*MIJIN KANWATA..*!
_(k'addarata)_*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*_Wannan Shafin gabadayansa Sadaukarwa ne gareki *ZAINAB ABDULWAHAB* Nagode sosai bisa karamcinki gareni Allah ya Rubanya miki Sister Allah ya biyaki da Aljannah Firdausi Nagode kwarai_
*Page 28*
Tunda suka zo bata kara saka Sulaiman a idonta ba sai dai da Daddare sunyi waya dashi ya kirata yana tambayanta ba matsala..?tace bakomai yace to sai da safe in zasu wuce zai shigo suna nan zasu kwana gidan su Saifullahi daganan ya tambayi yara tace gasunan kusa da ita Dayake Dayan Dakin aka saka mata Katifa ita da yaran da gajiya yasa duk suka Bige suna barci ita kanta agajiye take Tun da rana take son ta samu wani wajen da zata kwanta bata samu ba Saboda Taron jama"a sai da Yammah tayi suka ragu da Khadijan ta Lura sai faman gyangyadi take saman gadonta tasa aka gyara mata Dayan Bedroom din Dake Dauke da Katifa.
Bata yi barci ba sai da tayi wanka Saboda bazata iya kwanciya haka ba,Allah yasa akwai Tiolet adakin Samun wankan yasa jikinta yayi mata Dadi tayi barci sosai cikin Salama kamar jiya ba Sulainan daman babban Tashin hankalinta yace zai Rabeta wannan abu ne babban mtsalanta ayanzu ta kuma rasa kamo bakin Zaren.
Gari na wayewa suka fara shiri Saboda da wuri zasu koma,yayar Mejego ita tayima su wasim wanka ta Shiryasu ita kuma Sunaima ta kintsa kanta Cikin Shigar Jallabiya wacce Cikin wadanda Hajiya karama ta bata ne Lokacin da sukaje Abuja Sai tayi Roling da Vail din Rigar.
Tunda tatashi da Safe taji bata Sha"awar cin komai sai Waina mai kuli,Kuma bakazo waje ka Dora musu Dawainiya ba yasa ta bari sai ta koma gida ta Kira ko Breakfsat din da akayi musu bata iya cin komai ba Zuciyarta taji tana wani Dum yanzu ko Kamshin Madara bataso,Yaran kadai suka sha Tea din da Soyayyar kwai Karfe 9am na Safe Su Saifullahi suka Shigo gidan,Domin Sulaiman yaga Baby wacce taci sunan mahaifiyar Saifullahi Hauwa"u zasu rika Kiranta da Jidda.
Lokacin ba kowa agidan Daga kanwar Maman ita khadija sai yayarta guda Daya da kanwarta kuma suna Haraban gidan suna Soyan Naman Raguna Biyun da Saifullahi ya yanka koda suka shigo Sunaima na Bedroom Khadija suna gaisawa Jidda na Hannunta sai ga Saifullahi nan suka gaisa kafin ya karbi Yarinya ya fice yana Cema Khadija ta Dauko mayafi su gaisa da Sulaiman.
Tare suka fito falon da Khadija suka iske su Wasim sunga babansu sun makale masa,yana Rike da Jidda yana kallon Wasim yace"Yaya ne Abba na..?kana son bby ne..?
Da sauri ya Daga kai yana Fadin"Eh Daddy...Anty tatafi da ita..!
Sai da ya Dago ya kalli Sunaina Dake gaisheshi ya amsa yana Fadin"Lafiya lau..To ke kin ji wasim na son Bby..Yace mu tafi da tasu Karaye..!
Mirmishi tayi tana Daga tsayen Kofofin Hancinta Take Budewa Saboda Kamshin Soyan naman Da ake yi a tsakar gidan wani irin Dadi yake mata Wani salama take samu yasa bata bama Mganar Sulaiman muhimmanci ba tace"Su taimaka su bamu aron Jidda ko don Wasim..!
Sulaiman ya kalli Khadija yana Fadin"Maijego kinji fa me tace..?ke sai ki bata..Koda yake nasan ko kin bata karaye zai ce A"a in kina son Bby ki Haifi naki..!
Saifullahi ya rike baki yana Fadin"Kaji Sharri..Salon Sunaima taga bakina..Wlh kada ki yarda da mganarsa ni me baki Jidda ne har Abada daman shi yake son ya Fadi haka..!
