32

416 33 1
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''


3️⃣2️⃣

Murmushi ya saki had'i da cije lips d'inshi na k'asa, ya zura hannunshi d'aya yana shafa k'irshi while yana sakar mata shu'umin kallo,
gaf da ita ya matsa ya sanya hannunshi ya tokareta ya sanyata a tsakiyar hannayenshi, idanuwanta ta rufe ta bud'e a lokaci d'aya, ta sauke idanuwanta saman k'irjinshi me yalwataccen gashi kwance luf!

K'ara runtse idanuwanta tayi, lokaci d'aya jikinta ya d'auki wata irin muguwar tsuma, har hak'oranta na had'uwa kaf kaf kaf! kwallabar giyar ya d'aga ya soma tsiyaya mata a kanta,
jin saukar ruwa a jikinta yasata saurin bud'e idanuwanta aiko karaf idanuwanta suka shiga cikin nashi, murmushi ya sake sakar mata yana tuttule mata kwallar giyar aka,
ta gangaro ta b'ata mata jikinta, saurin rufe bakinta tayi dan kar giyar ta shiga cikin bakinta, hancinshi yakai wuyanta ya sunsuna, ya lumshe ido had'i da fitar da wahalallan numfashi.

Ya kai hancinshi wuyanta ya shak'a da k'arfi, "ahhhh! yace a fili yana k'ok'arin shigar da jikinshi cikin nata, ido Maryama ta soma k'ifk'iftawa irin na marasa gaskiya nan, yadda kasan wacce ta had'a gagarumin mumafircin k'asa da k'asa ake turketa.

Duk inda ya tab'a jikinta ji takeyi tamkar ya watsa mata wuta, lokaci d'aya taji jikinta ya soma yi mata yaji,
saurin zame jinta tayi jin numfashinta na gaf da d'aukewa saboda tsoro da firgici, ta saki murmushin yak'e tana cewa " can I eat first?

Ba yunwar take ji ba, ta fad'i hakanne danta tsira daga hannunshi.

"Yes! Sure!.

Yace yana matsawa baya had'i da nuna mata inda abincin yake da hannunshi, kamar wacce ake hankad'awa ta nufi wajen daya nuna mata ta zauna,
bubbud'e abincin tayi taga kusan kala 5, ta zubawa abincin ido deep down tana tunanin da tsakakken nama akayishi ko kuwa?

Kamar yasan abinda take tunanin yace " don't worry you can eat fish or chicken, batayi mishi magana ba ta soma cin abincin da aka girka da kifi dantafi samun nutsuwa dashi akan na naman, a nutse take tauna abincin kamar bata so,
yayi mata kallo d'aya kana ya shige, a fili ta fitar da numfashi had'i da dafe k'irjinta tana fad'in "Alhamdulillah ya Rabbi daka kub'utar dani...

Dakyar ta iya cin loma uku saboda firgicin da take ciki, bawai yunwar ce bata ji ba, tsoro ne ya hanata sakewa taci sosai, dan sai da ta fara cin abincin tasan tana jin yunwa,
tana nan zaune ya fito d'aure da guntun towel a k'ugunshi, ya zauna gaf da ita, rabin cinyarshi ma a saman tata take..

Murmushin yak'e tayi had'i da d'an matsawa kad'an tana kallanshi, hannunta yayi caraf ya rik'e gam idonshi kanta,
ji tayi tamkar ya nana mata wuta, saurin mik'ewa tayi tana fad'a " i want to pray, kallan tsaf yayi mata kana ya umarci d'aya daga cikin yaranshi takaita toilet..

Jingina tayi da k'ofar band'akin tana sauke ajiyar zuciya, kana iya ganin yadda k'irjinta yake sama da k'asa saboda tashin hankali..

Ta dad'e a haka kafin tayi alwala ta fito, sallar da bata san adadin suddar da tayi ba tayi, ta idar ta dad'e tana karatun Al Qur'ani daka,
ta maimaita addu'ar neman tsari da zina yafi sau 100, kana ta d'aga hannu ta soma kwararo addu'a..

"Ya Ubangiji me girma, kaine mad'aukakin girma, Ya Allah, kaine dai-dai, kaika san dai-dai, kai kakeyin dai-dai, ya Allah zina babban laifi ce kayi hani dayinta,
ya Ubangiji ka d'orani akan fajirin nan kada ka bashi ikon keta min haddi, Ya Ubangiji kada ka bawa wannan kafirin ikon yin zina dani,
Allah ka tsare ni da aikata zina, Ya Ubangiji ka kula damu karka tozarta mu, karka bawa wani ikon tozarta mu,
Ya Allah karka jarrabemu da abinda zaifi k'arfin rayuwarmu, ya Allah kayi mana katangar k'arfe da masu binmu da mugun nufi.

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now