AMRA P6

0 0 0
                                    

AMRA P6

Wayata na jawo naga ƙarfe ɗaya na dare (01:00) na yi wata sabuwar miƙa kana na mayar da kaina bisa katifa na kwanta sai dai, idanuna tamkar an ratayesu da fatarsu, sun ki haɗuwa da juna ballantana su yi mun kara na samu bacci. Babu abunda zuciyata bata hakaito mini ba dan ƙoƙarin sanin ko da kaɗan na abunda Huzaifa ya faɗawa Mama ɗazu.

Motsin Mama na jiyo tana alwala tuni na miƙe zumbur na nufi ƙofar ɗakin. Mama ba ki yi bacci ba kema?

Ta ɗago kanta ta kalleni kana tace"Na yi bacci mana, an faɗa miki Ni Ke ce da zan bari gulma ya hanani rawar gaban hantsi har na kasa bacci."

Haba Mama, dan Allah ki faɗamun abunda Huzaifa ya faɗa miki ɗazu wallahi na ƙahu in ji.

Ta yi shiru kamar ke da bakya wurin har sai da ta yi alwala ta je ta yi salla yayinda na yi ƙuru ina jiran tsammani.

"Yanzu saboda asara irin taki Amra ace ki kasa bacci dan kawai ki ji labari, maimakon ki yi sallar kema ki samu falala shi ne ki ka saka ni gaba kamar na miki laifi."

Mama akwai sauran lokaci fa, zan yi sallar idan uku tayi; dan Allah ki faɗamun abunda Huzaifa ya faɗa miki ɗazu.

"Huzaifa ya yi mini maganganu masu kama hankali sannan ya yi amfani da balagar harshe wajen tilastamun sauraronsa, a cikin bayanansa ya tabbatar mini da cewa ba shi da niyyar cutar da mu a rayuwa hasalima ya ɗaura ɗamarar taimaka mana ta kowace hanya iyakar iyawansa sai da, Ni ba zan bada goyon bayan hakan ba Amra."

Meye dalili Mama? Ya ce dan Allah zai yi, to meye matsalar?

"Matsar ita ce bana san alaqa da masu kuɗi. Mafi akasarin lokuta sukan yi amfani da mu talakawa dan cinma burinsu daga bisani su jefar da mu a kwandon shara. Tun da nake a rayuwata ban taɓa sha'awar abunda Allah bai bani ba, na tsaya matsayina dan haka yanzu ma ba zan bari wani abu ya faru tsakanin mu da Huzaifa ba musamman ke da Ummi. Na zubar da hawaye yayinda yake mun bayanin abubuwan da yake so ya yi mana, sai nake mamakin ta yaya wani daban a gefe zai ɗauki nauyin da Mahaifinku ne ya kamata ya ɗauka?"

Na fahimce ki Mama, amma bakya ganin Allah ne ya dubi halin da muke ciki ya kawo mana agaji ta hanyar Huzaifa?

"Wataƙila hakane, amma na fi jin tsoron akasanin hakan. Duk uwa da Allah ya bata 'ya'ya mata dole ta kasance mai duba da lura kana ta riƙa bincike tana nazarin irin rayuwarda yaranta ke yi saboda halin rayuwa. Amra a baya na sha fama da ke saboda ba kya jin magana sam amma tun ranar da kika mun alqawarin za ki shiryu na samu nutsuwa a raina game da ke; ina fatan ba za ki canza ba?"

Ƙasa na mayar da idanuna ina mai jinjinawa kaina game da sakin harshe da nayi na yi wa Mama wannan alƙawarin. ban ɗauki alƙawarin canzawa ba sai da na yi hasashen zama amaryar Huzaifa, ga shi kuma Mama tana so ta canzawa kiɗin rawa ƙarfi da yaji. Yanzu me zan ce mata? Wai anya zan iya ɗaukan nauyin alƙawarin kuwa? Ta yaya zan bari Huzaifa ya kuɓuce mini bayan na shafe tsawon lokaci ina jiransa? Ina, gaskiya da sake, Wallahi ba zan iya rayuwa cikin takauci ba!"

"Wai me kika faɗa ne ƙasa-ƙasa bana ji?"

Ba komai Mama, kawai dai ina tasbihi ne.

"Tasbihi, ke ɗin? Sai ki je ki haɗa da sallah"

Mama Huzaifa mutumin kirki ne fa, sam ba zai baki kunya ba in sha Allahu; ki yarda da shi dan Allah.

"Kin taɓa zaman maƙwabtaka da shi ne? Kin taɓa haɗa hanya da shi a tafiya baƙon wuri? Kin taɓa yin kasuwanci da shi ne?"

A'a Mama, yaushe ma muka haɗu?

"Alhamdulilah, kin yi wa kalamanki alqalanci yadda ya kamata. Tun da baku jima da haɗuwa ba to bai kamata ki bada shaida a kansa ba."

Bakina a zungure ina ƙunƙuni na baro ɗakin Mama, zuciyata na ci-gaba da yi mini huɗuba tana jaddada mini cewar ba za ta iya rayuwar talauci ba.

Gaskiya ni fa ba zan taɓa bari dama ta kuɓuce mini ba, wannan ita ce matsayata.

Next In sha Allah.
Thanks for reading.

AMRAWhere stories live. Discover now