AMRA
Written by
Fatima SajeMu leƙa littafi.
AMRA P3
('Yar son banza)
Written by Fatima Saje.Na ƙahu, zuciyata tana daf da fizgewa daga ƙarƙashin kulawata; ababen ci da sha dake gurin sun yi yawar da ban san ta ina zan fara ba. Kuma babban abun takaicin shine idanu da wannan kekkewan matashin ya zuba mini sun hanani rawar gaban hantsi.
"Bismillahi mana 'yammata ki ci wani abu ko kisha lemo" ya faɗa yana mai sake murmushi.
"Ta yaya zan iya kai lomar abinci bakina alhali ka kewayeni da idanu tamkar wacce kake zargi" na faɗa a zuciyata ina mai biya masa bashin murmushin dana ɗauka.
"Ko zan iya sanin sunan ki?"
'Amra' ko kace 'Queen'
Ya sunkuyar da kansa ƙasa ya yi dariya sannan yace "Queen shi yafi dacewa da kekkyawa kamarki."
Tamkar madara haka naji zuciyata tayi fari ƙal jin ya kirani da sunanda nafi so a rayuwata 'kekkyawa'. A daidai lokacin ne cikina ya fara wani irin ƙugi yana sakin amon yunwa kai kace sautin dj ne dake gurin.
A hankali na jawo farantin dake ɗauke da chips na fara kaiwa bakina duk da a cikin qalbina aminaina kawai nake hange. (Kaji).
"Da wani suna zan yi saving?"
Cikin salo na mamaki ya kalleni yace "ban gane ba"
Ka tambayeni sunana, kuma na faɗa maka. Amma kai ka yi shuru, tawa salon tambayar sunan kenan.
Ya yi dariya matuƙa sannan daga bisani ya amsa min da cewa "Khalid".
*****
Tabbas bikin manya shi ne biki, an kece raini babu ƙarya, domin na tabbata da ace kalmar 'babu' zata halacci wannan taron to tabbas sai ta sake suna.Khadid shi ne babban abokin ango a wannan taron, sai da dj ya kira shi sannan na fahimci hakan; a zuciyata nace lallai na yi babban kamu.
Misalin ƙarfe (08:30) na dare aka kammala 1 aka sallami baki dan komawa gidajensu cikin aminci (a lokacin Ummi ta kai sa'a biyu da komawa gida domin bata yin dare a waje) Bayan mun fito daga ɗakin taron Khadid ya yi mun tayin shiga motarsa dan ya mayardani gida, ban yi masa musu ba domin ko kuɗin motar komawa bani da shi.
Har bakin ƙofar gidanmu Khalid ya kawoni kana ya ɗauko jakar auren cike maƙil da kayan daɗi ya miƙo mini. Ba zan iya mayarda hannun kyata baya ba dan haka na sa hanu na ƙunshe jakata a jikina. Harna juya zan shiga gida sai Khalid yace mun "nan gaba idan kina buƙatar ki ci kaji ba sai kin saci kayan anko kinje gurin taro ba; cikin jakar hannunki akwai katina da number ɗina a jiki za ki iya kirana a kowani lokaci ni kuma na miki allƙawarin zan kawo miki a duk inda kike.!"
Next in sha Allah.
Thanks for reading.
YOU ARE READING
AMRA
General FictionNa so ace na ci na banza kamar yadda bana bari ta wuce ni. Amra 'yar son banza, laƙanina kenan kuma ina alfahari da hakan.