Ya Karishe fada yana Hararansa Dariya Sulaiman yake yi yana kallon Sunaima da ita hankalinta bai kansa Shima ya Lura da haka ido ya saka mata kafin yace"Are u ok..?
Da sauri ta gyada kai,jinjina kai yayi ya juya ga khadija yana mata barka da Fatan Allah ya raya ta amsa Lokaci Daya tana mai godiya abun Arzikin da suka gani yace bakomai an zama Daya.
Sai Hirar ta koma tsakanin Saraki da Saifullahi,Yaran kuma suna ta wasansu a falon khadija na gefe ita da Sunaima da kamshin Soya ya Tafi da ita sai Bude Hanci take yi bayan Son cin Waina yanzu nan kuma so take taci wanchan naman miyanta Har Tsinkewa yake yi gabadaya tama rasa natsuwarta Daga unh sai A"a take cema Khadija in tayi mgana,sun bata Lokaci sai wajen 10am sukayi Shirin Tafiya da aka basu kayan karyawa Sulaiman yace Mama ta cika musu ciki sosai Alhamdulillah.
Sallama sukayi da juna Sunaima da Khadija Sulaiman ya Dauki kayan su ita da yaran suka fita waje ita har Haraban gidan ta rakota ita da yan"uwanta suna ta mata Fatan zuwa gida lafiya Sunaima kamar tace Khadija ta Sammata nama sai dai batace ba kamar kuwa ta sani sai gashi yayarta ta kawo Nama dayawa aleda ta bama Sunaima ba yawa kamar ta saka Sunaima acikin Aljannah haka ta Rumgume Ledan nama tana ta godiya Bata fito ba tana daga bakin get take Daga musu hannu Saifullahi sai gobe Talata zai taho ammh Tare suka Tafi dashi gidan Mama suka mata sallama itama da yan kulle kullenta na su yaji kubewa daddawa da Garin kunu da Sauransu ta bama Sunaima su Wasin kuma ta basu chuculate da yawa tana ta Godiya da abun arzikin Hajiya sun zo sun kawo mata kudi Daga wajen Abba bayan Hidiman da suka kawo ma megejo itama Har bakin Mota Ta rakosu tana saka musu albarka Ita da Saifullahi suna Tsaye har Motarsu ta bace ma ganinsu.
Sulaiman da Sunaima na gaban Motan yaran suna baya suna Bikin Chaculate dinsu Sulaiman wani abu ya bashi mamakin ganin yadda Sunaima ta Rumgume ledan Dake hannunta ga kuma wanda Mama ta basu Warin Daddawa duk ya ishesa Duk da mai kyau ne ammh ai yana jin Tashinta rabin Hankalinsa na wajen Tuki ya waigo yana kallonta Lokaci Daya yana Fadin"Wai ita ledan Daddawa ne kika Rumgume sunaima..?warinta ya isheni ko zamu tsaya ne na sata cikin Booth..!
Da Sauri Sunaima tace"A"a don Allah ka barmin..Ni wlh Kamshimta Dadi..!
Tafada Cikin wani irin har tana wani Lumshe ido Baki ya Saki yana kallonta kafin yace"Ita Daddawan ne ke kamshi..?
Kai ta gyadamai tana Fadin"Wlh bakaji yadda hankalina ya kwanta ba nakejin kamshinta..!
Kai Saraki ya girgiza kafin ya maida Hankalinsa wajen Tuki Lokaci Daya yana Fadin"Umh da alamun kila Hancinki ya samu matsala..!
Tana jinsa batace komai ba illah Cigaba da Bude ledan hannunta tana Jiyo kamshin naman da Khadija ta bata Leka Ledan tayi kafin ta saka Hannu ta Dauki Daya ta saka abaki Tana Taunawa Har Bakinta na Haduwa waje daya Saboda yadda Zagin Naman ya Hade da Miyan bakinta Sulaiman kadan ya rage bai buga ma wani mai mota ba Saboda kallon Sunaima da Sauri tace"Saraki Kula..!
Sai da ya Daidaita kansa kana yasake kallonta yana fadin"Miye kike ci kuma..?
Tana Tauna naman tace"Nama ne..!
Cike da Karin bayani yace"Nama kuma..?ina kika samu nama kuma..?
Sunaima na kara Tura wani Naman abaki tace"Naman suna ne Khadija maman jidda ta bani..!
Sulaiman ya Kada kai yana Fadin"Lalle kina son cin Naman nan..Tun amota kya bari mu isa gida ko..?
