7

924 86 11
                                        

*MIJIN KAN'WATA..*!
_(kaddarata)_

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*Page 7*

Kamar yadda Sulaiman yayi Tunani kwana Hudu Tsakanin zuwan su Hajiya Kargi ya samu kira Daga Maimartaba kan yazo Fada yana son ganinsa,Dayake ya Kirasa Ranar Alhamis sai yace ya Dagamai Kafa Gobe bayan an sauko Daga Jumma"a zai zo da yardan Allah da haka suka Rabu.
Washegari Jumma"a da Shirin Tafiya ya tashi duk da Jikinsa. Duk yayi sanyi da al"amarin ammh ai bai isa ya kauce ma Kiran Maimartaba,Saifullahi ya bashi Shawaran ya tafida su Wasim ko kwana Daya suyi Tunda sun Dade basu Je ba Rabonsu da Kargi Tun Lokacin Rasuwar Sunaira,Shiyasa ya Sanar ma da mgajiya ta Shirya musu kayansu na Tafiya zasu tafi kargi suyi kwana Daya.
Sunaima bata sani ba Ranar aikin Safe gareta Tana asibiti kuma sai bayan da aka Sauko masallacin Jumna"a ta dawo gidan,Tana shigowa Magajiya ta fadamata yanzu suka Mika,Domin Sani na Dauko su Daga makaranta ko zama basu yi ba ska yi musu wanka suka shirya suka Dauki Hanya Saifullahi ma Karaye ya tafi Tunda yakai kimanin Sati uki bai Leka ba.
Gidan duk saiyayi mata Shuru ita kadai ba yara,Gashi Tun Ranar da Inna ta mata wannan Fadan tayi ma kanta alkawarin bazata kara Taka Kafarta Gidan ba sai da wani Dalili ballatana Taje chan ta wuni Ita Tun Ranar ma bata kara mgana da inna ba sai dai suna mgana da Baba da Ahmad.
Har Kiranta Ahmad yayi Ranar atsakar Gida ya Bude Murya yadda Inna Zataji yace"Antynmu yanzu Shikenan Inna ta korarmana ke nida Baba...Gidan duk yayi wani iri da baki nan don Allah ki manta da inna ki Rika zuwa ganin gida abunki..!
Ta wayar tana jin Sanda Inna Tayi Kafyci Tana Fadin"ai sai ta bar zaman auran nata tazo gida ku Tare..kuna Gogan kafada..Kuma Wlh in Sunana bai Fita Daga bakin ka ba zan ci Mutuminka Ahmad..!
Tana jinsa yana Dariya itama Dariyan Tayi Allah Sarki Inna Fada ai Jininta yake ko ba"a ambaceta ba mgana bama da ita akeyi ba sai ta Tsoma baki.
Dole tayi Hakuri ta Nade Cikin Dakinta Ta na Karatun littafin Data Samu Sallah kadai ke tadata sai ko cin abinci..
Sulaiman sanda suka isa Kargi basu samu kebancewa da Maimartaba lokacin Fada ta Cika da al'ummar garin Kargi da suka zo gaisuwan Ranar Jumma"a kamar yadda al"ada ta Tanadar,Shiyasa tun bayan Daya shiga Cikin Gida suka gaisa da su Fulani ya bar musu su Wasim a wajensu ya Dawo Fada shima ana Zaman Dashi Sani kuwa Daman ai Kargi ba bakonsa bane yana chan yana yawo Kusfa kusfa Har mamakinsa Sulaiman yake ko shi Da aka Haifa a garin Kargi Sani sai ya Nunamai Sanin garin
Ranar dashi akayi Zaman Fada Har Dare,tare sukayi Sallar Mangariba da Isha"i da maimartaba aka kuma Hada musu abinci Tare kamar yadda su Fulani suka sani indai Saraki na nan Tare suke cin Abinci da Maimartaba Hakan ya Samu asali ne tun yana Karaminsa Tare suke Gogayar Hannu da Takawa wajen cin Abinci abunda ko da ya"yansa ba"a Taba gani ba.
