*MIJIN KANWATA..*!
_(k'addarata)_*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*_Kuyi hakuri da Rashin jina kwana Biyu wani Sabgace tatasomin ban yi alkwarin samun update kullum ba sai dai ku karbesa duk lokacin da kuka gansa..Nagode..!_
*Page 3*
Sai da yayi wanka yayi Sallar Isha"i ya saka Madaransa da Furansa cikin karamin Fridge din Dake Falon nashi kana ya fito Domin ganin ya"yan nashi Sanye yake da Tattausansun Riga da wando na barci masu ruwan Duhuwa na kamfanin PJM,hannayensa Cikin aljihun wandon Barcin ya sauko kasa da Magajiya yaci karo Tana ta Safa da marwa Tsakanin Kitchen da Kayattacen bangaran makeken Dining din cin abincin Dake chan yammah da Falon.
Har ya sauko bata ma Lura dashi ba Magajiya mai aikinsu ba yarinya bace a kallah a shekaru zata bama arba"im baya Daga garin kargi take Mijinta Rasuwa yayi kuma bata taba Haihuwa ba kuma Mijin nata shine mai kula da Dabbobin Maimartaba alokacin bayan Rasuwarsa Magajiya ta Dawo Karkashin kulawar Fada cikin Hadiman Uwargidan Sarki Fulani Shime bayan Haihuwan Aliyu Wasim kenan da Shi sulaiman din ya Bukaci Samun mai taimaka ma Sunaira awanchan Lokacin Maimairtaba yabada Umarnin a basu Magajiya.
Tun achan baya akwai Girmama juna a tsakaninsu dagashi har sunaira suna mata kallon Uwa ce shiyasa take jin Dadin Zama dasu Tayi kukan Rashin Uwardakin iri Hajiya Sunaira,Ammh ko ayanzu bazata Dora komai game da Sabuwar uwar Dakin nata ba abu Daya ta sani bata da kwarammiya da Yawan mgana kamar Sunaira a kowani Fanni suna da bambamci Dabi"u da kuma Hallaya.
Ta duka tana Jera Filet din saman Dining din taji mganarsa Daga sama.
"Magajiya Barka da aiki..!
Yafada cikin kyakyawan Sautinsa da Hanzari ta Juyo tana kallonsa Lokaci Daya ta maida kanta kasa tare da dan Rankwafa Tana Fadin"Barka da Fitowa Sarakin Maimairtaban Kargi..!
Haka take Kiransa daman dan Murmusawa yayi kafin yace"Magajiya bana son Sarakin nan fa..Maimartaba Kadai ke iya Kirana na amsa..Sunana Sulaiman kuma don Allah ki Daina Ramkwafamin in zamu gaisa nan fa Gidana ne..Ba Fadar Sarkin na Kargi ba!
Ya karishe Fada Muryansa da alamun Zolaya ammh bai nuna saman Fuskarsa ba Kasa ta karayi da kanta kafin tace"Amin afuwa Ranka ya Dade..Bana iya kiran sunan mai garin Kargi gabadayane..Sunan yana Daraja da Kima awajena..!
Bai mata mgana ba illah kafada Daya Daga Daidai Lokacin da Samira ta Fito Daga Dakinta wani kallo yayi mata mai Cike da Tsana da gargadi Daya sata Zubewa tana mai barka da Fitowa kallo Daya yayi mata ya kauda kai Daidai sanda Magajiya ke Fadin"Saraki nan Zakaci abinci ko na Haura maka dashi saman Dakin ka ne..?
Kansa ya Girgiza yana Fadin"Am ok..Fura zan shan kafin na kwanta Ina yaran nan suke..!?
Magajiya tace"Mai sunan Hajiya tayi barci Tun dazu Datagama Rigima Hajiya ta mata wanka sai ta samu Barci..Mai sunan babban Mutum kuma yana Dakin nasu yana kallon yan aljanun nan nasu..!
Jim yayi yana kallonta batare da yayi mgana ba Har zai ce wani abu sai ya Fasa ya wuce ya Fara Taka Lallausan Cafet din kasar Italian Dake malale atsakar kayattacen Falon Dayaji kayan More Rayuwa.
Bayaso yayi mgana saboda yar aiken Hajiyarsu dole ya Fara Kafa Kafa da ita Domin bashi da ikon korarta faruwar hakan kamar ya siyan ma kansa Tikitin Fadan Hajiya ne da kuma Kudirinta akansa Da Fara Kokarin Tabbatar dashi.
Dakin su Wasim din daya zama Mallakinsu tun dawowarsu gidan,Wafiyya Dakin Magajiya take kwana Hatta Wasim din ma wani Lokacin sai dai shi ya fita Sakin jiki kuma baida Rigima ita ga ta yarinya sannan ga Kiyuwa da Rigima kala kala bata iya kwana batajita Lafe jikin Mutum ba
Koda ya shiga Dakin Wasim barci ya kwasheshi nan Tsakar Falon ga Talabijin nan a kunne ana Haska Cartoon din yara,gabansa kayan wasa ne su Ninja da superderman,da Bindogogi Daga gani dasu ya ke wasa kafin Barci ya Daukesa Tsausayinsa da Tsausayin Ya"yansa ya kamasa Allah Sarki Mutuwace mai Tonon asiri da ba domin Mutuwa ba da yanzu Wasim suna tare da Mahaifiyarsu tana basu kulawa shi kanshi da Rayuwarsa bata zama a Tagayyare ba
Ya kara Tattabar ma kansa Hasashen su Maimartaba akansa ba Daidai bane in suna Tunanin sun kakabamai auran Yayar matarsa saboda sun yi mai gata to wlh kara Gurgurta rayuwarsa sukayi,Domin shi dai bai ga amfanin hakan ba matar da bata wani da amfani acikin Gidan da Lokacin Datake nan da batanan duk Daya yaransa sun wuni Cikin Kadaici su kwana cikinsa Tana chan yawonta da sunan wai aikin asibitin gwannati aikin banza aikin Wofi Shidai Wlh an gama Kasheshi ba Tun yau ba ya Dade da Sanin ya Juyama Rayuwar jin Dadi baya Tun sadda Sunaira ta bar GidAn Duniya.
Cicciban Wasim dim yayi ya Rumgumesa yana kokarin kokuwa da Rauninsa Na Lokaci kafin ya maidasa kan gado,Kayan Jikinsa ya Ciremai ya isa ga karamin Durowansu ya Zaromai kayan barcinsa ya sakamai Barcinsa yayi nisa shiyasa bai Farka ba ya Dade yana Shafa kansa yana Tofamai addu"a ya Dade adakin kafin ya Fito sai da ya Ragemai Hasken Dakin ya karamai karfin A.C saboda garin akwai Zafi sosai Tunda yaga bai ga Wafiyya ba,Tana Dakin wanchan yarinyar mai girman kan tsiya alhalin shi kuma bai Tabataka Kafarsa zuwa Dakin ba Tun bayan Daya tashi ana Sunaira ya koma nata din Har Abada
ŞİMDİ OKUDUĞUN
MIJIN KANWATA(K'ADDARATA)
Aksiyon_*Wata irin KADDARA CE wannan..?Kaddaran data Ratso MIJIN KANWATA cikin Rayuwata..?wanda yake matukar girmamani kamar yadda Kanwata SUNAIRA take girmamani?Meyasa kaddara ta zamo tayi min haka..?meyasa sai ni..?Taya zan iya zama da wanda muke jin nau...