Sunaima tace"Bakasan yadda Miyau na yake ta tsinkewa bane..Wlh tun da suka fara Soyan naji ya shiga raina in ban ci ba kamar zan mutu haka nake ji kaga yanzu ji nake kamar amin gafara..!
Cike da wani karin mamakin yace"Ah lalle ba Shakka..!
Haka kawai ya fada ya cigaba da kallonta yadda take cin naman Tun yana Daukan abun wasa har dai yaga bana wasa bane sai ci take ta kusa ma Cinyewa Cikin Wani yanayi yace"Sunaima bazaki bar naman nan haka ba..!kada fa kici da yawa cikin ki ya Lalace..!
Bata bama mganarsa Muhimmanci ba tace"Babu abunda zai min Infact ma ban ci komai ba Tun jiya..!
Kai tsaye yace"Saboda mene..?
Kai tsaye tace"Ni yau waina mai kuli nake son ci..Bana ko son warin madara yanzu da ban samu ba na samu wannan naman kamar an min Gafara Saraki..!
Zuwa wannan Lokacin ya fara wani Tunani Cikin kara nazarinta yace"Yaushe kika fara daina shan madara..?
Sunaima tace"Oho ni ina na sani..!
Daganan bata kara mgana ba tacigaba da Cin namanta shi kuma yana kallonta Rabi hankalinsa na wajen Tuki sai da yaga zata cinye naman Duka kana ya shammaceta ya warce ledan yana Fadin"Ai ba ke kadai aka bama Naman ba malama..!
Kamar zatayi kuka tace"Kayi hakuri..In muka koma gida zan siyo nama Magajiya ta soya muku..!
Yana yar Dariya yace"munki wayon..Ke kibari in muka koma su soya miki mana..!
Tana sosa giranta tace"Ai wannan nake so..!
Ko sun soya ba lalle naji ya shiga raina ba kamar wannan..!
Saraki yace"Eh muma haka na suna muke so eye..!
Tayi magiyan ya hanata yana mata Dariya ta koma ta Juyar dakai tana Tura baki shi kuma ya amsa ne yaga Abun nata ya wuce hankali kada yayi mata illah yaran duk sunyi barci.
Daganan Sunaima sai ta fara gyangyadi,sai barci Sulaiman nata mgana yaji Shuru ya lekata yaga tayi barci afili ya Furta"Naga alot Change a wajen matar nan fa..!
Haka ya fada afili yana cigaba da Driving sun kusa isa kaduna Sunaima ta Farka Allah yakai idonta kan mai Gurasan tashan nan mai kuli da Sauri tace"Saraki Tsaya..Tsaya gurasa..!
Shi da Farko ma har ya Firgita sai da tace Gurasa ya Sauke Numfashi yana Fadin"Naman bai cika cikin ba..?
Da Sauri tace"Plz kakirasa Kada yayi nisa..!
Gangarawa yayi gefen titi yayi parking yana Fadin"Anya Sunaima..Bazaki bari mu koma gida su magajiya suyi miki mai Tsabta Duba wannan fa duk tasha Ranar tasha..!
Sunaima tayi Kamar tayi kuka tace"Wlh ita nake jin ci..In ba ita ba ba zan iya cin wacce kake mgana ba..!
Sai Kuka yana ganin Haka ya Bude Motar ya Fice yana Fadin"Meye na kuka..?bari na siyo miki..!
Tana kallonsa ya fita ya isa wajen mai Gurssan ya siyo mata na Dari Biyar ya kawo mata tun kafin ya Tada Motar ta Bude ledan ta faraci Tana wani Mirmishin jin dadi Sulaiman kallonta kawai yake yi kafin ya Kada kai ya Tada Motar suka cigaba da Tafiya Yana jinta tace"Saraki muna kwarya..!
Da Sauri yace"Aci lafiya..!
Mamakinta kawai yake yadda take cin sa ba ruwanta bai gama mamaki ba sai da yaga ta Bude Glass ta Jefa Leda ido ya Zaro yana Fadin"Sunaima meke Damunki ne..?naga kin Sauya ne..?
Sai Alokacin ta kallesa Tsam kafin ta Yamutsa Fuska tana Fadin"Ni ma bansani ba..Saraki ruwa nake so..!
Bai kalleta ba akwai Ruwa agefensa na Gora ya mika mata karba Tayi kafin ta bata rai Cikin Shagwaba tace"Saraki ba wannan ba..Irin na Rijiya mai Gartsi din nan Kagane shi..!?
