*MIJIN KANWATA..*!
_(k'addarata)_*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️**Page 22*
Sai gashi Sunaima ta sabule akan kirjin Sulaiman tayi kyakyawan barci Harda minshari,alokacin zuciya tasamu abunda take muradi ne batare da Tunanin shi din mijin kanwarta bane kamar yadda take fada.
Sunaima harda makara bata tashi ba sai da Sulaiman ya tashi ya shiga wanka bayan ya fito yazo yana yarfamata ruwan Wankan Dake hannunsa sannan ta bude kananun Idanuwanta da suka kara kankancewa Saboda Nauyin barci Sai idanuwanta suka Hasko mata Sulaiman Sanye da rigar wanka bai Daure igiyan ba gabadaya Kirjinsa yana waje ne ga gashi nan Ruwa yasa sun kwanta sai da taji tsikar jikinta ya tashi Allahya taimaketa ya Daura Towel a kugunsa ai da tayi mugun gani Da Saurinta ta kauda kanta Kunya Duk ya kamata.
Mirmishi ya saki kafin yace"Sarkin barci..Ki tashi mun kusa makara..!
Daga haka ya isa gaban madubin Dake Dakin ya fara shirya kansa Ita kuma Cikin jin kunya ta Sauko Daga kan gadon Lokaci Daya ta gyara zaman karamar Rigar barcin Dake jikinta shi ya Daukota da kansa bata da wani Tsawo iyakarta gwiwanta gabadaya kafadunta suna waje ne shiyasa take ta jan Rigar tana nokewa sai ya nuna kamar bai ganta ba yacigaba da Tsane kansa har ta shige Tiolet da kallo ya Bita aransa yana mata Dariya ahakan dai Duk wayonta komai zai wakana da yardam Allah.
Koda ta fito ya fita zuwa masallaci Shiyasa ta samu Damar Sulalewa zuwa Dakinta tayi sallar achan,Sama sama tayi azkar saboda wani barci mai mauyi daya kwasheta alokacin Shi kuma yana Dawowa Dayaga bai ganta ba daman yasan zata gudu bai Damu ba sai ya cigaba da Duba abubuwan da Saifullahi ya turo mai kafin yayi Shirin Tafiya wajen aiki.
Karfe 7:30am na safe ya gama Shirinsa Cikin Shigar Amerian suit baki da Fari da takalminsa Sawu ciki Na fatar damisa ya fito ras dashi sai yar rama kadan da yayi koda ya Sauko kasa Magajiya sun gama Shirya Breakfast,Tea kadai ya sha sai Soyayyan kwai Alokacin ya riga ya kira Sani yana Hanya sai da ya natsa kana ya nufi Dakin Sunaima yana Dauke da karamar Briefcase dinsa na Tafiya Office.
Har ya shiga dakin bata sani ba tana nannade cikin Hijabin Datayi sallah anan Saman Sallayar sai barcinta take Dariya ta kusa kamashi ganin yadda tayi Daga alamu barcin ya Sureta ne bata sani ba
Bai tsaya wani Tunani ba ya ijiye jakar Hannunsa Saman madubin Dake Dakin ya Duka ya Ciccibeta sai saman gadon ya kwantar da ita Barci yayi Dadi har tana rike masa hannu Tana kara gyara kwanciya Mirmishi ya Saki kafin ya saka Dayan Hannunsa ya shafa fuskarta zuwa kanta yana mai kallon Doguwar Fuskarta.
Acikin barci take jin Hannunsa saman Fuskarta sannan Kamshin Turarensa ya cika Duka Kofifin Hancinta Saboda ya Duko ne gabda da ita Da sauri ta Bude idanuwanta sai Fes kan Sulaiman Dake duke kanta yana Sakin mata Mirmishinsa nan nasa mai kayatarwa.
Gabanta ya fadi Saboda wani iri kyau da yayi mata da kwarjini na musamman yasa da Sauri ta kauda kanta Gabanta na Fadi shi kuma sai ya dan murmusa yana Fadin"Madam my Hand..!
Sai da ya fada ta Lura da yadda ta Damke hannunsa da Sauri ta Sakesa Tana kokarin tashi Daga inda take ya saka Tattausan hannunsa ya maidata yana Fadin"Koma kiyi kwanciyarki..Nima fita zan yi Office zani bazan Takura miki ba yau..!
Binsa tayi da kallo sai alokacin ta Lura da Shigar Dake jikinsa bai bata Damar mgana ba yace"Ina Fatan babu wata Damuwa..!?
Da sauri tace"Babu komai...!
Kai ya kada kafin ya Taka zuwa gaban Madubin ya Dauki jakarsa daidai sanda Sani ya kirasa a waya bai Daga kiran ba sai ya Dauki Briefcase dinsa kana ya juyo yana kallonta Lokaci Daya yace"Zan tafi office kila nakai Dare saboda akwai tarin ayyukan Dake jirana..Kimin Alfarman zaki wuni Cikin Aminci Matata...!
Lumshe ido tayi saboda yanayin yadda ya fadi matatace har Tsakar kanta bata samu ZArafin mgana ba Har ya kara Kariso gabanta sai jinsa tayi ya Duka yayi mata Kiss a goshinta yana Fadin"Gud mrning..Tunda ke baki gaisheni ba ni naci girman na baki Anty Sunaima..!
Ayadda ya fadi sunan ne sai da ta Murgudamai baki tana Fadin"Ba gatse kayi ba Sunan kenan..!
