan Sarakin yake ciki..!?
Ta kara Rike mayafinta kafin ta Cigaba da Fadin"Ranka ya dade ba Gidan Saraki ba Hatta shi kanshi SArakin yana Cikin WaniHali..na samu Labarin Tun bayan Tarewar yarinya ba wani Cigaba da aka samu sai Lalacewar wasu abubuwan..Danaji haka sai na Fara Tunanin anya ba"ayi kuskuran Hada wannan al"amarin ba Takawa..?duba da ita batasan Hakkinta na mtsayim matar aure ba Wlh Tallahi kaji Rantsuwan Musulmi Ranka ya Dade in baku yi wani abu ba Rayuwar Saraki zata koma Gidan Jiya yana Bukatar taimakon mu..!
Ta karishe Fada kanta na kara kasa Cikin Nazarin mganarta yake kallomna Kafin yace"Miye Hujjarki Zabba"u..?
Da sauri tace"Magajiya da Samaira Rnka ya Dade..!
Kai Tsaye yace"Su waye su..?me zasu Taimaka mana wajen sanin abunda ke Faruwa..?
Kanta na kasa tace"Magajiya tsohuwar Hidimace daga masarautarka Ranka ya Dade..Ita aka bama Saraki Tun abaya matarsa nada Rai..tana Tare dasu har yanzu..Sai Samira ita kuma Hadimatace Ranka ya Dade..!
Kai tsaye yace"Me ya Hada Hadiman ki da wannan mganar Zabba"u..?
Sai wannan karon tadan Dago kanta Kafin tace"Ni na Turata gidan Saraki ..Saboda ta taimaka ma magajiya Nauyi sun karum mata ga Kula da gida ga kula dasu Wasim..!
Kai yadan Girgiza Zabba'u bazata Sauya ba kenan Cikin Mulki da hikima yace"yara..?ina ita matar tasa..?
Hajiya ZAbba"u ta gyara Zama Tana Fadin"Ranka ya Dade bata zama agida..Koda yaushe tana wajen aiki in ta Dawo kuma Tawuce gidansu Daga yaran Har Saraki bazasu Dora komai kan Tallafinta ba Ranka ya Dade shiyasa nace maka Saraki na Bukatar Taimako uwa uba yaran suna Bukatar Uwar da zata Tsaya ta basu Tarbiya Tunda ita batasan gatan da akayi mata in bazata iya ba sai asamu wacce Zata Tallafi Raunin Saraki Wlh Ranka ya Dade Ina Tsausayin Yaran nan sun taso ba uwa sai Hannun Hadimai kuma Saraki baya zama kasani..Ina mai maka Rantsuwa Ranka ya Dade Laila Zata iya Zama da Saraki da kula dashi yaran susamu Rayuwa mai inganci in har kaga Hakan shine Daidai..!
Bai kalleta ba wannan karon idonsa na kallon Zanen Lallausan Cafet dim Dake shimfide a wajen daman yasan Daga Karshe sai tace haka Zabba"u Tana da naci da Kifiya bazata bar mganar nan ta wuce ba.
Kai Tsaye ya kalleta yace"Tashi ki shiga Cikin gida..!
Dagowa tayi ta kallesa kafin ta Sadda kanta Tana Fadin"Ammh Ranka ya d...!
Hannu ya Daga mata Kafin yace"Ki shuga Cikin gida nace Zabba'u...!
Dole ta Mike Tana Fadin"Ahuta Lafiya Ranka ya Dade..Allah ya kara maka Lafiya..!
Asaman bakinsa ya amsa sai da yaga Fitarta kana ya Muskuta wayarsa Dake gefe ya Dauko ya Lalubo sunan Saraki Daman ai Tsakaninsu ba Shamaki ya Kirassa.
Lokacin da Kiran Maimartaba ya Shigo Wayar Sulaiman yana Office din Saifullahi suna Shirya Haduwarsu da kamfanin Dasuki Venture agobe suna Tatttauna abunda zai gudane yaji Kiran wayarsa yana Dagota yaga sunan mai Kiran ya kalli Saifullahi Dake Kallonsa yace"Wani abu ya Faru..Maimartaba na Kirana..!
Saifullahi yace"Kayi maza ka amsa..Insha Allahu ba mtsala..!
Bai samu Zarafin mgana ba ya Daga wayar Lokaci Daya yana Ficewa daga Office din Saifullahi yabisa da kallon Tsausayi kafin yajawo Fayel gabansa yacigaba da Dubawa.
Cikin Fara"a da Shakuwa suka gaisa da Takawa kafin Sulaiman yace"Ranka ya Dade ina Fatan dai komai Lafiya ko..?