Kokarin Rage gudun Motan yake yana kallonta kafin yace"Ban gane sa ba..!
Da Sauri tace"Irin na Bohol burtsatse din nan da ake Bugawa Wlh Saraki irinsa nake so nasha..!
Wani irin Nauyi yaji a kirjinsa Yana kallonta yace"Babu ki sha wannan kafin mu koma gida..!
Juya Ruwan ta farayi kamar bazata sha ba taji yace"Kisha kada abunda kikaci ya Danne miki Dan zuciya..!
Ba gaddama ta Bude ta fara sha shi kuma kai ya Kauda yana Goge kwalarsa Sunaira ya Tuna Tabbas in ya Hasaso Daidai Sunaima ciki gareta itama bata sani bazai manta Cikin Wasim ba Sunaira Ruwan Rijiya ta Dinga sha har ta Haihu bata son Ruwan gora ballatana na Leda Sai yanzu ma wasu abubuwan na Sunaima ke dawomai Allah Sarki koda yake yawan fada bai kawo Rabon kaddaransu nan kusa ba Allahu akbar wannan Rabon Dake Tsakaminsu shi ya Dauke Sunaira ashe..Allah ya jikanta da Rahma..!
Sama sama yaji Muryanta tana Fadin"Saraki zuciyata na tashi Zan yi amai..!
Saurin kallonta yayi tana Danne bakinta da Sauri yayi parking yana Fadin"Subhanallah!
Ko kafin ya fito Daga Motan ya Zagayo ta Bude ta fito nan bakin Motan ta Durkusa ta fara kelaya amai Riketa yayi yana Mata sannu gwanin ban Tsausayi sai da ta amayar da Duka Naman da Gurasan dataci nan ya barta ya koma Mota ya Dauko Ruwa ya zuba mata ta wanke bakinta shi ya Taima ka mata ya wanke mata gaban Rigarta daya baci Fadi take"Saraki sai da nace bazan sha ruwan nan ba bashi nake so ba..!
Tafada sai Hawaye Jikinsa ta Fada Saboda Jiri take gani Riketa yayi yana ta mata Sannu da kansa ya Taimaka mata ya maidata Mota kafin ya koma ya Shiga bangaran Direba yaja suka Fara tariya yana ta jera mata Sannu aransa yana kara Tabbatar da Zarginsa.
Inda Allah ya taimaka sai ta samu barci Har suka isa gida,Sai da ya tasheta Daga ita har yaran suna isa Sunaima tace yunwa take ji ya bata Sauran naman nan taci yace a"a kada ta kara yin Amai ai sai ta sakamai kuka Dole ya bata taci bata sha Ruwa ba tace sai irin wanda take so ya kalleta yana Fadin"ina zan samu wannan Ruwan Sunaima..!.?
Tana Daga kwance tace"Wajen Inna..akwai Bohol a bayan gidanmu don Allah Saraki..!
Dolensa ya Dauki key din Mota ya tafi Anguwan Dosa sai dai inna ta gansa kwatsam,alokacin tasan ma sun
Dawo Duk da Daman Sunaiman tace mata yau din zasu dawo.
Shi kanshi Sanda zai Fadama Inna sakon kansa na kasa Inna na jin haka sai da Tayi hamdala acikin Ranta kenan gabadaya ya"yanta ita suka Dauko itama indai Tana da Ciki bata shan Ruwan gora dana Leda sai mai Gartsi Cikin jin kunya ta Shiga Daki suna dashi dayake dashi suke girki Ahmad ya Cika ko"ina kafin ya fita Cikin wani karamin Botiki ta Diban mata ta kawo mai kenan Sunaima ta Kirssa Sulaiman tace ya bama Inna Wayar bayan sun gaisa ta mata Hanya tace me ta girka..?inna tace Danwake da Miya ta Tuna tun abaya Sunaima batacin Danwake Ranar da tayi shi ita sai dai ta kare da cin awara Ammh sai gashi tace tana jin ci ta bama Saraki ya kawo mata Inna tace shikenan.
Sai da yadan jira inna ta Zubamai kana ya mata sallama tana tambaya su wasin yace mata suna gida yau suma sun rasa makaranta ammh Gobe Daga makarantar nan Direbansu zai Kawo su.
