AMRA P8

3 0 0
                                    

AMRA P8
('Yar Son Banza)

Na so na daure zafin faɗuwar amma ina, dole na ce 'wash, wayyo Allah!' yayinda na ji tamkar ƙashin kunkumina ya goce saboda tsananin zafi. Haka suka yi ta yi mini sannu suna nuna alhininsu gare ni, Huzaifa ya matsa ya ce lalle sai mun tafi asibiti dan a yi gwaji a tabbatar da lafiyata lau ban samu gocewar ƙashi ba. Mama ce ta hana faruwan haka cewarta "wannan faɗuwar bata kai aje asibiti ba, mayin zafi kaɗai ya isa. Sakalci ne kawai irin na Amra ya sa kaga take wannan rakin"

Wasu 'yan canji ya ciro ya miƙawa Mama yace a siyamun magani sai dai, mama ta yi ƙememe ta ƙi karɓan kuɗin kazalika ta hanamu karɓa.

Har dare ina jin ƙullin asarar kuɗin nan a maƙoshina har sai da na fara ji tamkar zazzaɓi na faman rufeni.

Sautin dariyar Ummi da Fahad na jiyo wanda na yi imani gulmata suke yi domin kuwa tunda na faɗi suka kasa kore dariya daga fuskarsu.

"Idan kun gama gulmar ku bani ruwa in sha" muryata a kausashe nake maganar!

"Mu fa ba gulmarki muke yi ba, ke dai kawai tunanin kuɗin nan ke ɓata miki rai kike son hucewa a kanmu"
"Fahad wallahi ka kiyayeni ko na maka dukan tsiya"
"da wani ƙarfin za ki dake ni? Ke da sai an taimaka miki ki ke iya tashi"
Suka kwashe da dariya wanda ya tunzurani na miƙe tsaye na nufi ƙofar ɗakin ina balbalin bala'i.
"Au, da ma lafiyarki ƙalau kika sakamu ɗawainiya dake?" ummi ta faɗa.
"Eh lafiyata ƙalau tunda ba ku da tausayi ai gwara na miƙe na taimaki kaina"
"Anty Amra kin san me ya kawo Huzaifa gidanmu ɗazu kuwa?"
"Ban sani ba, me ya kawo shi to?"
Na nemi waje na zauna tare da tattaro dukkanin hankalina na miƙa mata nace ina jinki.
"Dama ko, zuwa ya yi ya sanar da mu...."
"Kul! Ummi kada ki faɗa mata ki bari shi zai sanar mata da kansa"
"Haba Mama, ya za ki katseta muna magana!"
"Idan shi Huzaifan ya so zai faɗa miki da bakinsa, domin kuwa ya ce yana son yin magana da ke kuma na bashi dama dan haka ki shirya zai zo gobe da yamma in sha Allah"
"Dan Allah Mama?, gaskiya na ji daɗi sosai Allah sarki Mamata ta kaina ina ƙaunarki"
"Hm! Amra kenan, ki sauya tunanin da ke kanki da zuciyarki game da Huzaifa domin kuwa hanyar da kuka dosa sam ba ɗaya bane; ina baki shawari ne a matsayina na uwa"

Ban fahimci abunda Mama take son faɗa mini ba ballantana na yi aiki da shi sai dai, har cikin zuciyata na ji daɗin damar da Mama ta bawa Huzaifa na magana da ni kai tsaye. Ta shi na yi na koma kan katifata na kwanta fuskata cike da murmushi ina mai mamakin yadda Huzaifa ya yi nasarar mallake kekkewar mace irina kuma cikin sauƙi.

Kiran sallar farko na tashi na yi wanka na shirya tsaf na ɗauro alwala na jira lokacin salla, ƙarfe shida da rabi na tafi unguwar bolewa gidansu Ummi me lalle, nan take ta fara haɗa kayan lallen, ba a jimaba ta fara zaiyano basirarta ga fatar jikina wanda ganin hakan ya tilastamun yiwa Allah tasbihi ina tsarkakeShi da ƙara tabbatarwa zuciyata shi kaɗai ya can-canci a bautamaSa. ina zaune ƙahuwar yamma ta yi duk ya mamaye ni. Jan ƙunshi da gaurayar baƙi ta yi mini, ƙafafuna tamkar na sauniya kyawun hannayena kuwa ba'a magana dan ko ni da nake kallonsu na kasa ɗauke idanuna daga gare su. Misalin ƙarfe goma na safe na baro gidan lallen, ina dawowa gida na ɗau abincina na ci kaɗan dan ko yunwar ma bana ji. Ummi na tasa a gaba sai da ta yi mini kitso ƙananu tamkar da allura aka tsaga su, Mama dai na ta idanu kawai iya ka ta ce mun 'iska na wahalar da mai kayan kara'.

