7

583 39 3
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''


7️⃣


Tun daga ranar Maryama ta shiga wasan b'uya da Yuraam, duk inda yake to bata nan, idan kuwa tana waje yazo saita san yadda tayi ta zame,
duk yadda yake yin k'ok'arin ritsata tak'i bashi dama.

Kowa a gidan ya kula da yadda Maryama ta mayar da Yuraam surukinta, matuk'ar yana waje kwata-kwata bata sakewa, ga yayyenta sun saka ta gaba da tsokana wai tana so tana kaiwa kasuwa.

Tana zaune kusa da Umma tana daddanna waya ya shigo bakinshi d'auke da sallama, ganinta yasashi fad'a fara'arshi, ya zauna daga d'an nesa da ita,
duk motsin da take idonshi na kanta, a jikinta taji idonshi na yawo a kanta, " baki ga Yayanki ya shigo bane?

"Kai Umma! na ganshi mana, " to kuma shine baki gaidashi ba?

Saida ta turo d'an tsukakken bakinta tace " ina yini?

Ta fad'a batare data kalleshi ba, murmushi yayi saboda turo bakin nayi mata kyau, kai duk abinda Maryama tayi kyau yake yi mata,
" lafiya lau, ya kike?

"Alhamdulillah! ta fad'a har lokacin tana jin yadda idonshi ke yawo a kanta, yabi ya zuba mata ido, ya hanata sakat da kallo,
tana d'ago kai idonta ya sark'e cikin nashi, dukkanninsu suka kasa d'auke idonsu daga kan junansu, ya d'an fad'a kad'an ko idonta ne ke nuna mata hakan oho,
Umma na sane da duk motsinsu, tayi murmushi had'i dayin gyaran murya, da sauri Maryama ta d'auke idonta daga kanshi cike da kunyar Umma,
saida ya sauke ajiyar zuciya kana ya kalli Umma yana fad'in " Umma na rasa meke damuna gaba d'aya bana jin dad'in komai,
" hmmm tace tana murmushi kana ta d'ora da " saboda ka kasa yawo kan Maryama?

"Karka bani kunya mana Yuraam, a wahalce yace " wallahi Umma 'yar nan taki tana bani wahala, gaba d'aya na rasa nutsuwata,
a hankali ta d'ogo idonta ta saci kallanshi aiko karaf suka had'a ido, tayi saurin kawar da idonta,
Umma ta mik'e tana fad'in " kadai k'ok'arta karkayi sake, ganin Umma na k'ok'arin barin wajen yasata saurin mik'ewa zata bar wajen,
a kasalance ya kira sunanta " Maryama!, cak ta tsaya bareta data juyo kotayi magana ba, " please Maryama ki so ni,
wallahi ina sanki da gaske, sosai jikinta yayi sanyi, ta juyo ta fuskance shi tare da kallanshi na kamar second 2 zuwa 3 kana ta duk'ar da kanta tace " kayi hak'uri Yaya...!

Tun kafin ta k'arasa ya soma girgiza kanshi yana fad'in " a'a please karki ce min na hak'ura dake dan Allah, bazan iyaba Maryama please,
yadda ya marairaice mata ya bata dariya sosai, " au dariya ma na baki?

"Eh Allah, ji fa yadda ka koma abin tausayi.

"Ba dole na koma abin tausayi ba Maryama, so fa, kina wasa da so.

"To naji sarkin masoya duk duniya, d'an shiru sukayi gaba d'ayansu kana tace " Yaya.....! " shhhhhh yace yana d'ora hannunshi saman lips d'inta, had'i da cewa " please ki barni nayi ta kallanki.

"Duk kallan da kayi min tun d'azu bai isheka ba...?

"Wai Allah, ya za'ayi kallanki ya isheni?

A shagwab'e tace " Yaya bacci yazo, "tom muje na raka ki matar Yaya.

"Allah Yaya ka bari.

"Na bari, yace yana had'a hannuwanshi, har bedroom d'inta ya rakata yaja mata burgo ya rufeta, ya kashe mata fitilar d'akin kana ya fita,
yana fita ta mik'e tana fad'in " daga yau ban sake bari ka ganni duk wayonka.

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now