Sai da suka gama kana Kilashi ta kawo masa su wasim,Wafiyya ce tadai yi Rigima kadan ammh Tana Samun wanka aka goyata shikenan Wasim kuma sai Harkarsa yake ya shiga nan ya Fita yaga Tsarin Gida ba irin nasu ba Hidiman Fulani Indo ita aka barma Ragamar kula da yaran Kafin su koma.
Kwata kwata Kwarjinin Sarki baisa Wafiyya tamai kiyuwa ba yana mika mata Hannu tazo Duk da alokacin ya Sauke Rawanin kansa Tunda yana ainihin Shashensa na Cikin Gida ne sun baro Fada.
Haka ya Hadasu ita da Wasim ya Daukesu ya Dafa kawunansu yana ta Musu addu"a Daga Karshe ya Hada da addu"an Allah ya Jikan Mahaifiyarsu Kam Sulaiman na kasa yana amsawa da Ameen.
Da Farko Har ya saki jikinsa jin Takawa ya fara mai Hira yanayin aikinsu ya gyara zama suna fara Hira,Cike da Fahintar juna da Shakuwa Har su Wasim suka Fara Barci ajikin Maimartaba kana Kilashi tazo ta tafi dasu Cikin Gida sai alokacin Maimartaba ya kalli Sulaiman yana Daga saman Wata Kujera mai kyau da Tsari ga Taushi Kujeran Dayake zama indai yana Shashensa yayinda Sulaiman ke Zaune saman Lallausan Cafet din Daya Mamaye Falon kansa na kasa Cikin Ladabi da Biyayya.
Gyaran Murya Takawa yayi kafin yace"Ina yaron nan Direban ka..?badai komawa yayi ba..?
Kan Sulaiman na kasa yace"A"a Ranka ya Dade sai Allah ya kaimu gobe zamu koma Gabadayanmu..Yana Wajen su Barde chan yake kwana in yuyuwar hakan ta kamamu..!
Kai ya gyada Cikin gamsuwa kafin yace"Banga ka kara wani Kumari ba Saraki Har illah yau da matarka tafi Shekara da rasuwa baka Saduda ka yarda da kowa zai mutu ba..?har ni har kai Saraki..!?
Famin Raunin bamai Sauki bane yasa kansa na kasa ya Dago yana kallon Maimartaba kafin ya Sadda kansa yana Fadin"Ranka ya Dade ai kowa yasan Mutuwa tana kan kowa..Sai dai kasam Shi Rashi sunansa Rashi..Ballatana Rashi irin na Iyalin da aka Fara Shiryama Rayuwa Ranka ya Dade..Sai a hankali ammh Alhamdulillah Ranka ya Dade na Dauki Dangana nasan Allah ne ya bani Sunaira kuma domin ya Dauketa bazan ce don me ba..Allah ya jikanta da Rahma..!
Maimartaba yace"Ameen ya Allah..Haka nake son ji..!
Daga Haka Falon ya Dau Shuru,Sai chan Maimartaba ya Dago kansa ya kara Kallonsa kafin yace"Yaya wajen ita iyalin naka na yanzu..?Ina Fatan Daga kai har ita kun Rumgumi Kaddaranku Hannun Bibbiyu ko kuma Har yanzu baku yarda da cewa bamu muka Hada ba Allah ne da kuma alkalamin kaddaran ku..!?
Gabansa sai da ya Fadi wata amsa zai bama maimartaba Eh mun shirya kanmu ko A"a
Eh yana Nufin tsira Daga koma wani irin abu ne ke Tunkarosa Sannan Fadin Haka Tamkar Sabama mganar Hajiya ce Eh kuma Farantamata da kuma Sallama da kaddaran Datake jiransa.
Maimartaba nata Nazarinsa ganin yakasa mgana yasa ya kara gyara zama yana Fadin"Baka ce komai ba Saraki..!
Kansa ya shafa Lokaci Daya ya Sauke Numfashi kafin yace"A"a Ranka ya Dade..!
Yafada Dakyar kamar zai shide,Yana Lura dashi Cikin Hikimarsa yace"Bangane A"a me hakan ke nufi ba..?
Kansa ya Dago yana kallon Sarki Kafin ya Kauda kansa Cikin Fitar Numfashi yace"Bamu daidaita kanmu ba Har yanzu Ranka ya Dade..!
Maimartaba ya taresa da Fadin"Mtsalan Daga bangaran ka ne ko Daga bangaranta..?
