AMRA 09
('Yar Son Banza)Ban taɓa samun kulawa ta musamman daga wurin Huzaifa ba kamar wannan lokacin, ya kan kirani a waya ya turo mini da saƙonni har ma da aiken manyan jakar leda cike da kayan 'ya'yan itatuwa masu ƙarawa garkuwar jiki ƙarfi. Mama ta tausaya mini matuƙa kana ta jajanta lamarina ganin abun ya kasance ba yadda ta yi zato ba. Sai a waɗan nan kwanakin Mama ta fahimci da gaske ina ƙaunar Huzaifa kuma tabbas zuciyata ta yi nisa a soyayyarsa sai dai kash, mai aukuwa ta auku kamar dai yadda hausawa ke cewa 'ƙaddara ta rigayi fata'.
Ganin irin kulawarda nake samu daga wajen mutanenda ke kewaye, hakan ya sakani jin kaina tamkar sarauniya a fada. Hatta ga Ummi da bama zama inuwa ɗaya ta yadda makaman yaƙinta gare ni sai dai, gaskiyar da basu sani ba ita ce: Ni fa ba soyayyar Huzaifa ke damuna ba hasalima, ƙaunar Huzaifa a zuciyata kaso ashirinne kacal cikin ɗarai domin kuwa ni na fi yin imani da kuɗi sama da soyayya. Na kan yi amfani da kalmar so ne dan ta fi narkar da zuciyar mai saurarena sama da kalmar taro ko sisi. Da za a raba Huzaifa da arzikinsa kana a ɗauke shi kacokam a miƙa mun shi, to da ko a farfajiyar zuciyata ba zai samu gurbin tsuguno ba ballantana ya kai ga zama.
Duniya ta sauya, babu wata soyayya da take tasiri sai da abunda za a ciyarda soyayyar wannan karatun na koye shi daga mahaifina da mahaifina yana da dukiya da na kasance tare da shi a yau amma rashin abunda zai ciyar da mu ya sa ya tsallake ya barmu ya koma rayuwar mijin Hajiya. Na kan ji babu daɗi idan na tina da abunda ya mana sai dai wani sa'in mutum ya so kansa wannan ma uzuri ne."Amra! Amra!! Tinanin me kike yi ne haka?"
"Ba komai Mama, ina wayata na duba ko Huzaifa ya kirani?"
"Har yaushe za ki ci-gaba da yaudarar kanki Amra? Ki yi haƙuri ki rungumi ƙaddarar rayuwarki hakan zai sa ki samu sauki a ranki"
"Mama Huzaifa mijin mace huɗu ne, muddin zai aureni wallahi zan jira shi ko da kuwa zan kasance ta ƙarshe a cikin matansa"
Ƙwallada ke zuba daga idanuwana sun karya zuciyar Mama!
"Ya isa haka, ki yi addu'a Allah ya baki wanda ya fishi alkhairi".
Jikinta a sanyaye ta fita daga ɗakin. Ni kuwa fuskata ɗauke da murmushi ina mai yi wa Allah godiya da ya bani basirar tsara kalamai yadda na so.*****
"Huzaifa, kwana biyu na kasa gane maka! Baka iya mun hira idan ka zo wajena sannan kuma ko labari nake baka bana ganin karsashi a fuskarka; dan Allah idan na yi maka laifi ka yafe mini.""Sarina ba ki mini laifin komai ba, hasalima ni na miki laifi. Ko za ki iya tina yarjejeniyarmu?"
Zaro idanu ta yi tare da bugun kijinta firgici da tsoro sun bayyana ƙarara a fuskarta gamaiyar ababen biyu ya tilasta cikar idanunta da ƙwalla nan take. Da kyar ta saki laɓɓanta tace masa:
"Kwarai da gaske, tabbas na tina. Kada ka ce mun ka samu!"
"Na samu, wallahi na samu Sarina."
"Na shiga uku! Yanzu wani hukunci ka yanke?"
"Na yanke shawarar rabuwa da ke; kamar yadda ki ka faɗa a baya"
"Kada ka mun haka Huz, dan Allah ka ce mun wasa ka ke yi, wallahi zuciyata tafasa take yi a halin yanzu".
"Sarina, na haɗu da wata yarinta kwanakin baya, na yi iya ƙoƙarina dan ganin na nisanceta sai dai haƙata bata cinma ruwa ba; ma'ana dai na gaza wajen hana zuciyata faɗawa soyayyarta. A halin yanzu ba zan iya hana kaina ba musamman ma da na tabbatar ita ma tana so na"
"Idan har hakane tabbas bani da wani gurbi a cikin rayuwarka ko kuma gidanka, dan haka ka sanar a gida na fasa aurenka dan ba zan taɓa zama da kishiya ba"
"Gaskiya sarina ko da ace bana son wata to ba zan miki alƙawarin za ki zauna a gidana ke kaɗai ba. Kin faɗa mini a baya cewar kin amince da haɗin iyayenmu ne dan babu wata yarinya a zuciyata, kuma duk lokacinda na so wata to ki za ki janye daga maganar aurena. Kina da zaɓi biyu: ki amince da aurena na aureku ku biyun ko kuma ki rasani."
"Na zaɓi rashinka"
"Dama ba kya so na ashe?"
"Ka fi kowa sanin babu soyayya a tsakaninmu"
Tana faɗin haka ta juya ta shiga daki ta barshi zaune a falo.****
Sarina, ita ce 'yar wajen baban aminin mahaifin Huzaifa. Budurwa ce wacce bata yadda da soyayya ba a cewarta to amma fushin da ya bayyana a fuskarta a yau shi ya nuna alamu na ƙwanƙwasar da soyayya ke yi wa zuciyarta.