Cikin Dattako da amincin Dake Tsakaninsa da Jikansa yace"Lafiylau Saraki..So nake kasaka Direbanka ya Daukomini Hadiman nan Guda Biyu Dake gidan ka yanzu ya kawo minsu Fadata..!
Sulaiman yaji mganar kamar Daga sama Cikin mamaki yace"Magajiya da Samira Ranka ya Dade..?
Cikin gamsuwa yace"Kwarai..Su nake nufi..!
Sulaiman bai iya cewa komai ba Maimartaba ya Katse Kiransa Gabadaya bai da natsuwa mamaki ya kashesa ba shakka ya sani wani abu na Faruwa sai dai yajira Lokaci kawai kuma bai isa ya Tsaya Tambayan Ba"asi ba maimartaba ne da kansa fa ba Sako ba.
Sani ya kira ya fadamai cewa yaje gida maza maza ya Dauki Mgajiya da Samira zuwa Kargi Umarnin Maimartaba ne..!
Sani yace"Ammh Ranka ya Dade wazai Dauko su Wasim Daga makaranta..!
Kai tsaye yace mai"Ni..!
Daga Haka ya Datse Kiran yau bai da Zabi sai dai ya kaisu Gida Wajen Inna Kafin ya tashi Daga wajen Tunda wachan yarinyar baisanin mata ba ko Tana Gida,duk da yau agida ya barta bai sani ba kota Fita.
Bai koma Office din Saifullahi ba,nashi ya koma yana Faman Tunanin Guguwar Dake Tassomai,sai Uku da Rabi na Rana bai iya Tsinana komai ba Kafin ya fice Daga Office din Kai Tsaye ya Fice Daga ma"aikatan bayan ya Biya wajen Saifullahi ya karbi Key din Motarsa Bai maiwani bayani ba yacemai sai ya dawo.
Da kanshi yaje ya Dauko su Wasim Daga makaranta yakai su anguwan Dosa akofar Gida ya Hadu da Ahmad saiya Godema Allah shi ya Hada da yaran yace ya kaima Inna in ya taso Daga wajen aiki da yammah Zaizoya Daukesu,Daman basu da Mtsalan kaya suna da kaya anan Gida Wasim nata Murna Har ita Wafiyya Saboda Gidan Inna Kamar Gidane a wajensu.
Daganan ya dawo ma"aikata Sani ya Kira yana Tambayansa ya dawo ne..?Sani yace Maimartaba yace ya Jirasu ya maidasu sun saida shiga Cikin Gida Tun dazu..!
Sulaiman Wuni yayi Cikin Zallumi sai wajen Karfe Shida Saura Sani ya Kirasa yace ya dawo dasu sai alokacin ya samu natsuwa.
Abunda bai sani ba Maimartaba ya gana da Magajiya da Samaira Daya bayan Daya kuma ya Tambayesu Tsakaninsu da Allah Cikin Hikima me suka sani game da Rayuwar Gidan Saraki..?
Mgajiya tafadi iya gaskiyanta ta bada Shaidar ba wani jituwa ta ma"aurata a Tsakaninsu sannan ba sunan Zaman Miji da mata sai dai ta Fadi in Sunaima na Gida ita ke Wahala da yaran,Samira kuma harda gishiri da magi ta kara da Fadin tana yawonta sai taga dama take dawowa Gida da sauran abubuwan da Hajiya Zabba"u ta Tsara mata Dukkansu sai da yagama jin Bayanansu ya Sallamesu.
Bayan nan bai kira kowa ba ganin haka yasa Hajiya Zabba"u tace su yi Shirin Tafiya har sai da Fulani Tayi mganar sun yi yammah tace bakomai.
Sun je yima Takawa Sallama bai ce musu komai ba Sai Hajiya Zabba"u tasha Jinin jikinta,ba wani kwakwaran mgana suka Dauki Hanyar komawa Abuja Tasan Halin Maimartaba Baya yanke Hukunci ba Hujja shiyasa koda Taga Su Samira bata Damu ba sanin Tsarinta ne Magajiya kuma bata da mtsala da ita Domin bazata Fadi sabanin abunda ta Fada Duk ai Duk abunda ta Fada gaskiya ne.
Sun tashi daga Ma"aikata shida da wani abu na Yammah amotar Saifullahi suka je gidan Inna suka Dauko su Wasim bayan sun shiga sun gaisa da ita,Baba Baya gida alokacin sun kamo Hanya Saifullahi zai kai Sulaiman gida Shi da yaran Tunda shi yace Sani yakai motan gidan yaje ya Huta hakanan sai gobe.