Wannan karon bai yi Jinkiri ba yace"Daga garemu ne Duka Ranka ya Dade..Akwai Nauyin juna Tsakaninmu Sannan ni tun ina auran kanwarta bamu da Fahimtar juna atsakanimmu..akwai Tarin bambamce bambamce Tsakaninta da Yar"uwata shiyasa nake ganin kamar abubuwa bazasu tafi yarda ake so ba Ranka ya Dade..!
Mirmishi Saman baki Maimartaba yayi kafin yace"Yaro yaro ne..Waya Fada maka Dole sai kun samu Fahimtar juna Allah zai Zana muku Kaddaram zama ma"aurata..?abaya kataba Tsammanin matarka zata Rasu har ka auri yayarta..?
Kai ya girgiza bai bashi Zarafin mgana ba ya Cigaba da Fadin"Ita Kaddara bata Shawara da Mutum Saraki..Da ace Tana Shawara da mutanen Duniya sun Zabi Dukkan abunda suke so ya Kasance a Rayuwarsu...Ammh Kaddaran Allah shi kadai ke wanzar dashi a Rayuwarmu in kuma mukayi Hakuri mukayi juriya sai mu cin ma Nasara Har Daga baya mu Fara Tunanin wanchan kaddaran tamu ta Farko batamu bace aronta Allah yabamu Kaddaran da muke ciki ta yanzu Itace Zahirin mu..!
Saraki kansa na kasa aransa yace"Kada Allah ya nuna min Ranar da zan ce gwara yarinyar nan da Sunairata..!
Afili kuma bai ce komai ba,Haka Maimartaba ya Dinga mai Nasiha har ya Saki jikinsa da bakomai yaji Maimartaba na Fadin"In kayi min Izini zan Wakilta Waliyanka su karbo maka auren Laila yar wajen Salame wajen Waliyanta..!
Daman mganar ai yasan tana nan tafe sai dai bai kawota nan kusa ba da Sauri ya Dago yana kallon Maimartaba wannan karon Lokaci Daya yace"Laila kuma Ranka ya Dade..?
Maimartaba ya gyada kansa yana Fadin"Eh..Tun abaya ni na Ture mganarta Duk da Auran cikin Gidan shine Tarihin wannan Masarautar tamu..shakuwar Dake Tsakanina Dakai yasa na baka abunda kake so..Bayanan na kara Aura maka yayar matarka Shima bada Sanin Mahaifiyarka ba..Zabba"u tazo ta sameni tana kukan na Duba Rayuwarka don Allah na aura maka Laila wacce take da yakinin Zata Kula dakai da ya"yanka..!
To ai daman shi ya sani Idanuwansa suka Sauya Launi Cikin Wata Murya yace"Taya akayi ta samu Tabbacin Zata Kula Dani Ranka ya Dade..!?
Kai Tsaye Maimartaba yace"Bansani ba..Sai dai wannan karon ina jin kunyar idanuwanta In ki yimata abunda take so Saraki Zabba"u kamar Aliyu take a wajena..Kuma nason yadda Tayi ta Hakurin ikon da nuna mata akanka bata yi Fushi ba tazo wannan karon da kokon baranta Tana Fatan na kara Nuna Ikon akanka..Shiyasa nake so in ka bani Dama sai na Sakata Dariya koda Sau Dayane Tak akan ka Saraki..!
Ya kasa mgana Saboda ya gama Kashe masa Jiki da Kalamansa to me zai ce wannan fa ba Neman yarda bane Kamar Jin ta baki ne da kuma Umarnin manya afakaice.
Yasa yama kasa mgana Saboda yadda ya Shiga Rudi Maimartaba ya Sauko Da kansa Daga saman Kujera ya zauna akasa Cafet kusa da Sulaiman ya Dafa Kafadarsa yana Fadin"Kada ka damu..Aure sunnar Ma"aiki ne Saraki...Kayi ma Mahaifiyarka Biyayya Saraki..Watakila wannan auran naka Shine Hanyar warwarewan Duka Lamuranka kai dai kayi Fatan Alheri ka kuma ka neman Zabin Allah..!
Kansa na kasa yace"Duk yadda kayi Daidai ne Ranka ya Dade.!
