16

462 29 0
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''


1️⃣6️⃣


Gaba d'ayansu k'amewa sukayi a tsaye cike da matsanancin mamakinta, sai lokacin ta ankare da abinda yake faruwa,
kamewa tayi tare da sunkuyar da kanta k'asa, Yuraam yace " Abba am win!

"Aban kyautata!

Cikin kamewa da nutsuwa yayi murmushi yace " gaskiya kam ka cancanci kyauta me tsoka tunda ka juyar da impossible ya koma possible..

"So you win an na baka sabuwar motata da nayi oder jiya tazo, kuma duk k'asar nan babu me irinta, tsalle ya buga yana fad'in " nagode Abba, Thank you so so much..!

Mama dake cike fal da mamaki tace " shiyasa idan kaga mutum yana aikata abu koba me kyau bane kar ka sake ka aibata shi saboda kaima baka fi k'arfin Allah ya jarrabeka ba,
shiyasa akace kada kayiwa k'addarar wani dariya domin kuwa ba abin mamaki bane Allah ya karkato ta ta dawo izuwa gareka....

Abba ya kalleta yace " mu kiyaye tunaninmu domin sune zasu zamo kalmominmu,
mu kiyaye kalmominmu domin sune zasu zamo aiyikanmu, mu kiyaye aiyikanmu domin sune zasu zamo d'abi'unmu,
mu kiyaye d'abi'unmu domin sune zasu zamo halayenmu, mu kiyaye halayenmu domin sune zasu zamo makomarmu.

Kan Maryama k'asa batace komai ba, Umma ta mik'a musu kular abincin tana sauke ajiyar zuciya dan ita she's totally speechless akan abun..

Nan fa 'yan gidan aka shiga tsokanar Maryama kowa yana fad'ar albarkacin bakinshi, kuka ta saka tana nufar wajen Abba tace " Abba ka gansu ko?

"Ni ban gansu ba!

Ya fad'a yana dariya!

"Kai Abba har da kai!?

"Ai dole su tsokane ki saboda yadda kika cikawa mutane kunne akan ball, kika fito k'iri-k'iri da k'iyayyarki ga ball kika nuna,
kinga wannan ya isheki *IZNA* gaba idan kinga mutum yana aikata wani abu koda ba me kyau bane, ki fad'i alkhairi ko kiyi shiru..

A shagwab'e tace " to Abba, amma kace subar tsokanata..

Juyawa yayi wajensu yana murmushi yace " kai ku kyalemun Kakata!

Haka rayuwa taci gaba da gudana da Maryama sosai soyayyarta ga Marshall ta bayyana kowa ya gane shine d'an kwallan da take mugun so.

Maryama tana iya hak'ura da ci da sha idan Marshall zai buga wasa dan karya wuceta kai tana iya hak'ura da komai, yanzu har ita ake zama a mini cinema su ayi kallan ball da ita...

Yauma kamar kullum gaba d'ayansu sun had'u a Estate Cinema ana kallan Marshall Maryama ce a gaba,
tunda aka fara buga wasan yake sukuku kamar mara lafiya, ya kasa tab'uka abun arziki, har aka kusa tashi baici wasan ba.

Ran Maryama inyayi dubu ya b'aci hankalinta yakai k'ololuwar wajen b'aci ana gaf da tashi wani ya jefa kwallan a raga akaci su Marshall,
yadda kasan an bugawa Maryama guduma haka taji, take gaba d'aya annurin fuskarta ya d'auke, jitake kamar ta shak'e kanta ta mutu..

Sai yau ta fahimci abinda 'yan kwallo sukeji idan aka ci su wasa..

Sai yau ta fahimci dalilin dayasa Yuraam yake rufe kanshi cikin d'aki idan aka cisu wasa..

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now