Tittle
'Yar Son Banza
Written by
Fatima Saje"Kwance nake a kan shimfiɗaɗɗiyar katifata, mai matsakaicin tsawo kamar dai ni mai maganar.
Miƙa na yi tare da sake sanyayyar murmushi sannan na buɗe idanuna ina mai sake lumshesu saboda hasken rana.
Ban ankara ba, ina duba agogo naga ƙarfe uku na yamma (03:00pm). A hanzarce na miƙe tsaye cikin rashin sa'a tattausar ƙafata ta ture wata farantin roba dake ɗauke da abincina. "Mtsw!" na ja tsaki na ƙara gaba.
Sabulun wankan ƙanwata na ɗauko ba tare da ta sani ba. Nan na yi wuf na shige banɗanki a guje yayin da na ga ƙanina Fahad ya aje ruwan wankansa ya fatito ɗaukan soso.
Haka nayi kunnen uwar shegu da masifarsa na yi wankana ina mai jinjinawa ƙamshin sabulun, har ma nake ji a raina wannan sabunlun da ni ya dace ba Ummi ba.
Sa'a guda na kwashe ina wanke lungu da saƙo na jikina, domin yau babbar hidima ce a gabana.
Kau da kaina na yi, nayi kamar bana ganin su Umma da sauran masu jin haushina a gidan kana na wuce kai tsaye izuwa ɗakinmu.
"Alhamdulilah" na faɗa kana na saki wata kakkaurar murmushi. "Ankon bikin ne wannan fa" na faɗa ina mai duba kayan dan ganin yaya yanayin ɗinkin yake.
Take na zunduma ƙatuwar hijabi na sungumi kayan na dunƙulesu a cikina zan fice waje. "Ina kuma za kije da ƙatuwar hijabi kamar matar Liman?"
Da ji na san Mama ce ke magana.
"Nan fa ƙofar gida zan leƙa duba yaro."
Nan na yi hanzarin ficewa ba tare da na ji wata maganar ba.
Ina fita na tare mai adaidaita nace masa kai ni Unguwar Kaji, nan muka nausa sai gidansu Afra. Muna tsayawa ƙofar gidan, na saki salatin manzo, mai adaidaita yace "lafiya kuwa baiwar Allah?"
Nace ina fa lafiya, na yadda naira ɗarin da zan biyaka. Yau na shiga uku yanzu yaya zan yi?
Take na fara ƙif-ƙifta idanu alamun dai kuka zan yi. "Haba 'yammata kada ki damu, je ki abunki na yafe miki."
Matsakaiciyar murmushi na jefa masa na daidai kuɗinsa na ƙara gaba.
Tana ganina ta haɗa rai dan ta san abunda ya kawo ni.
Shiga ɗakin na yi, na baje kolin mayuka da turare harma da kayan kwalliya kana na zaɓi takalmi, gyele harma da 'yar karamar jakarta ta ratayawa.
A haka muka wuce gurin dina, ƙarfe biyar daidai sai gamu a bakin ƙofar shiga.
Afra ta sa hanu ta ɗauko ƙaramar kati ta nunawa masu tsaro sannan ta shige. Nan na tsaye sororo ina zare idanu domin ko katin gayyatar bani da ita.
Ganin kada ajina ya zube nayi lu na saki jiki zan faɗi, take na ji hannu ya kamani. ina buɗe idanu naga fuskar Ummi; zumɓur na miƙe tsaye.
Murmushi ta yi ta shiga ciki ta bar ni a waje ina kallo ana cin kaji da lemon kwalba.
Na so na ci banza kamar yadda bana bari ta wuce ni. "Amra 'yar son banza" laƙani na kenan kuma ina alfahari da hakan.

YOU ARE READING
AMRA
General FictionNa so ace na ci na banza kamar yadda bana bari ta wuce ni. Amra 'yar son banza, laƙanina kenan kuma ina alfahari da hakan.