AMRA P7
('Yar Son Banza)"Anty Amra, wai ina kika ajiye kayan shafe-shafenda Huzaifa ya aiko mana ne?"
"Ba ajiye su na yi ba, ƙarewa suka yi"
"Ban gabe ba! Ta yaya za su ƙare cikin sati guda?"
"Ni ma ban sani ba"
"Kada ki raina mun hankali mana, kawai ki ce mun baƙin halin naki na rowa ne suka motsa"
Ta shi tsaye na yi na ƙare mata kallo nace "har ke kina da hankalinda zan raina?, naga a Ni ya aikowa kayan to meye naki?"
"Ba ake kaɗai ya aikowa ba, kuma ke a su wa da zai aiko miki? Kuma in kina da kara ai abunki namu ne"
"Bana son dogon surutu Ummi, kaya dai sayarwa nayi saboda ina da buƙatar kuɗi"
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Yanzu Anty Amra har son banzan naki ya kai haka?""Wai hayaniyar me ku ke yi ne?"
Ummi ta buɗe baki za ta yi magana na yi wuf nacewa Mama "rashin kunya take yi mun kamar yadda ta saba"
"Wallahi Mama ba rashin kunya na mata ba, kayanda Huzaifa ya aiko mana ta sayar yanzu ko man shafawa bani da shi"
"Subahanallahi! Shin da gaske ne Amra?'
"Mama ina buƙatar kuɗi ne, kuma ƙawayena sun ga na yi kyau shine suka dameni sai na sayar musu ni kuma na sayar musu da wasu na bar na amfani na"
"Ita kuma Ummi ina nata?"
"Ta yi haƙuri idan ya ƙara aiko mini wani sai in bata"
"Kin ji kunya Amra, wallahi Allah ya yi wadaran halinki! Har kin mata kuɗin da kika bayar na tukuici daga jakar Ummi kika ɗauka har dubu ɗaya; kuma yaushe Huzaifa yace kayan naki ne ke kaɗai?"
"Mama duk abunda Huzaifa ya kawo gidannan a sanadina aka kawo shi, dan haka Ni ce ke da iko akan kayan"
"Amra kin san me kike faɗa kuwa?"
"Na sani Mama, na rasa me na yi miki kike azabtar da zuciyata haka; kin mini katanga tsakanina da mafarkina"
"Wani mafarkin kenan?"
"Mafarkin auren mai kuɗi dan na huta na ji daɗin rayuwata mana, tunda ki ka yi magana da Huzaifa bai ƙara kirana ba, kuma ko na kira shi baya ɗagawa sannan baya responding duk wani saƙo da nake tura masa"
"Lallai ya cika ɗan halak mai riƙe alƙawarinsa, Amra dole ne ki nisanci mutanenda baki san da me suka shigo cikin rayuwarki ba"
"Mama Huzaifa da alheri ya shigo rayuwata, dan haka wallahi ba zan taɓa bari ki zama mini ƙadangariyar bakin tulu ba"Sauƙar wani ƙara na ji a fiskata wanda ya yi sanadin zubewata ƙasa kan katifa ina mai ganin tirtsatsin wuta na giftawa ta gabana, gabanin na kai ga fahimtar abunda ya faru muka jiyo sallama a ƙofar gida, muryar ta so ta yi kama dana wanda kunnuwana ke hasashe sai dai ban sani ba ko amon marinda na sha ya taɓa masarrafan sautin majiyata.
"Wa alaikumussalam wa rahamatullahi wa barkatuhu"
Mama ce ta amsa kana ta sanya hijabinta ta nufi ƙofar gidan dan ta ga wake sallama.
Muryarta na jiyo tana ambaton sunan Huzaifa, ai kuwa da hanzari na nufi makewayi na wanke fiskata na dawo na ɗan fara shafa hoda da jan baki a daidai sa'ilinda Mama ta shigo da baƙon yana zaune bisa taburma. Ummi kuwa ta saki baki sai jero kalaman godiya take masa har da alakoron addu'o'in tsari, kariya da ƙarin buɗi.
Ƙarewa kaina kallo na yi gaban madubi ina mai jaddada godiya ga Rabbul izzati wanda ya ƙawata halittata na kasance son kowa ƙin wanda nace bana so, kai ko da na ce bana so ba za a iya ƙi na ba.
"Ban ga Amra ba, bata gida ne?"
Wani irin shauƙin ƙauna ya lulluɓe akwatin zuciyata jin Huzaifa ya kula da ɓacewar kekkewar fuskata duk da fuskar ta yi jawur shatin yatsun Mama sun bayyana a kuncina rangaɗadau kamar lallen amarya sai dai, duk da haka ban yi ƙasa a guiwa ba wajen bayyana kaina a gaban shi.
A hankali na jeho ƙafata daga ɗakin ina mai cewa gani nan ba inda naje, kwatsam na yi arba da ɓawon ayabar dana aje a bakin ƙofar ɗakin, su! na jini ƙasa tamkar daga sama aka jeho ni kunya ta sake lulluɓeni a karo na biyu gaban Huzaifa.
"Wai shin anya za ki yi abun arziki kuwa?"
Zuciyata ta azalzaleni da masifa tamkar za ta fito daga ƙirjina, wani abun takaincin ma sautin iskarda na sake yayin faɗuwar sai da ta karaɗe majiyar kowa da ke wurin.
Next In sha Allah.
YOU ARE READING
AMRA
General FictionNa so ace na ci na banza kamar yadda bana bari ta wuce ni. Amra 'yar son banza, laƙanina kenan kuma ina alfahari da hakan.