AMRA P5 ('yar son banza)
Written by Fatima Saje.Jikina a sanyaye nake buɗe wasiƙar a lokaci guda ina ƙididde adadin kayayyakin dake jere a bisa barandar ɗakinmu. "Ki karanta mana ki ji mai yace" Mama ta faɗa fuskar bana ce ga yadda yake ba.
*
"Barka da safiya Amra.Na kasa rintsawa a daren jiya, zuciyata cike da damuwa duk da ban san dalilin hakan ba, idan abunda na furta ya ɓata miki rai ki yi haƙuri.
Ga saƙo nan na aiko muku ki roƙa mun Mama ta yafema ƙanwata bisa rashin ɗa'a da tayi, sannan ni ma na san ban kyauta ba al'amura sun faru cikin fushi amma ayi haƙuri dan Allah. Yau zan koma Abuja saboda wani aiki daya bijiromun ba zata, idan kin samu dama ki kirani mu gaisa.
Na barki lafiya."
Ya sake jaddada lamabar wayarsa a cikin wasiƙar.
Zare mun idanu da Mama ta yi yasa dole na karanta wasiƙar da Matsakaiciyar muryar da zata iske majiyarta, kana ta yi ajiyar zuciya ta kai duba izuwa kayan a karo barkatai tana mai yiwa masanin gaibu godiya.
"Ki kira Ummi ku kai kayan ɗakin girki, sannan ki kirashi a waya ki masa godiya sosai amma, daga godiyar kada wani abu ya biyo baya kuma ki faɗa masa kada ya sake aiko mana da komai waɗannan ma sun isa domin bana so mu saba da kyautarsa har hakan ya kashe mana zuciya mu koma zaman jiran tsammani."
"To Mama"
Na amsa mata, na shiga ɗakin domin na tada ummi a bacci.Tare muka fito daga ɗakin muka fara jidan kayan zuwa ɗakin girki. Buhun shinkafa, kwalin taliya, jarkar man ja da man gyaɗa, ledar magi da gishiri, ƙullin albasa da attarugu har ma da naman miya. A gefe guda ga kayan kwalliya, turare dogin riga da takalma, hijabai kai kace kayan lefe yake haɗawa, daga cikin abunda ya yi awun gaba da zuciyata akwai Mamie's spicies dana gani cikin kayan har kwali guda yau nesa ta zo kusa ƙamshin da nake ji gidan Fatima Saje yau za ta jiyo shi gidanmu.
Take na ɗauko itace na haɗa wuta na ɗaura sanwa ina ta murmushi har sai da Ummi ta gane. Sallama muka ji a karo na biyu, nan take na leƙa nace waye? "Ashiru ne, wanda Huzaifa ya aiko ɗazu; na manta da wannan ledar ne shiyasa na dawo." to mun gode, na sake ɗauko ɗari biyar daga jakar Ummi na bashi a karo na biyu; sai dai ya ƙi karɓa duk da matsawar da na yi.
"Muga kayan"
Ummi ta faɗa tana mai buɗe ledar. Mayukan shafawa, sabulai na gyran jiki da maganin duk wasu cuta na fata Organic soap, shampoo da kuma mayukan gashi farin ciki ya mamaye dukkanin zuciyata saboda ina tsaka da buƙatar duk abunda ya aiko mini. A lokacin sanyi babu abunda fatarmu ke buƙata sama da waɗannan kayayyaki dan inganta fata. Wani abun sha'awa shi ne, kayan haɗaka ne na products ɗin Basnaz da Marnaf kayan da nake gani a shafukan sada zumunta ina mafarkin ina ma zan samu, yau sai gasu a gabana na samesu ba tare da sisin kobona ba.Har dare ban kira shi ba, misalin ƙarfe takwas na dare Ummi tace na kira na masa godiya sannan na sanar da shi saƙon Mama. A zuciyata na ji ina son yin hakan sai dai ji nake bai dace da ajina ba na fara kiran namiji a waya, sai dai babu wata mafita face yin hakan. Rangaɗa mini kira Mama tayi na tashi ƙafafuna na harɗewa na isa gareta.
"Kin kira shi?"
Yanzu zan kira Mama, na amsa mata ina mai latsa number a wayata. "Miƙo mini shi mu yi magana" nace to Mama.
Yana amsa kirar tace da shi "mahaifiyar Amra ke magana, mun ga saƙo ina mai godiya a gareka da karamci irin wannan sannan kuma abunda ya faru ya wuce kana ina so duk wata zumunci ko alaqa ta tsaya daga iya haka tsakaninka da 'ya'yana domin bana son hulɗa da masu hali gwara mu rayu daidai ruwa daidai tsaki. Wataƙila kalamai na su maka tsauri amma ka sani, ni uwa ce kare martaba da mutuncin 'ya'yana nauyi ne da ya rataya a wuyana."
Ban san mene Huzaifa yake faɗawa Mama ba naga ta yi shuru tana sauraron sa tsawon ɗaƙiƙa biyu ba tare da ta tanka masa ba. Bal ma hawaye na gani na kwaranya daga sansanin idanunta. Ko me Huzaifa ya faɗawa Mama? Allah kaɗai ya sani.
"Na gode"
Mama ta faɗa sannan ta miƙo mini wayar na ƙara gaba.
Next in sha Allah.
Thanks for reading.
YOU ARE READING
AMRA
General FictionNa so ace na ci na banza kamar yadda bana bari ta wuce ni. Amra 'yar son banza, laƙanina kenan kuma ina alfahari da hakan.