'''DUK NISAN DARE...!'''
*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*
*HAUWA A USMAN*
~JIDDARH~'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''
4️⃣1️⃣
Maiduguri...
Su Abba na zaune a babban falon gidan gaba d'ayansu Umma ce kad'ai babu suna kallan Al Jazeera Channel, sunga komai, duk abinda ya gudana a kotun sun gani,
Abba ya sauke ajiyar zuciyar had'i da cewa " da tuni muma muna can amma suka hanamu Visa, kome yasa oho?"Abba bamu kad'ai suka hana bafa, gaba d'aya 'yan Nigeria suka hana Visa saboda abinda ke faruwa, suna gudan mutum ya shiga ya k'ara haifar da wata matsalar,
amma kamar naji abun bazai dad'e ba zasu bud'e komai ya dawo dai-dai, Yuraam ya fad'a yana kallan Abba."Sudai suka sani, ai in banda wannan Barrister yayi hakan da har yanzu shari'ar bata k'are ba, amma in sha Allah ana bud'e Visa can mukayi,
Bakura yayi maganar cikin nutsuwa.Rawaana yace " ai wannan Barrister Allah ya biyashi wallahi yayi namijin k'ok'arin sosai, ya nunawa duniya shi me kishin nashi ne.
Mama ta furzar da iska daga bakinta tare cewa " wai ni Maryama kota yafe mu ne?
Gaba d'aya wajen kowa ya kalleta cikin rashin fahimtar inda zancenta ya dosa.
"Eh! Mana in banda ta yafe mu ai yaci ace ta nememu ko'a waya ne tunda yanzu ta samu freedom ba'a d'aure take ba, kosau d'aya ya kamata ace ta kiramu nasan dai bazatace bata rik'e number ko mutum d'aya a cikinmu ba.
Kowa shiru yayi yana juya maganganun Mama cikin kanshi, dan ko ya kamata ace ta nemi gida, " Allah ya kyauta, Abba yace had'i da mik'ewa ya shige ciki.
London...
Sosai Maryama ke rayuwar kwanciyar hankali da jin dad'i a gidan Barrister Shatima, babu wanda ke nuna mata komai,
abinci sai wanda ta zab'a ake girkawa, haka daga b'angarenta tana iya bakin k'ok'arin wajen taimakawa Khadija tana kama mata aiki sosai musamman ta fannin Hanif da Hanifa."Wash.. nagaji sosai, Barrister Shatima yace yana zama kusa da Maryama, murmushin yak'e tayi had'i da satar kallan Khadija da itama tana falon amma bai zauna kusa da ita ba,
itama Khadija Maryama take kallo suka had'a ido, Maryama tayi saurin d'auke idonta tare da mik'ewa tana fad'in " bari na shiga ciki,
"daga gani na shine zaki tashi Maryama?"Kodai baki san na rink'a fitowa idan kina falo, yayi mganar yana jefa mata wani irin kallo me narkar da mutum, "idan baki so bazan k'ara fitowa ba muddin hakan zai sanyaki cikin farin ciki, yayi maganar so calm, ba Maryama da akayiwa maganar ba dai- dai Khadija saida taji wani abu,
murmushin yak'e Maryama tayi tare da cewa " ba haka bane sallah zanyi.Shigowa d'aki tayi tana juya abubuwan Barrister Shatima cikin ranta, ta dad'e kwance saman bed tana kallan Pop hankalinta gaba d'aya yayi gida,
mik'ewa tayi da niyyar fita tayiwa Barrister Shatima maganar tafiyarta Nigeria dan bata ga amfanin zaman da take yi ba,
tana gaf da isa falo ta fara jiyo muryar Khadija cikin kuka."Haba Ahamadi! idan kasan mutunci da k'imata ya kamata ka rink'a sakaya wasu abubuwan, amma a gabana, akan idona Ahamadi ka rink'a nunawa wata mace soyayyarka a fili?
"Soyayyar da baka tab'a nuna min irinta ba duk da ina matsayin matarka, wannan wanne irin cin fuska ne Ahamadi?
"Ko baka fad'a ba, ko baka nuna ba, ko aikinka bai nuna ba nasan kana san Maryama, nasan waye kai Ahamadi, nasan ita kad'aice a zuciyarka, nasan waye mijina.
YOU ARE READING
DUK NISAN DARE....
AdventureUnlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something t...