MEDIA (DAN DALIN SADA ZUMUNTA)

123 11 8
                                    

*MEDIA (DAN DALIN SADA ZUMUN TA)*

Na
*_Nanah khadii💅🏽*_ 🛍️

*Marubuciyar👇🏽*

*Cousins ne*

*Aruwan sama* ( *kaddara tasameni* )

*Auren kiyayyah*

*Hamdan paid book*

*Agarin son Duniya*

*nd now*

*Media(yanar gizo)*

_Bismillahir~Rahmanin~Raheem_

Alhamdulillah inayima Allah godiya daya bani ikon sake dawowa da sabon book dina mai suna *MEDIA(* *YANAR* *GIZO)* banyi wannan littafi dan cin zarafi ko yi dawani ba aa kodaya idan ma wani abu yazo daya da lbrin ki/ka kayi hkri akasine 🥰🥰

_Wannan page din gaba dayansa sadaukarwa ne ga_

*Habibbty Nah Asli smasher💕* 💕 muna jiran new novel hua🙄🙄

"Cikin garin kano knan ta dabo tumbin giwa kodame kazo anfi garine mai cike da d'umbin mutane,ruwa sauka a garin yayi kyau sosai dayake wajajen k'arfe 3pm na yamma.

wata unguwa na dosa mai suna unguwa uku wanda da kaga unguwar kasan unguwar talakawane,yarene sun fito sunyi cuncurundo masu gare gare nayi,masu carafke nayi,masu iwan nayi.

wani gida na dosa wanda hanyar shiga gidanma kwatane,anyi labule da buhu an daure nan nashige gidan hayane mai dauke da d'akuna hudu,kowanne ciki daddayane sai dan tsakar gida wanda rabi simintine rabi k'asane sai bayan gida da kitchen.

wani daki nadosa wanda labulen d'akinma marabarsa da tsumma kad'anne,ina shiga maci karo da wata yar tsumman katifa da marabarta da dandamalin k'asa kadanne,sai leda wanda iya rabin d'akin ya tsaya kuma duk ta bubbule.

wata yar matashiya nahango da bazata wuce kimanin shekara 24,ba a duniya na hango kwance kan katifan tana rik'e da cikinta, kallo d'aya zaka mata kasan yunwane ya duk'unkune ta hakan koda halin dana ganta aciki bai boye kyanta ba.

batada jiki sosai ita ba fara bace kuma ba b'aka bace tana ido da hancinta daidai,sai gashin giranta daya kwanta dana idonta dayake zara zara.

tayi nisa a tunanin da takeyi bata ankara ba saijin muryar mahaifiyarta tayi tana fadin........

"Zaheederh!!ki mik'e muje yau kam nasamo miki aiki dakyar,suka yarda zasu dauke ki sunce su kawo musu yan kwana akeyi dan hka ma nace musu idan aiki yayi yawa kya iya kwana,nagaji muyita zama muna zubawa juna ido d'an ribar k'osan matasa suncinye jari da bashi na hakura kitashi kisa hijab muje anan CBN Quaters na nema miki.

"kinga bbu mgnar kudin adaidaita.saida ta kara mgnar nasamu daman kallon face dinta kyakyawan bahaushiya ce bbu laifi,itama haskenta ba sosai bane bazata gaza shekara 50 a duniya.

turo baki Zaheederh tayi tare da fadin... "ni wlh bazanyi wani aikatau ba kamata ace ina aikatau wlh aa bazan iyaba gara ma ki canza shawara rashin uba ai ba hauka bane.

tana kaiwa nan ta sake gyara kwanciyarta,tare da sake dunkulewa dan maganarma da kyar takeyi.

"To barina danake da ciwon asmah(asthma)barinaje nayi kinga nakwanta kiyi jinyata,zaki tashi ko saina zo kanki.

ganin yadda uwar tayiyo kanta yasa saurin mik'ewa,tazari hijab dinta da farine amma harya koma brown Wanda ko kyakkyawan dank'a kamasa zai iya yagewa tasa suka fice tana k'unk'ini jan k'ofar sukeyi tare dayima matan gida sallama suka fice.

Koda kagansu a hanya bazakace tafiyarsu d'aya ba maman na gaba yayin da Zaheederh ke biye da ita abaya.

Ďan tafiya Sukayi Kafin suka tsallaka titi suka ďauki hanyan gidan.

Koda suka shiga layin sun ďanyi tafiya kafin suka isa k'ofar gidan.

knocking Mamah tayi da ďan k'arfi kusan 5mins aka bude musu, ganin itane yasa gate man din dayake sanye da uniform dinsa na masu gadi, ďan murmushi yayi "yace kin sake dawowa Knan murmushi mamah tayi tare....... "eh harka shaidani knan tsabar sintirin danayi ko?

Bai sake cewa komaiba har Mamah tayi nisan tafiya... Jin alamar ita kadaice ke tafiya yasata juyowa tana neman Zaheederh da ta manta da kanta wajen kallon gidan.

Juyowa mamah tayi ta kamo hanunta suka shige dan kallon gidan.gidane na sama da k'asa fentinsa milk color ne sai gate dinsa bak'i,duk gidan grass carpet ne a shinfid'e sai can gefe pool side mai had'e da basket ball field sai gefe gurun hutu dayasha kujeru masu shegen tsada bayan gidan knan,gaban gidan shuke shuken flowers ne kala kala sai parking space acan gefe sai dayan gefen kuma BQ ne.

suna isa k'ofar da zata sadasu da parlor mamah ta danna wani abu ya bude, Zaheederh dai tazama kaman wata wawiya sai kalle kalle takeyi.

k'ofar na budewa suka shiga tsayawa fadan haduwar parlorn ma bata lokacine,nan suka tarar da wata matashiyar buduwa kwance kan 3seater tasha riga da skirt na wata jar holland atamoa,ya matseta sosai tana kallo a makeken plasman dake manne a bangwan parlorn tana kallo da gugguru a hanunta.

sallamansu ne ya dawo da ita daga kallon dakeyi na wani Nigerian film mai suna "The wedding party.

d'ago dara daran idonta tayi ta ansa sallamansu,yayin da take mik'ewa daga kwanciyar datayi.

"sannunku da zuwa Babah bismillah kuzauna tana nuna musu kujera.

murmushi mama tayi tare da fadi....."nanma yayi tana zama kan carpet din daya mamaye parlorn.

saide banda Zaheederh da batama san inda kanta yakeba,sanda mama tajata kafin ta zauna.

"sannu k'aramar Hajiya da hutawa,mamanki fa dan Allah?

D'ago idonta tayi tare da fad'in "tana sama barina kirata pause tasa ta haye sama,da ido zaheederh tabita da kallo batasan time din datayi wani ajiyan zuciyaba tare da teb'e baki.

tafe take da hijab dinta har k'asa tasa nikaf din jikin hijab din....sanda tayi nisan tafiya kafin ta tsaya ta ciro wanyanta k'irar iphone 12 tayi dialing lst num din,baifi ringing biyu tayiba aka picking tare da fad'in "ki karaso kadan naga hijab dinki zakiganni.

kashe wayan tayi ta k'arasa da sauri tana hangi motarsa kirar 406 tasha tint tashige.....ganin garin yafara duhu yasata sauke nikaf din tana fad'in......"wlh yau ka wahalar dani ta k'are mgnar tana turo baki.

murmushi yayi tare da janyota jikinsa yana shafa bayanta tare da fadin....."sarauniyar mita muje dai kinsan a hanu nake yana fadin hkan yaja motarsa da mugun gudu yayin da ita kuma tamasa wani fari da ido.

IDAN NAGA RUWAN COMMENTS NACIGABA DA POST A WHATSAPP IDAN BAN GANIBA SAIDE ABINI WATPAD.....

08039171989
DON NEMAN KARIN BAYANI .........

MEDIA (DAN DALIN SADA ZUMUNTA) Where stories live. Discover now