Yafada kamar ya Kurma ihu Ko abaya bai jin Sha"awar auran Laila ballatana ayanzu da komai ya Sauya ammh Taya zai iya Ture alfarman takawa da kansa Ga kuma Hajiya agefe ai shidai kawai Allah yasa yazamemai kaffara.
Maimartaba yayi ta sakamai albarka kafin su Rabu Shashem da suka Saba sauka Tun marigayiya nada rai Kayattacen Shashensa da shi kadai keda wannan Shashen kaf a jikokin Takawa ai Saraki na Dabam ne Ranar Wlh bai iya barci ba kamar yadda Takawa yace kwana yayi Sallah yana Rokon Zabin Allah kan Lamarin da asuba Tare sukayi salla da maimartaba a masallacin Fada,Daganan suka yi sallama Tunda da Sassafe zasu dau Hanya Maimartaba ya bishi da Saka albarka da Godiyan Fura da Tsafffaciyar Madaran daya zo mai da ita.
Karfe 8am na Safe suka Dauki Hanyar Komawa Kaduna duk yadda Fulani da Kilashi suka so ya bar musu Wasim su kara kwana yaso haka ammh Wafiyya ta fara Rigima Data gansa sai Wasim ma ya Fara Dayaga za"a barsa shi kadai Sai maimartaba yace su barshi ya Tafi da ya"yansa.
Suna zuwa Gida ya sake wanka ya Fita Zuwa Wajen kamfani Tunda Saifullahi baya nan sai Gobe zai dawo yaran Wajen magajiya ya barsu tunda Baima Tsaya bi ta kan Sunaima da sai sufi kwana Biyar basu ga juna ba Bata Gida Tana wajen aiki,Dayake ta koma na Safe ne.
Tunda ya barma Allah Zabinsa yaji ya samu natsuwa ya Cire abun aransa ya Cigaba da Harkansa Bai Fadama Saifulllahi ba sai da ya Dawo yake Fadamai Saifullahi yaji matukar Tsausayinsa ammh bai nuna ba illah Kafadarsa Daya Daka yana Fadin"Allah yasa alheri abokina..Kada ka Damu komai zai zama Daidai..!
To in ma yace zai damu ai yasan sai Damuwan ta Illatasa shiyasa ya watsar da komai sai dai duk Dare yana Kukan Mutuwa da Rashin Sunaira Domin Ba Domin mutuwa ba da Duk Abubuwan da suka Zagaye Rayuwarsa basu Faru dashi ba.
Maimartaba komai zai iya kai Tsaye yake yinsa ko Sati ba"ayi ba Abba ya Kira Sulaiman yana Shaidamai Sunyi mgana da Babansa Sa"idu jiya Maimartaba ya Kira su Kargi ya kuma basu Umarnin su nema masa auran Laila wajen Waliyanta.
Yana Tambayansa yasan da Labarin Domin shima Takawa bai nemesa ba Sulaiman yace eh ya sani Daganan bai kara cewa komai ba shima Abba bai ce ba ya Riga ya gano bakin Zaran Zabba"u taje kargi kuma itace ta taso da wannan mganar.
Kwana Uku tsakani aka Sake zama Tsakanin Su Sa"idu da Waliyan Laila Tunda duk abun gidane anan Fada Maimartaaba bai karban ma Sulaiman auran Laila wannan karom ba su Sa'idu yabama wannan Damar sun biya Harda da Sadaki da kayan na gani ina so akwati cike da kaya Sai Kayan al"adun na Sarauta sun yanke Lokaci nan da wata Daya za"ayi Taron Bikin kamar yadda suka sani Kowani Dauri aure da Taron Biki ana Gudanar dashi anan Fadar Maimartaba ne..
