AMRA P2

2 0 0
                                    

Mu leƙa littafi.

'Yar Son Banza.
Written by
Fatima Saje (Umm Adam)

Ƙirƙirarren labarine idan wani sashi na labarin ya taɓo wani ɓangare na rayuwarki/ka to sawun ɓarawo ya taka.

Ban yarda a juyamun labarina ta kowaninfanni ba ba tareda izinina ba.

*****
....Har na juya zan kwashi kunyata na ƙara gaba musamman da nayi duba da yadda masu tsaron wajen taron ke mun kallo mai cike da fassara mabambanta. Take na ji zuciyata, ta daka mini wani irin tsawa mai cike da razani tana yi min kashedin kada na yi kuskuren barin wannan wajen domin ba za ta ɗauki asara ba.

"Shin yaya kike so in yi?" na jefa mata tambayar ina mai zare idanuna tamkar gani ga ta a a gabana muke musayar yawu.

"Wannan kuma ruwanki, ni dai na faɗa miki sharaɗina domin kina barin wajen nan duk aji da kimarki zubewa za su yi."

Sai a lokacin na fahimceta, amma duk da haka ban san ta ina zan samu damar shiga ba.

"Ita kuma wancan me take yi ne a tsaye, ko dai gayyar soɗi ce?"

Wata murya naji kusa da ni wanda na tabbada samari biyun dake jikin baƙar mota ce dake hira da 'yammatansu. Take jikina ya yi sanyi na ga dai banda sauran dama da ya wuce na koma gida.

Na ɗaga ƙafata zan taka sai kwatsam naji ance dani, "Shin ko za mu iya shiga tare?"

Da hanzari na juyo dan ganin wane ne kuma shin da ni yake maganar ko kuwa...

"Idan ba damuwa zan so mu shiga ciki tare da ke?"

kyawawan laɓɓana na sake tare da zaro madaran idanuwana masu sheƙi da matsakaitan girma ina mai ƙare masa kallo cike da mamakin irin kyawun halittar da Allah ya yi masa. da ban kasance a wannan wurinba, to da tabbas sai in ce ya fi dukkanin jama'ar dake wurin taron kyau da fasali.

"Alhamdulilah"
Na faɗa fuskata cike da murmushi zuciyata kuwa ta yi maƙil da farin ciki marar misaltuwa sai dai, idan na bada kai a karon farko hakan zai jawo mini zubewar girma a idanunsa.

"Ka yi haƙuri, akwai wanda nake jira za mu shiga tare"

Ina maganar zuciyata cike da fargaban kada fa ya yi tafiyarsa ya barki.

"To ba damuwa, sai kin shigo" ya juya zai shige cike.

"Na shiga uku! Yanzu tafiya ya yi? Ko dai na tsayar da shi ne? Ta yaya zan iya tsayar da shi!?"

'Cak' na ga ya tsaya yana mai duba izuwa ga wayarda ke hannunsa kana ya juyo a karo na biyu yace "me zai hana mu shiga tare idan wanda kike jira ya iso sai ki fito ki same shi?"

Ban tsaya ko jan numfashi ba nace masa ba damuwa, mu je. Hannu na sa na dafa kan ƙirjina tare da sauke dunƙulalliyar numfashin da ta tsaya a maƙoshina.

Takuna ɗaya bayan ɗaya cike da ƙasaita tamkar 'yar sarki. Ba wannan bama, muna dosar ƙofar shiga ɗakin taron masu tsaron wajen suka sara masa cike da girmamawa. Nan na ji a raina tabbas shi ɗin na musamman ne.

Ummi tana hangoni ta ɓata rai a lokaci guda kuma tana tsaka da mamakin ya ya aka yi na shigo ciki, gani tayi mun wuce kai tsaye wajen zaman manyan baƙi. Ƙarara nake gani tarin tambayoyi a fuskarta sai dai babu damar ta yi mini su saboda na wuce tsararta a wannan wajen. duk da ni kaina ina dakon tambaya kwara ɗaya game da shi, "shin wane ne shi?"

Next In sha Allah
Comment ɗinku shi zai bani damar ci-gaba da kawo muku labarin.

Na gode.

AMRAWhere stories live. Discover now