22

578 42 3
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''


2️⃣2️⃣


"Anya zan iya zafe miki kuwa Maryama...?

"Anya zakiga haske a rayuwarki...!?

"Anya bazakiyi kukan dayafi wanda kika saka mu ba...!?

"Ya Allah ka....!

"Dakata Falmata karki jefamu a masifar data fi wacce muke ciki, haba yanzu ma ya yarinyar ta k'are balle kina neman yi mata baki.

Fattuma mahaifiyar Yuraam ta fad'a tana danne nauyin da k'irjinta yayi mata.

"Ke kika sani, kanki ake ji Falmata idan kinga dama ki tsine mata, in sha Allahu babu abinda zata gani sai alkhairi, da nasarar rayuwa aduk inda take, ina fatan alkhairin Allah yakai mata aduk inda take.

Harta juya zata fice ta dawo ta kuma kallan Mama tace " kada ki manta idan uwa tayiwa d'a baki Mala'iku suna amsawa da "Amin tare da ke" haka idan kayiwa d'a addu'a ta gari zasu amsa da "amin tare da ke, shiyasa zakiga duk wanda yayiwa d'a baki ya lalace sayya shiga mummunan jarabawa shima da firgici a rayuwarshi.

"Idan kin so kina iya cigaba da yi mata idan wani abu ya tashi samunta ina fata ya sameku tare, da zata fice gadan-gadan kan Abba ta nufa yayi saurin matsawa danshi tsoro ma take bashi yanzu, duk da ya matsa saida ta bangaje shi ta wuce, sosai abun ya bawa kowa mamaki dan an san hakan ba hanlinta bane, kwata-kwata Umma bata san fitina da rikici, an sha yi mata abu tayi kamar bata san anyi ba, dan haka akeyi mata kallan me san zaman lafiya, haka bata da abokin fad'a a family..

*BODA MALI DA NIGER..*

Tafiya sukayi me shegen nisa  sai cikin dare suka shiga Mali, basu tsaya a Mali ba suka cigaba da nausa tafiya sai da suka kwana suka yini suna tafiya kana suka shigo MAURITANIA, daga gefen garin suka tsaya suka sha mai a motar suka cika tankin motar tap kana suka fito da manyan jarkoki suka cika su da mai,
da mai gidan man yayi musu maganar kud'i kanshi suka fasa da bindiga, nan fa gidan man ya kacame da iface-ifacen mutane,
kowa yayi ta kansa, suka shiga cikin super market d'in gidan man suka jidi kaya san ransu kana suka cigaba da tafiya, sai da sukayi tafiyar kwana biyar da yini d'aya kana suka isa camber su a *WESTERN SAHARA...*

Parking yayi a tsakiyar wasu bukkoki wad'anda bazasu wuce guda goma sha biyar zuwa ishirin ba, kana suka fito, mota suka gani fake a wajen, dan haka sukayi shirin harbi had'i yin kwautan b'autana, dan su a saninsu babu kowa a wajen, wajen b'oyayyan waje ne, dan ko gwamnatinsu bata san da wajen ba,
nan ne mab'oyarsu, babu wani mahaluk'i  daya san da zaman wajen,
inda suke jin motsi can suka nufa, cikin sand'a, sun d'ana zasu saki harbi d'an uwansu ya fito, da mamaki suke kallan juna, cikin harshen fransanci yace " lafiya..?

Babbansu yace " dama baka cikinmu?

"Eh! kai fa kace na taho..
"Ya akayi ka rigamu k'arasowa?

"Nima zuwa na kenan ban dad'e da k'arasowa ba, yarinyar nan nakai ciki.

Babbansu bai fahimci zancen yaran dayace yarinyar yakai ciki ba, sai yace " ina ka samu mota?

"Kan wani na fasa na d'aukota..

Juyawa yayi wajen sauran yaranshi yace " ku sauke kayan, yana fad'a ya wuce ciki, ihuuuu ya saki yana fitowa waje a rikice kamar yaga mutuwarshi duk yaran sukayo kanshi suna tambayar lafiya,
ihunn shine ya farkar da Maryama daga dogon suman datayi, d'aya daga cikin yaran yace " êtes-vous ok? (Kana lafiya?)

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now