Hajiya Zabba"u da Hajiya Salame da sukaji wannan Labarin bazatan kamar su Zuba Ruwa akasa su sha,Abazata sukaji mganar Domin ko Iyayen Laila bai nema ba Waliyanta masu Ahalin aurar da ita suka gama Komai Ranar bakinsu kamar Zai Tsage Saboda Murna Laila kuwa sai da tayi suman Dadi Burinta na Shekaru Takwas yau Allah ya Cikamata zata zama matar Sulaiman Abunda take Buri kenan Domin aduk Duniya Sulaiman ne taji tagani Zata iya Zaman aure dashi Domin shine Namiji kwara Daya da ke da abunda take so wajen Namiji Saboda Jiransa yasa har Degree dinta tayi a Jami"ar Jos Ta kuma yi Service dinta aiki ne bata Fara ba,Sannan bata Cire rai da Sulaiman ba saboda Mahaifiyarta da Hajiyar Sulaimam sun Tabbatar mata da Cewa sai ta auri sulaiman indai suna Numfashi..
Hajiya Zabba"u ta Kira Sulaiman tana ta sakamai albarka Kamar ta Hadiyeshi Saboda Murna shidai bai iya cewa komai ba ya karbi wannan kaddaran nasa ma akaro na Biyu..
Ko Hajiya karama Daga sama Taji mganar Hajiya Zabba"un ke Fadamata su fara shirin Bikin Sulaiman da Laila kannensa suna ta Murna Barin ma Safiya taji Labari Tunda kamar itace Yar Shawaran Hajiya Ba wanda ya nuna adawa da auran saboda yasan Yadda ZAta kwashe dashi Hajiya Zabba"u shiri take sosai saboda tace wannan karon ne Sulaiman zai yi aure.
Abba na gefe ya zama dan kallo Domin yaje kargi sun Zauna da Takawa ya Fadamai yayi shuru da bakinsa ayi Bikin nan Lafiya Allah Daman chan ya kaddara Laila Matar Sulaiman ce Shiyasa ya kawo ido ya Saka mata Kuma taji Dadin haka ita gani take tafi kowa sa"a Burinta ya Cika alokacin Dataso kuma komai yana Tafiyan mata ba Gardama.
Bangaran Sulaimam bai wani Shirye Shirye ba Aikinsa kadai ya saka gaba sai  Hajiya Zabba"u ta Kirssa tace suna Bukatar kudi na Hada Lefe Dole ya Dauka ya bata Saboda samun Salama har kuma lokacin bai gana da Amaryan ba wacce shi Rabon Daya ganta anfi Shekara Biyar Tun zuwansa Abuja shi da Sunaira Lokacin datayi arba"in din Wasim Rabon Daya saka Laila a idonsa Tunda ba wanda ya Damu da hakan shima ya Share.
Baisan cewa Hajiya ta Nuna Bukatar Sulaiman yaje su gana da Laila Hajiya Salame ta hana lamarin ta kawo uzurin a kyalesa kawai Kada a Wahalar Dashi abari in Anyi auran ai Shikenan an gama mai Wahalar da Haka suka bar mganar har ga Allah Hajiya bata kawo wani abu aranta ba ita kuma Hajiya Salame aiki ake mata mai Tsanani kan Yadda Laila Zata Samu mallakan Sulaiman a Tafin hannunta kuma Sharadin aikin bazasu hadu da juna ba sai ranar da aka kaita Gidansa aranar zasu hadu da juna aikin zai kama,Daman ai Ta Dade tana jiran wannan Damar Har garin Maradi wata kawarta ta Rakata sukaje saboda Laila ta samu yadda Take so bata Fadama kowa ba Daga ita sai kawar tata sai Allah ko Laila bata sani ba Shima yana Cikin Sharadi bazata sanar da ita ba sai Ranar da za"a kaita Gidan Sulaiman zata Fadamata komai ta kuma Damkamata mganin da nan da kwana Uku Kawarta zata koma chan Maradin ta karbo mata wato makarin aikin da akayi mata kenan ita bazataje ba Saboda Hidiman Biki kuma Kada ta bada Kofar da za"a Fahimci wani abu.
Sunaima Duk bata san Wainar da ake Toyawa ba,Su Inna dai sun sani Abba ya Kira Baba sun yi mgana Inna taso ta Kira Sunaima tazo Gida ta kara mata Fada sai Baba ya hanata yace ta Kyaleta Gidan auranta ne ta iya gwagwarmaya ita kadai Watarana sai Labari.
Itakuma bataji Labari ba Tunda ba Haduwa da Sulaiman din take ba sai Bikin na Saura kwana Goma Ranar ta Shigo Kitchen daukan Ruwa taji Samira na bama Magajiya Labarin Jiya su Hajiya Uwani suka kai kayan lefen Laila mai kama da an Bude Shago Jos data ga Shigowar Sunaima ne ta kara kaimi wajen Labarinta Tana Fadin nan da kwana Goma Hajiya Laila na cikin gidan nan a mtsayin Matar yallabai.
Dataji haka bata damu ba ai Hajiya ta Fadamata Baki ta tabe Daga auran har mai auran baya gabanta.
Dayake Taron da Daurin auran chan Kargi Za"ayi nan din ba wani Shirin da Sukeyi sai dai ana Saura Sati Daya Biki su Hajiya Jamila suka zo suka gyara Sama Shashen Sunaira da bata Taba amfani dashi ba da Kamfanin shirya Gidaje sukazo komai sai da aka Fidda aka Sauyashi Harda Falon kasa wannan kuma aikin Uban Amarya ne har suka gama abunda zasu yi suka tafi Sunaima na asibiti chan ta wuni Saboda Aneesa bata da Lafiya tana da aikin Rana batazoba sai Sunaima ta Tsaya ta yi mata aikin nata bawai don Dole bane sai don tasan in ta koma Gida babu abunda Zata yi ne sai Zama su Wasim kuma tasan in suka Dawo makaranta Magajiya zata Kula dasu.
Sai yammah ta dawo ta iske waje duk ya Sauya da gyara bata Tsaya ma batama kanta Lokacin Tambaya ba tasan Dalili Duk da batasan Lissafin ainihun ranar Bikin ba.
Saifullahi ya bama Sulaiman Shawaran yaje ya fada ma su Inna Koda sukaje Baba ya sanar dasu ai Abba ya Kirasa kuma da yardan Allah zai je Daurin auran Inna da Baba sun Dade suna mai Nasiha chan suka kai Dare..
Suna Hanyar dawowa Saifullahi ke Tukin Tunda Motarsa ce ya sallami Sani Tun Dazu,hankalinsa na kan Tukin ya kalli Sulaiman yana Fadin"Angon ranar sati..!
Sulaiman na jinsa yayi masa banza sai chan yace"Iyayenta Mutanen Kirki ne..Nagama yadda Sunairata su ta Dauko ita kuwa wannan Muguwar bansan ina ta Dauko mugayen Hali ba..Ko Alama batasan Imani ba Saifullahi duk Halin da muke Ciki Ita ce Silar shigata Wlh..!
Saifullahi yayi yar Dariya kafin yace"Haba..Muguntar me tayi maka..?in hakane ai Dukkan ku ne mugayen tunda baku sauke Hakkin juna ba..Nidai ina Fadamaka kai ne Sama da ita ka Fara Sauke wannan Izzan naka ka Shirya da Matarka..!
Tsaki Sulaiman yaja bai kara mgana ba Shima Saifullahi sai yayi mai Shuru sun kusa isa Gidan Sulaiman Saifullahi yace"Duka gidan zaku tafi Kargin..?
Sai ya Kauda kansa kafin yace"A"a...ko ni inda zan samu wata Hanya da ba Inda Zani..!
Saifullahi yace"Kama isa..?duk mutanen da muka tara saboda waye..?
Sulaiman yace"Ni ai ban buga katin gayyata ba..kuma ban Turama kowa ba..!
Saifullahi yace"Ni nayi maka na waya kuma na Tuttura maa abokanka..!
Sulaiman yayi karamin Tsaki kafin yace"Kai da Hajiya na rasa waya fara Kasheni..!
Dariya Saifullahi ya saka kafin yace"Angon Sunaima da Laila..!
Harara ya sakarmai yana Fadin"Kama Tunamin ban Fadamata bafa..!
Saifullahi ya kwalalo ido yana Fadin"Ka bari don Allah..!
Yace"Wlh ban Fadamata ba ban sani ba ko taji wajen su Inna..!
Saifullahi yace"In hakane baka kyauta ba gaskiya..!
Sai dai taga amarya kawai..?hakan ba adalci bane..!
Sulaiman yace"Bana ganinta fa Karaye..Binta Dakinta zan yi ita ke Zamana ko ni ke zamanta..?ni Wlh nafi Sati ban ganta ba Tun watarana da Ina Sauko Daga Upstair na ganta ta Fito Daga Kitchen bata ma ganni ba Kullum Tana Daki kamar wata Daddawa..!