Tun sha biyun rana na kira Afra a waya nace mata ta zo na haɗata da Huzaifa su gaisa, ai ko ana idar da sallan la'asar sai gata a gidanmu.

Ƙarfe Huɗu na yamma na shirya tsaf tamkar amaryar da ke jiran angonta, ko daya ke ma ai hakan na nan tafe in sha Allahu. Misalin haɗu da rabi na ga kiran Huzaifa a wayata murna da farin ciki kamar ya kasheni sai dai dan kada yace jiransa nake na ƙi ɗaukan wayar a karon farko har sai da ya kirani a karo ja biyu.

"Amra ina zauren gidanku, in da hali ki fito yanzu"

Tattausar muryarsa na tsaya ji tana rasa dukkanin sassan jikina har saida Afra ta ɗan bigeni kafun na dawo haiyacina. A hanzarce na miƙe tsaye na sake duba kaina a madubi na tabbatar da na cika ɗari kafin na fita. 

Jamfa yake sanye da shi fara fat kamar madara ya ɗaura baƙar hula kana ya sana sanye da baƙar takalmi, idanunsa sanye da farar gilashi wacce ta ƙara ƙawata fuskartasa.

"Barka da zuwa,fatan ka iso lafiya?"
"Lafiya lau Amra, yaya jikinki?"
"Da sauƙi, na warware"
"To Alhamdulilah"
"Ga ƙawata nan Afra ku gaisa"
"Malama Afra ya kike ya gida?"
"Lafiya qlau, yaya hanya?"
"hanya sai godiya"
Afra ta dafa kafaɗuna tace "ƙawata zan shiga ciki in jira ki"
Na dubeta na ce haba dan Allah ki tsaya mana kada ki barni ni kaɗai. Afra ta yi na'am da buƙatata da sa bakin Huzaifa.

"Amra, na buƙaci magana da ke kai tsaye dan bana so ki ji saƙon a bakin kowa sai nawa"

Wani farin ciki da ƙahuwar jin ta bakinsa suka mamaye zuciyata, na yi wuf nace masa...
"ina jinka Huzaifa"
Ajiyar zuciya ya yi kana ya karkato da fuskarsa gareni yace...
"an saka ranar bikina Amra, nan da wata biyu za'a ɗaura mini aure da 'yar abokin babana"

Zamewa ƙafafuna suka yi bayan na ji wani irin sara da ya doki tsakiyar kwanyata wanda ya tilastamun dafa Afra dake kusa da ni, "inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" Afra ke maimaitawa hankalinta duk ya tashi ganin ina ƙoƙarin sumewa a hannunta.

"Amra! Amra!! Amra!!!
muryar Mama nake ji daga nisan zango tana kirana, ahakankali na buɗe idanuwana naga Mama a tsaye a kaina cikin tashin hankali da damuwa.

"A ina nake Mama? Me yake faruwa ne? Ina Huzaifa?, Mama, dan Allah ki faɗamun mafarki nake yi, dan Allah ki ce mun abunda ya faru wasa ne ba gaske ba" wasu tagwayen kwalla suka zuba daga idanuwana masu zafin gaske.

"Ba wasa bane Amra, ki yi haƙuri dan Allah, da na san abunda zai faru kenan da ban sanar dake maganar aurena ba"

Jin hakan ya sake tabbatar mun da kunnuwana ba ƙarya suke ba, tabbas ni ce kaɗai nake haukata amma Huzaifa matsayin ƙanwa kawai ya ɗaukeni, na shiga uku ni Amra!.

Next In sha Allah
Thanks for ur time.

AMRAWhere stories live. Discover now