Da haka suka Rabu Sunaima taji Dadin Danwaken nan taci ta Rage na anjuma Ruwan nan kuwa kamar tana shan Zuma ko zamzam haka take ji Sulaiman dai sai kallonta kawai yake yi sai da yaga taci har tayi wanka tayi Sallah batayi amai kana hankalinsa ya kwanta Shima wankan yayi ya Fice masallaci Daganan zai shiga kamfani yaran kuma suna Wajen magajiya ita tayi musu wanka ta basu abinci.
Zuwa Yamma Sunaima taji ta wartsake Sulaiman nata Kiranta yaji ko ta na lafiya tace mai Lafiyanta kalau Gata ma zata shirya tatafi wajen aiki ya Turi mata Sani.
Sulaiman yaso ya hanata zuwa sai tace ita fa Lafiyanta kalau babu abunda ke Damunta Shiyasa ya kyaleta da kansa yazo ya kaita Sani na Gida bai riga ya kirssa ba Sai gobe,Abun har Dariya ya bama Sulaiman ta Dura Ruwanta agora da kulan Danwake,wai zataci a asibiti shidai bai ce komai ba Jira yake gobe Ya matsa mata suje asibiti Domin a Tabbatar mai da abunda yake Zargi.
Washegari ma da Safe shi yaje ya Daukota suna Tafiya a hanya tace ya Tsaya mai suyan kosan manja ta nunamai tace ya siyo mata Har Dankali ya ya iya haka ya Fita ya Siyo mata ta Hada sai ci take ta Hada da Ragowan Ruwanta na jiya,Danwaken dai ta Cinye gabadaya Tun jiya Aneesa nata mata Tsiyan Gulmarta tatashi kenan ita batace mata komai ba sai Dariya Aneesa ita kanta taga Ciki ajikin Sunaima abunda yasa batayi mganar ba ta zata Sunaimar tasan da abunta.
Su wasim Ranar gidan Inna Direbansu yakaisu bayan ya Daukosu Daga makaranta Sunaima kuma tana Gida Ranar Samira ta saka tayi mata Danwake sai kuma da aka gama ta kasa ci karshenta dai sai Inna ta Kira tace tayi mata Danwake,Ahmad ya kawo mata da Ruwan nan Haka kuwa akayi Inna tayi mata Ahmad ya kawota mata kamar an sakata a ljannah Yaji da Daddawa ta Zambada aciki tana ci da Saraki ya dawo ya gani kamar yayi amai Daddawa Danya da Yaji acikin Danwake Tabdijam.
Haka sukayi ta fama Har satin nan ya kare Sunaima Danwake in ba na Inna ba bataiya ci kullum da Safe sai taci kosan manja dasu Dankali,Cima kala kala dai Ruwa kuwa bata shan ko wani iri sai mai Gartsi Sulaiman in yace suje asibiti sai tace ita Lafiyanta Kalau shiyasa ya kyaleta asatin ta fita aikin Dare ta koma na Safe Ranar Monday da Safe Tatafi wajen aiki Sani ya kaita Saraki da wuri ya fita suna Meeting a kamfani Saifullahi nata Kiransa.
Lafiyanta Kalau taje wajen aiki Sai taga Sister Fatima tazo da Fankasau da Miya sai taji ranta ya Biya tace ta san mata taci shikenan kamar taci Bala'i zuciyarta tatashi kamar zatayi amai Ruwanta tasha Ashe kamar ta Kira abun sai amai Sai jiri Dayasa Dole Aka bata gado a maternity Likita yazo ya Dubata abunda ya bata mamaki yadda Sister Aneesa ke Fadama Likitan tana da Juna Biyu.
Tana Daga kwance Cikin mamaki ta ke kallon Aneesa Dr Ukasha ya kalleta yana Fadin"Sister Sunaima..Yau kina mtsayin patient nefa..Cikin ki wata nawa ne .?kin yi Scan ne..?
Tana Daga kwancen hannunta Zafi yake mata Sister Fatima ta saka mata Drip Tace"Ni bani da ciki Dr..!
Kallon kallon Tsakaninsu kafin Dr Ukasha yace"To ya haka..?Sister Aneesa tace kina da juna Biyu ko baki sani bane..!?
Kai ta gyada Aneesa ta kalleta kafin tace"Wai ke daman baki san kina da Ciki ba..?
Sunaima tace"Ban dashin ne yasa ban sani ba..!
Aneesa tace"Yau aiki gamai kareka..Dr ayi mata Test sai ta Tabbatar..!