Saifullahi yayi yar Dariya Kafin yace"Baka da wata Hujja Mai garin Kargi..gaskiya ka Fadamata yau na ijiye ka gida don Allah kaga fa saura kwana Hudu Daurin auran duk da Har yau bamu ga Amaryan ba..!
Ya karishe Fada Cikin Zolaya Sulaiman ya Mele baki yana Fadin"Kasan Jos ko..?bismillah za"a karbe sosai ko saboda kai abokin Ango ne kafi angon Rawan kafa..!
Gabadayansu sukayi Dariya,Daidai Lokacin da suka iso bakin get din Gidan Sulaiman yace ya saukesa anan basai ya shiga ba.
Saifullahi ya kallesa yana Fadin"Au da wai nazo na tayaka Dannan Kirjin Antynmu..!
Wata Harara ya Sakarmai kafin yaace"Kai da Antyn taka Buraubaku..!
Saifullahi ya rike baki yana Dariya Sulaiman ya Bude Mota ya Fice yana Basarwa Saifullahi na kallonsa har ya Buga Karamar Kofa megadi ya Budemai ya shiga kansa ya gyada yana Fadin"Antynmu ga kishiya Lokaci Daya ga Tsaraban Zagi..Allah ya Shirya Kargi..!
Daga haka ya take Motarsa ya wuce Zuwa Gidansa inda yake zama In yana Kaduna Matarsa ma Firdausi taso zuwa ya Hanata Mamarsa ce kila tace Zataje Kargi Ranar Daurin auran Daga Karaye saboda Sulaiman ai yawuce Amini ya koma Dan"uwa.
Rashin Dawowarsa da Wuri yasa Har su Wasim sunyi Barci shima Shashensa ya wuce yana Kallon Shashen Daya bata Lokaci Wajen Tsarashi an Kullesa nan Hajiya ta bada Umarnin ya Zama Shashen Laila..
Wanka yayi ya sauya kaya zuwa Tattausansu Riga da wando masu ruwan Toka na barci ya Sauko kasa kan Dining ya Zauna magajiya ta Rugo ya Dakatar da ita da kansa ya Hada ma kansa Tea yasha saboda Cikinsa ya Saki,Sai da ya gama yaji Cikinsa yadan Samu Natsuwa bai nemi su wasim ba yasan sun kwanta Falon ba Kowa Sai magajiya itama ta shige Ciki Sai Samira datake Dakinta Tana Barci yanzu ta Daina Dauko Rahoto Tunda aikin gama ya gama..
Hannunsa cikin Aljihun wandon Barcinsa ya Tunkari Dakin nata Dakin da indai zai shiga sai ya Tuna mai da Rayuwarsa da Sunaira.
Knooking ya farayi yaji Shuru sai ya Tura Kofar ta Bude ya Tura kansa ya shiga yayi mamakin ganin Haske acikin Dakin Idonsa yafara Wurgawa Saman gadon bayan Kafarsa ya Samu Matsugguni Saman Cafet din Dakin
Bata akan gadon sai dai yaran Wasim da Wasiyya Dukkansu sanye Cikin kayan Barcinsu Tattausasu Wasim na Gefe Ta karamai Filo kada ya Fadi sai Wafiyya Data Rumgume filo ga Littafin Datake karantawa nan Masarautarmu gefen Waffiyya Daga gani Tana kan Jikinta ne da zata tashi ta Saka mata Filo Gudun Rigima Dakin yake bi da kallo Gabadaya Tarkacen kayan wasan yaran ne adakin Daga alanun sun fara Kwaso Duka komai nasu Daga Dakin su zuwa Dakinta.
Takawa ya Farayi Cikin Sanyinsa Har Bakin gado kan Wafiyya ya Duka ya Shafa ahankali kafin ya Duka yayi mata Kiss a goshi haka shima yayi ma Wasim ya Mike kenan sai idonsa yakai ga Littafin Datake Dubawa ya Saka Hannu ya Dauka yana Duba Sunan mamaki ya kamasa Daman Tana karance karance.?in bai manta ba Itama Sunaira har sai da ya Fara mata jan ido ta Rage shegen karatun karyan Masu Novel din nan akallah dai yau akaron Farko yaga Abunda sukayi kamanceceniya da juna.
Yana Shirin maida mata littafin yaji Bude Kofar Tiolet da Fitowarta da Sauri ya ijiye littafin ya Waigo suka Hada ido Hudu.
Sanye da kayan Barci itama Riga da wando suma masu Ruwan Toka masu Taushi sosai ta Boye gashin kanta Cikin Tattausan Hulan barci sai Ramarta da tsayinta ya kara Fitowa.
Saurin Dauke kansa yayi saboda Kare mata kallon Da yayi itama Hijabinta Dake saman Wardrope dinta Taja ta Saka Kafin ta Daidaita Tsayuwarta bata samun Zarafin mgana ba ya ce"Dama daman na shigo na Duba su Wasim ne..!
Kai ta kada batace komai ba ya kama Hanyar fita sai ya Tuna da Abunda ya kawosa yasa ya Tsaya Cak kafin ya Juyo yana kallonta Cikin mganarsa yace"Ina so zan yi mgana Dake..Kan wata mgana da nike son sanar Dake..!
Basai ya fada ba tasan bai wuce mganar auransa ba  yasa ta juya tana Isa Gefen gadon Lokaci Daya Tana Fadin"Kan Auran ka ne ko..!?
Da mamaki yake kallonta ahaka kamar bata Lura da abubuwa kafin yace"Ya akayi kika sani..!?
Tana gyarama Wafiyya kwanciya tace"Hajiya ta fadamin zuwan da sukayi..!
Salallami kawai yake acikin Ransa Wato ita Tun alokacin Hajiya ta sakamai Rana baisani ba.
Yakasa mgana ba illah cemata da yayi"In kina Bukatar kudi ko wani abu kimin mgana..!
Bata bashi Zarafin Hutawa ba tace"Kada ka damu bana Bukatar komai...Allah ya bada Zaman Lafiya..!
Mamakinta ya kamasa Lalle tacika Muguwa ko ajikinta Harda Allah bada Zaman lafiya.
Kai tsaye ya kada kai yana Fadin"Zaki Taron ne..?
Da wani kallon kama Rainani tayimai kafin ta Dauke idonta cikin Muryanta mai Sanyi tace"Taro fa kace..?Uhn aiko Lokacin da kaddarata ta Ratsoni cikin Rayuwarka ban yi Taro ba ballatana yanzu da zaka auri yar"uwarka yar masu kudi da Sarauta wacce ta dace dakai ba irina ba..Taro na Wajen masu abin..!
Daga haka ta tsuke bakinta Harara kasan ido yayi mata aransa yana Fadin Ido kamar an saka k'uma abuta.
Afili kuma sai ya Zakuda kafada yana Fadin"Ranar jumma"a ne Daurin auran..nan da kwana Hudu kenan Taron Bikin da Daurin auran a Kargi Za"ayi ranar asabar zasu kawota..Na yanke shawaran yaran zasu zauna dake ranar in kuma bakya nan sai Akai su gidan Inna magajiya taje chan Tataya inna Kula dasu Samira kuma sai ta zauna tayi abincin Saukan Baki..!
Kai Tsaye tace mai"Ranar bani da aiki..Sai Monday in kamin Izinin nima Zan bisu Wasin sai muje gidan Inna mu kwana sai washegari mu dawo..!
Kallonta yake yi Cikin mamaki Dama Tana mgana haka kansa ya shafa da Hannu daya kafin yace"Inna Zata bari..?
Kai tsaye tace"In ka bada Izini zata bari mana..!
Kansa ya gyada kafin yace"Shikenan..!
Daga haka ya Juya ya Fice ta Bisa da kallo Hawayen idonta sun Taru tayi saurin maidasu Tunda Kaddara ta Hadasu waje Daya basu taba Doguwar mgana dashi ba sai yau..Gwara su je gida su kwana da ta zauna ita kadai tana son ganin Inna tana Bukatar zuwa Gida Sosai acikin Ranta tana kewar Baba da Ahmad.





*Janafty*

MIJIN KANWATA(K'ADDARATA)Where stories live. Discover now