Dariya yayi yana Fadin"Nikike Murgudama baki..?so kike na Tsotseshi kenan..?
Jin haka yasa ta Zaro ido Lokaci Daya tana Mirginawa ganin yana Sassauta Tek tie din Dake wuyansa Dariya yayi Lokaci Daya yana Fadin"zamu gauraya anjuma yarinya..Am going bye..!
Ya juya zai fice Daga Dakin ta Bisa da kallo kamar daga sama yaji tace"Kayi Breakfast!?
Dakatawa yayi kafin ya juyo yana kallonta Cikin Halin ko in kula yace"Kin Damu da inci abinci ko kar naci ne Sunaima..?ya"yanki kadai kika sani.banda abunki Abun cikin kwan ai yafi kwan Dadi Sunaima..!
Kallonsa tayi domin gaskiya ya fada yasa bata kara mgana b har yafice Daga Dakin lokaci daya yana Rufo mata Kofar Dakin da kallo ta bisa tana jin wani iri acikin Ranta Tabbas gaskiya ya Fada tana da Laifi Saboda Har yanzu bata Sauke Nauyin Auran Dake kanta ba Sulaiman nada Laifi ammh itama Laifinta yafi yawa.
Yasa jikinta asanyaye ta koma ta kwanta tana wani Tunani Tsakani ga Kewarsa takeji kewar dake fitowa daga kasan ranta batare data sani ba Kasala ya saukar mata sai 11am ta iya tashi tayi wanka ta saka Doguwar rigar na Atamfa kana ta gyara Dakinta ta Fita Falo Samira na gyaran Falon Marliya na goge goge suna ganinta suka Zube suna gaisheta ta amsa sama sama Kitchen ta shiga suka gaisa da Magajiya ta gabatar mata Breakfast bata ci ba ita ta Dafa Doya da Miyar kwai taci tasha ruwa.
Ta koma Daki ta kwanta ta kasa komai gabadaya Sulaiman ke yawo ajikinta da Duniyarta tana jin wani irin kewa kewar da bata taba Zato ba Gabadaya wunin Ranar haka ta wuni Cikin wani yanayi acikin Daki ita kadai gashi ba yaran ballatana su Debe mata kewa Daga Sallah ke tada ita sai kwanciya kamar wata mai karamin Ciki ko Falon bata kara fita ba gabadaya Jikinta ya Mutu sosai ita kanta ta kasa Fassara Halin datake ciki.
Sai 6pm na yammah ta samu ta mike ta Sake fita ta iske magajiya kadai da Samira ne agidan tayi mamaki Domin bata Dauka da gaske Sulaiman yake yi ba sai da Magajiya ta Fadamata tun Dazu Saraki ya aiko Sani ya Daukesu marliya ya maida su Fada sai kuma taji ba Dadi aranta sai dai bata da wannan Hurumin koma tana dashi bazata shiga ba Abunda ya Dace da gidansa yana da ikon Zartar da komai.
Tea ta hada tasha ta koma Daki ta Sake yin wanka yau zata fara Night Duty,sai da tayi Sallar mangariba kana ta Shirya cikin Uniform dimta Ta gama Shiryawa kenan Sai ga Kiran Inna bata Dauka ba sai da wayar ta katse kana sai ta Kirata Daga baya.
Nan taji Inna na Fadamata tayi ma Sulaiman godiya dazu mota guda Sani ya kawo musu na kayan abinci Harda 30k abama Baba kudin Cefene da kayan kwalama nasu wasim da su Indomie da kwai da Cornfkles saboda Lunchbox dinsu Sunaima batayi mamaki ba sanin tun yana auran Sunaira shi mutun ne mai Himma da Sanin ya kamata mai kyauta ya Dauki Baba da Inna tamkar iyayansa.
Sai dai awannan karon sai tji tafi jin Dadi kimarsa da Nasabarta ya Karu acikin Idanuwanta Duk da ta nemi Rabuwa dashi baisa ya Dubi wannan ba ya Taimaka iyayanta kuma bai Duba yanayin zamansu ba gabadaya sai Alherinsa ya Lullube zuciyarta ta kasa tabuka komai har suka gama waya da inna bayan ta Roketa Allah da Annabi kan ta tayasu godiya wajen Sulaiman.
Har suka gama wayar ta rasa mafita da farko taso tafiya asibiti ne kanta Tsaye kamar yadda ta saba sai dai kuma akaron farko taji yau in ta aikata hakan kamar bata kyauta ba Domin tasan bai kamata ba Duk abunda take yi Tunda ai aure sunansa aure bai kamata tana Fita da sunan aiki bada Izinin Mijinta ba.
Shawaran Turamai Test ta yanke na Godiya da kuma tambayan Izinin Tafiya wajen aiki Domin bazata iya Kiransa ba tafi Minti goma da Rubuta Sakon ta kasa Turawa sai da taga Lokaci na tafiya har bakwai na Dare yayi bata tafi ba,Dole tayi gundumbala ta tura masa.
![](https://img.wattpad.com/cover/306768265-288-k170923.jpg)
ŞİMDİ OKUDUĞUN
MIJIN KANWATA(K'ADDARATA)
Aksiyon_*Wata irin KADDARA CE wannan..?Kaddaran data Ratso MIJIN KANWATA cikin Rayuwata..?wanda yake matukar girmamani kamar yadda Kanwata SUNAIRA take girmamani?Meyasa kaddara ta zamo tayi min haka..?meyasa sai ni..?Taya zan iya zama da wanda muke jin nau...