17

410 26 0
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''


1️⃣7️⃣


Murmushi yayi yana shafa kanshi yace " Maryama kowa yasan kina san Marshall duk mun san ke fan d'inshi ce ta mutuwa.

Kanta ta girgiza tana danne kukanta tace " ba irin sanda kuke zato bane Yaya.

"Ba irin sanda kuke yiwa Celebrities bane ni nawa san yasha bambam da wannan san.!

" *SO NA SOYAYYA NA AURE* nake yi mishi.

Fashewa tayi da matsanancin kuka tana tallafe kanta tace " na rasa yadda zanyi, nayi addu'a har na gaji ba wani sassauci ko sauk'i.

"Na rasa wanda zan fad'awa, na rasa dawa zanyi maganar kona samu sassauci Yaya.

Kallan mahauciya yayi mata yana fad'in " amma dai wasa kike yi ko?

"Please tell me you're joke, kice da wasa kike!

"Da gaske nake Yaya ina sanshi ina yi mishi mahaukacin SO, ina sanshi da duka zuciya ta.

Mik'ewa yayi yana dariya tare da tafa hannu ya nunata yace " na gane April kike yi min ko?

Tunawa da yayi da ba'a April month ake ba yasashi cewa " like seriously?

"Wallahi bada wasa nake yi maka ba Yaya da gaske nake, ina cikin mummunar jarabawa, da bak'ar k'addara Yaya.

"Kina da hankali kuwa?

"Kanki d'aya kuwa?

Ya fad'a yana nuna kanshi.

"Kin san me kike cewa?

"Gaskiya da alama kin samu tab'in hankali Maryama.!

"Dan baki san abinda kike fad'a ba, kinci kai.!

Mik'ewa tayi tana kallanshi ido cikin ido while hawaye na gangarowa saman fuskarta tace " ina cikin hankali na Yaya.

"Makauniyar soyayya ce Allah ya jarrabe ni da ita, wacce ta makantar dani, ta kurumtar dani, bana ji bana gani Yay.....

Cikin fad'a da masifa da hargowa yace " enough!

"Enough dalla malama!.

"Kinyi hauka ne?

"Kin san akan wa kike magana kuwa?

"Mutum ne da duniya kaf babu kamarshi.

"Mutum ne da duniya tasanshi kuma take ji dashi.

"Dan kina cikin wannan d'an lungun a duniya!

"Kina cikin wannan akurkin gidan da ko masu aikinshi sun wuce shi, wacece ke a duniya?

"Wa kika sani?

"Waya sanki?

"Ina kikaje!?

"Duniya kaf magana takeyi akanshi, babu inda bashi da alfarma a duniya, babu inda sunanshi bai kai ba, bature ne fa!.

"D'an k'asar America, farin fata, d'uwawunshi ma yafi fuskarki fari Maryama.!

"Me zayyi dake K'AZAMA!, wawiya wacce bata waye ba, ke wallahi ko inda inuwar wanda ya sani ta taka ke baki isa ki taka ba balle shi..!

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now