Miƙewa Huzaifa ya yi kana ya tunkari gida dan ya kashe wutar da ke ci a zuciyarsa.Shigowarsa ɗakinsa ke da wuya ya tadda mahaifinsa na jiransa a cikin ɗakin.
"Abba lafiya kuwa?"
Ya yi tambayar muryarsa na rawa!
"Ba lafiya ba!"
"Me ya faru Abba?"
Ta shi ya yi ya wanke Huzaifa da mari har sai da gilashinsa ya faɗi a ƙasa.
"Huzaifa ni zaka wulaƙanta? Ni zaka watsawa ƙasa a ido? Ni zan baka amana ka ci?...."
Kan ya kuma cewa komai Huzaifa ya durƙusa ƙasa yana mai faɗin...
"Abba dan Allah ka yi haƙuri, wallahi ba zan taɓa maka haka ba"
"Na nawa kuma Huzaifa? 'Yar aminin nawa kace ka fasa aurenta ana saura mako biyu aure?"
"Wallahi ba ni na faɗa mata haka ba, ita ce ta faɗa"
"Ka yi mini shiru sakaran banza! Faɗa mata kana son wata ya fi zafi a zuciyarta fiye da kalmar ka fasa aurenta. Mace tana fuskantar barazanar kishi ne bayan aurenta amma ita Sarina tun kafin auren ka aza zuciyarta bisa garwashi"
"Ka yi haƙuri Abba"
"Abunda nake so da kai shi ne, gobe ka shirya ka je ka bata haƙuri kuma ka bawa iyayenta haƙuri. Aure kuma mun yanke shawarar jibi bayan sallar juma'a za mu ɗaura shi da yardan Allah"Bai jira jin uffan ba daga bakin Huzaifa ya yi fucewarsa daga turakar. Wasu zafafan hawaye ne suka mamaye idanun Huzaifa a hankali ya yi wa kansa matashi da gwiwarsa yana mai kewar mahaifiyarsa da ta rigayemu gidan gaskiya.
Gari na wayewa misalin ƙarfe takwas Huzaifa ya shirya domin wanzar da umarnin mahaifinsa, ƙarar wayarsa ce ta dawo da hankalinsa daga dogon tunaninda ya faɗa. Yana dubawa ya arba da sunan Amra. "Yanzu me zance mata?" ya jefowa kansa tambayar yana mai kama kunkuminsa da hannunsa na dama.
"Hello Amra!"
"Haba Huzaifa, tun jiya nake kira baka ɗaga min waya, me ke faruwa ne?"
"Ki yi haƙuri Amra, ban taɓa soyayya ba sai a kanki, ban taɓa jin ina so na samu 'yanci ba sai a kanki, ban taɓa jin na samu farin cikin da na rasa ba sai da na haɗu da ke Amra, sai dai kash! Za mu rabu tun kafin haɗuwar ta yi nisa; jibi iwar haka ana shirin ɗaurin aurena da Sarina dan haka ki yi haƙuri Ni da Ke a nan labarin mu zai tiƙe"
"Na shiga uku! Dan Allah kada ka min haka Wallahi ina sanka Huzaifa ba zan iya rayuwa babu kai ba, Ni aurenka ba matsalata bane burina na kasance tare da kai ko da kuwa zan jiraka tsawon rayuwata muddin za ka aureni"
Kaɗawar da zuciyarsa ke yi ya sa jikinsa ya yi rauni, ya ajiye wayar a gefensa ya danna amsa kuwwa dan jin abunda Amra ke faɗa, daidai lokacin mahaifinsa ya zo zai ƙwanƙwasa masa kofa ya jiyo abunda ke faruwa a ɗakin, ba tare da ya yi abunda yake nufi ba ya bankaɗa ƙofar ya shiga. Huzaifa ya yi matuƙar razana ganin yadda mahaifinsa ya faɗo masa ɗaki bagtatan. Miƙa masa hanu ya yi alamar bani wayarka, "wace ce ke?"
A razane tace "Amra! Suna na Amra!"
"Amra, da gaske kina son Huzaifa?"
"Eh Abba ina ƙaunarsa"
"To ki bashi lokaci, zan yi bincike a kanki ma'ana tarbiyarki da nasabarki idan har kin can-canci zama surukata to na miki alƙawarin zan aura miki Huzaifa matuƙar iyayenki sun amince; sai dai, daga yau ina so kada ki sake kiransa ku nisanci juna har sai kun ji daga gareni"
Ya gintse wayar ya miƙa Huzaifa yana mai faɗin tashi mu tafi. Rungume mahaifinsa Huzaifa ya yi yana mai sunbantar goshinsa yana yi masa godiya.
"Kada ka gode mini Huzaifa, wannan 'yancinka ne a matsayinka na ɗa namiji wanda Allah ya baka, kana da damar auren mata huɗu. Matsar shi ne ku matasa kun fiye gaggawa a lamarinku bakwa duba lokacinda ya dace kafin ku aiwatar da umarnin zuciyarku ta baku"
"Hakene, tabbas na yi kuskure abba"
"Mu tafi lokaci zai ƙure mana."
"To Abba"*****
Hm in ji mai ciwon baki.
Next In sha Allah.
Ina mai baku haƙurin jinkirinda labarin ke yi kafin ya iso gareku, wallahi ina iya ƙoƙarina kuma a kullum kuna nan a can ƙarƙashin zuciyata in da ba zan iya taɓa mantawa da ku ba.

YOU ARE READING
AMRA
General FictionNa so ace na ci na banza kamar yadda bana bari ta wuce ni. Amra 'yar son banza, laƙanina kenan kuma ina alfahari da hakan.