Sunaima batace komai ba gabanta Fadi yake tana kara auna mganganun Aneesa da yanayinta Sai alokacin ta Tuna wajen wata Biyu kenan Bata ga Al"adanta ba kamar Allah ya mantar da ita bata Tuna ba sai yanzu.
Jininta aka Diba zuwa Lap ita tana nan kwance tana Nazarin abunda Result zai nuna,Barci ya Dauketa Saboda Drip din da aka saka mata.
Har Wajen uku tana asibitin Sulaiman yaji Shuru bata kirasa ba sai ya Kirata Jakarta na Hannun Aneesa ita ta Dauka ta Fadamai Cikin Tashin Hankali ya baro kamfani Shi da Saifullahi zuwa asibitin.
Koda suka isa Aneesa ita ta taresu da albirshin din Tunda Tundazu Aka kawo Result din Sunaima na barci bata tashi ba.
Sulaiman Duk da yana Hasheshen haka Daya gani Sunaima na Dauke da Cikinsa na Sati takwas Farinciki ya kasa barin ransa Bakinsa yaki Rufuwa Saifullahi ya kallesa yana Fadin"Congratulation Kargi..Akallah dai yanzu Lokacin zuwa Kargi yayi kenan..?
Sulaiman na Dariya yana fadin"Ofcourse..yana Damke hannayen Saifullahi Cikin Farimciki 5k ya bama Aneesa Tukwaici sai Murna Take Office din Likita sukaje ya sake musu bayani da Shawarwarin Sunaima ta samu bedrest na Sati Biyu agida Ta Rubuta ta Takarda zuwa gaba na insha Allahu ba mtsala sai manganunan karin jinin Daya Rubuta mata yace in ta Farka zasu iya tafiya gida..
Suna komawa suka iske ta Farka yadda Sulaiman ya Rumgumeta gaban abokan aikinta da sauran patient ya kara Tabbatar mata Abunda Aneesa ta fada ya tabbata Tana Dauke Da Cikin Sulaiman sai taji wani Farinciki.
Dago da ita yayi yana Fadin"Congratulation MRS SULAIMAN ALIYU KARGI....!AND THANK YOU SO MUCH...!
su Saifullahi ne suka amsa da Ameen Sunaina kanta na kasa ta kasa mgana Aneesa ta Cire mata kalulan hannunta Sulaiman ya Taikamata ta Mike suka Fita Daga Dakin ana taa mata Fatan Samun Sauki,Har bakin Mota Sistrer Fatima da Aneesa suka rakasu Sulaiman ya karbi Jakar sunaima Da Goran Ruwanta zuwa gida.
Ranar bai koma kamfani ba,Sunaima kamar ta nutse saboda ba wanda bai kira ya Fadamawa ba Har da Baba da Inna ko kunya baya ji Inna Daman tana Zargin haka ta kuma tababbatar sai da tayi sujjuda ta godema Allah tare da addu"an allah ya jikan Sunaima.
Hajiya dataji Murna kamar mene Duka gidan ma Sulaiman ko kunya shi ya kira Duka kannensa ya Fada musu suna ta tayashi Murna Koda ya kira Abba ya Fadamai Abba na Dariya yace ya makara Hajiya karama ta Fadamai Fatan Allah ya ingatamai yayi mai.
Maimartaba ne kadai bai kira ba yana so ne suje Kargi da shi da itane Saboda ya tabbatar da shi din Yaci sunansa ne ba Raggo bane.
Daga dare zuwa Safe Sunaima batasan adadin wayar data amsa ba na Kannen Sulaiman harta Abba sai da ya Kirata ya mata sannu Baba ma haka kunya duk ya gama kamata Ga kunya Ciki ga kunyar yadda Ta rika nuna Mijin kanwarta ne bataso sai gashi Har da Cikinsa acikin jikinta Shi ko ajikinsa sai Murna yake da kansa ya Sanarma Magajiya da Samira bayan ya Fada musu su kula da komai Sunaima an bata Bedrest ne suma ganin yana ta Murna yasa suka Tayasa Murna da Fatan Allah ya inganta.*Janafty*
DU LIEST GERADE
MIJIN KANWATA(K'ADDARATA)
Action_*Wata irin KADDARA CE wannan..?Kaddaran data Ratso MIJIN KANWATA cikin Rayuwata..?wanda yake matukar girmamani kamar yadda Kanwata SUNAIRA take girmamani?Meyasa kaddara ta zamo tayi min haka..?meyasa sai ni..?Taya zan iya zama da wanda muke jin nau...