Suna Tafe Wasim na Gidan baya Wafiyya Tana gaba ajikin Sulaiman Tana ta wasanta ga Biscut nan a Hannunta wanda Ahmad ya siya musu a Shagon Hamisu da zasu tafi Tunda Dazu ya Lura Sulaiman baya Cikin Hayyacinsa sai Faman Kurama waje Daya ido yake yana Tunani baya Cikin natsuwarsa.
Yasa ya karkata kansa Rabin Hankalinsa na wajen Tuki Lokaci Daya yana Fadin"Wai meke damunka ne Saraki..?tun bayan fitarka da kiran Maimartaba naga ka sauya Hop dai komai lafiya?
Ajiyar rai ya sauke Kafin yace"jikina ya bani wata kaddaran zata sake Fadamin Saifullahi..!
Cikin mamakinsa yace"Meyasa kace haka..?
Cikin Wani yanayi yace"Dazu kiran da Takawa yamin..Umarni ya bani na Turamai Mgajiya da Samira zuwa Fada..kuma sani yacemin ya kaisu sun Dade kafin Maimartaba ya Sallamesum.!
Saifullahi ya Zaro ido kafin yace"Kabari don Allah..?
Sulaiman yace"Uhm..
Me ka fahimta..?meyasa Maimartaba ya ce Magajiya da Samira suje Fada..!?
Saifullahi yayi shuru kafin ma ya samu Zarafin mgana wayar Saraki ta Dauki Tsuwwa alamun ana Kiransa a kasalance ya Dagota Kansa ya Dafe yana Fadin"Nafadamaka Wlh Hashashena gaskiya..Wata kaddaran na Sake jirana!
Saifullahi yace"Bangane ba..?
Kai tsaye yace"Hajiyarmu ne ke kirana..!
Shima Saifullahi sai ya yarda da mganar Sulaiman bai ce komai ba Har ya Daga wayar da sallama.
Dagachan bangaran Hajiya Zabba"u da Hajiya Falmata Dake zaune kan Daya Daga Cikin kujerun Falon gidan na Saraki tace"Saraki kana ina ne..?
Cikin Ladabi yace"Ina Hanyar komawa Gida Hajiya..!
Kai Tsaye tana kallon Magajiya da Samira dake Durkushe agabanta bayan sun gama Cika gabansu da kayan Ciye ciye tace"Gani acikin Gidnka..Nazo naga bakanan ba matar gidan ba yara..!
Dam!.
Gabansa ya Fadi Cikin In ina yace"gi...gidana kuma..?
Tace"Eh..Kargi mukaje nida Hajiya karama..Sai Dare yayi mana nace mu Tsaya gidanka mu kwana ko bamu da masauki ne..?
Shikenan ta Faru ta kare Anyi maai Dami Daya sata Dakyar yace"Kuna dashi Hajiyarmu..Gani nan zuwa ina Tare da yaran..!
Ok kadai tace ta Katse wayan tana kallon Hajiya Falmata wacce ke Zaune tace"Na kira Yaya Jamila ban samu Wayarta ba..Zamu kwana anan da Safe sai mu wuce..!
Dakai ta gyadamata Domin tasan ai bata Kirataba,bata da tacewa ne ammh In da zatajita datace bai kamata suna iyaye suzo gidan dansu suce zasu kwana ba.
Kuma Tana Fatan Allah yasa su Kwana Lafiya su koma Lafiya Domin Tun zuwansu take ta Taka le takalen abun mgana Tun bayan da Mgajiya ta Fadamata Sunaima tun kafin su tafi kargi Dazu da Rana ta mata sallama tatafi wajen aiki.
Sulaiman na Sauke wayar a Sanyaye Saifullahi yace"Meya Faru..!?
Cikin Sanyin sa yace"Hajiyarmu da Hajiya karama suna gidana..Sunje kargi Dare yayi musu zasu kwana sai gobe su wuce..!
Saifullahi ya Jinjina kai kafin yace"Koma menene zai faru..Koya Faru..Hajiya ce ta shirya komai..kuma in na Hasoso Daidai kila wannan gabar ita keda Nasara...!
Sulaiman ya Furzar da iska kafin yace"Nasani..Nasani Saifullahi...!*Shakira*
![](https://img.wattpad.com/cover/306768265-288-k170923.jpg)
YOU ARE READING
MIJIN KANWATA(K'ADDARATA)
Action_*Wata irin KADDARA CE wannan..?Kaddaran data Ratso MIJIN KANWATA cikin Rayuwata..?wanda yake matukar girmamani kamar yadda Kanwata SUNAIRA take girmamani?Meyasa kaddara ta zamo tayi min haka..?meyasa sai ni..?Taya zan iya zama da wanda muke jin nau...