MEDIA (DAN DALIN SADA ZUMUNTA)

48 3 0
                                    

*MEDIA(DAN DALIN SADA ZUMUNTA* )

*Na..Nanahkhadii💅🏽* 🛍️

*Marubuciyar👇🏽*

*_Cousins Ne_*

*A Ruwan sama (kaddara tasameni* )

*Auren k'iyayyah*

*Hamdan paid book*

*Agarin son duniya*

*_nd now MEDIA(DAN DALIN SADA ZUMUNTA* )_

*ELEGANT ONLINE WRITERS*📚📝🌤️

🅿️3️⃣2️⃣🔁3️⃣3️⃣

Bismillair~Rahmanin~Raheem.

Zaheedarh da gudu ta shiga gida tana kuka,Mamah nazaune kan sallayah tana jan casbaha jin yadda Zaheedarh ta shigo da gudu ta wurgar da ledan hannunta tare da fad'awa kan gado ne yasa mamah cikin tashin hankali fad'in...."lfy zaki shigo kamar wacce aka koro menene? duk a lokaci d'aya take tambayanta Zaheedarh k'in kulata tayi ta cigaba da rera kukanta Mamah ganin abun bazai k'are bane yasa ta fad'in....."amma da ke nake mgna ko kiyi kamar baki jini ba. sai lokacin tace     "Mamah dan Allah ki fad'a min garin dazan je naga mahaifina koda kuwa ni y'ar shege ce,ina so naje nagansa yasan da zamana ya share min hawayen da bayida ranar daina zuba a idona,jin mgnanta sosai ya dag'a hankalin mamah tunda Zaheedarh ke mgna Mamah ji tayi wani zufa a keto mata,koda Zaheedarh tayi shiru tana kallon mahaifiyarta tare da jiran ansa a gareta sai taga Mamah na share hawayenta tare da fad'in...."Zaheedarh bana so allura ta tona garma meye ya kawo wannan mgnar? magar mahaifinki kuma ki sani har abada bazaki taka inda yake ba,suna zaman su lfy bana so na zama silar tada wani fitina tunda koda na taho da cikin ki bai saniba abu d'aya dai nasani kin raba garda ma tunda kin fito sak shi kaman an tsaga kara,amma zancen neman sa kam kiyi hkri yanuz meye ya kawo wannan zancen ma? kallon Mamah tayi da jajayen idonta ga zuciyarta ta dayi mata k'una jin mgnar Mamah cikin kuka tace...."Mamah wlh dole naje neman mahaifina duk ranar da kika ga baki ganni ba to natafi neman mahaifina nane,tunda abun har yakai Zubaida ina hira da Harees taje tace masa wai bani da uba jin mgnar Zaheedarh sanda mamah t had'iye wani abu daya taso mata a abaki zuwa zuciya,kafin tace..."Zubaidan ce ta miki hka? innalillahi wa'innah ilaihin raji'un,lalle duniya tana tare da abin mamaki da al'ajabi iri iri yanzu abinda ya farune yakai harda cin mutun ci hka,toh Allah yayi mana katangar k'arfe dasu sai mu bar musu gidan zanje nasamu mai gidan ko rabine a kud'in dana bayar ya bani mu nemi wani,aini a jimawan da zaman da mukayi dasu Lami idan akace zasu kwance min zani a kasuwa bazan yarda ba,kiyi hkri taki k'addarar knan zamu bar gidan kawai dan mu zasu tonawa asiri.
Zaheedarh jin mgnar Mamah sosai ya tada mata da hankali na baza ta tab'a ganin uban ta ba wanda ita agunrin ta hkan ba mai yiyuwa bane,hka zata k'are rayuwarta a wulak'an ce dan an haifeta bbu uba?kai da kamar wuya baxata iya ba,ringing din da wayarta tayi ne ya dawo da ita daga tunanin da takeyi,ganin sunan Harees yasata janyo wayan b3r din wayan ma tacire baki d'aya ta juya taciga ba da rera kukanta,hankalin Mamah sosai ya tashi dama tasan rana irin tayau dole saita iso yanzu tau sayin yarta ne sosai aranta hka tayita tunani kala kala,Zaheedarh kam sai kuka takeyi kamar ranta zai fita.

washegari koda Mamah ta tashetl ta sallan asuba da wani mugun ciwon kai ta tashi,banda layi bbu abinda takeyi hka ta daddafa bango ta shiga bayi tayi alola tana daddafa bangon still,ta kama hanyan shigo daki dai dai bakin k'ofa ta fad'i sai tim Mamah take ji da sauri ta mik'e jin kamar fad'uwar abu ta fito da Zaheedarh taci karo a zube a k'ofa a sume....."innalillahi wa'innah ilaihin raji'un shikenan zasu kashe min y'ar tawa k'walli d'aya tillo a duniya wacce nake kallo naji sanyi a ruwata,hankalinta a mugun kad'e ta kikkibo Zaheedarh ta shin fid'eta kan katifa tsabar ta rikice ma rasa me zata yi mata tayi kawai saita fara mata fifita,ganin still bata motsine yasata mik'ewa ta ibo ruwa ta shafa mata a fuskanta tana yi tana mata addua,takai kusan 3mins kafin tayi ajiyan zuciya mama kam banda addua duk wacce tazo bakinta bbu abinda takeyi,idonta da suka mata nauyi tafara k'ok'arin bud'e wa saide ta kasa tajima da idon a kulle kafin da kyar ta bud'e a hankali dan sun mata nauyi Mamah tagani zaune tayi ta gumi tanata mata addua,cikin muryan daya dishe baya fita sosai tace...."Mamah kaina zai fashe yana min ciwo, "sannu Maryam zaki samu lfy insha Allah yanzu bbu wani chemus (chemist) da zamu samu abud'e kiyi hkri zuwa gari yayi haske sai nakai ko?

MEDIA (DAN DALIN SADA ZUMUNTA) Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora