'''DUK NISAN DARE...!'''
*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*
*HAUWA A USMAN*
~JIDDARH~'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''
2️⃣3️⃣
"Zan fad'a miki dokokinmu idan kika sake kika karya d'aya daga cikinsu sakamakonki MUTUWA...
Ido ta zaro a masifar tsorace cikin matsanancin tashin hankali da firgici muyarta na rawa tace " ban gane d'aya daga cikinku ba...!?
"Me yake nufi dana zama 'yar k'ungiyarku....?
Cikin hausar Issah ta bata fita sosai ta 'yan koyo yace " eh ta yarinya yana fadin kin zama 'yar fashi kema...
"Fashi....!?
"Wai fashi da makami irin naku da kukeyi yake nufi...!?
"Ehta yarinya..
"Irin wanda kuke kashe mutane..!?
Ta kuma tambayar Issa cikin kid'ima.
Issah yace " ehta! yarinya shifa..
Djeneba ya kalli Maryama kana ya mayar da kallanshi ga Issah cikin France yace " me take cewa ne..!?
Cikin girmamawa Issah yace " tambayata take yi.
Muryar Maryama na sark'ewa saboda tsantsar tashin hankali tace " wallahi tallahi kozan mutu bazanyi fashi da makami ba, koda zai ban raina a hannuna wallahi bazanyi fashi ba..
Cike da tsoro Issah yace " a'a yarinya karkiyi hakanan na, inba hakannan ba mutuwa kinayi yanzu nan...
"In mutun mana, inna mutun sai me..?
"Dadai na aikata fashi gwara na mutu... bata k'arasa ba Djeneba ya buga mata gindin bindiga akanta, ta sulale k'asa sumammiya..
Abinda Maryama bata sani ba shine Djeneba yana jin hausa sarai, dan har yafi Issah jin Hausa da iya mayarwa sosai, yana yin b'adda bami ne kawai da kuma iya taku, danko yaranshi basu san yana jin Hausa ba sai yanzun....
A fusace ya kalli fuskarta dake ta faman kyallin da rana ta haske ya tofa mata yawu yana fad'in " wulak'antacciya...
Ya sanya k'afa ya tsallaketa ya shige bukka, sauran yaran kowa ya shiga sabgar gabanshi, bata farka ba saida aka d'auki awa d'aya kana zafin ranar daya haske mata fuska da zafin saharar da take kai suka had'u suka farkar da ita, a wahalce ta farka ta bud'e idanuwanta da sukayi mata mugun nauyi,
dan har yaji-yaji suke mata, ga bak'ar yunwar dake azalzalarta, a hankali taja jikinta ta tashi zaune kanta dake barazanar tarwatsewa ta dafe tana lumshe idonta..Ji take kamar a mafarki, kamar ba ita ba, wai itace Maryam Bukar Bugaje's kuwa..?
Anya ita ce?
Ta tambayi kanta, k'afafuwanta datakejin kamar ba'a jikinta suke ba taja ta mik'e tsaye tana jin yadda jikinta yayi mata mugun nauyi.
Cikin mutuwar jiki ta nufi randa data gani aje ta bud'e ta d'ebi ruwa da nufin kaiwa bakinta taji an kwab'ar da ruwan,
jajayen idanuwanta ta d'ago ta saukesu akan Djeneba."Bazaki sha ko ki ci daga gare mu ba, tunda kina kyamar sa'ar muke yi, saiki rayu cikin sana'ar da kike so kike ganin zata fishsheki.
"Dan Allah ruwa...
YOU ARE READING
DUK NISAN DARE....
AdventureUnlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something t...