AMRA P4

2 1 0
                                    

AMRA 'yar son banza. P4
Written by
Fatima Saje. Umm Adam.

****
"Wane ne kai?"

Na jeho masa tambayar yayinda ni kaina ban san yaya yanayina yake a wannan lokacinba, domin kuwa na ji kunya matuƙa duk da ni kunya bata fiye damuna ba. A lokaci guda kuma ina cike da mamakin yadda aka yi ya san ankon dake jikina ba nawa bane.

"Sunana Huzaifa, Huzaifa Hafiz Hamman."

"Ta yaya zan amince da wannan suna ta biyun gaskiya ne alhali na farkon ya kasance ƙarya!?"

Juyawa yayi zai shiga motarsa sannan ya juyo yace mini "idan kin shiga, za ki samu amsar tambayoyinki wajen 'yar uwarki Ummi." yana faɗin hakan ya shiga motarsa ya yi tafiyarsa.

Maganarsa ta ƙarshe ta jefa zuciyata da masarrafin tunanina cikin tsaka mai wuya, a ƙoƙarinsu na warwaremun zare da abawa. Na ɗan ɗauki lokaci ina tsaye kana daga bisani na sallamawa Allah komai na shiga gida.

"Kin ga damar dawowa kenan?"

Tambayar da Mama ta jefo mini bayan na roƙa mata aminci a gurin rabbul izzati. Kaina ƙasa nace Mama ina yini? Ta dubeni da mugun kallo tace "baku haɗu a gantalin da kika je bane?"

Ummi ce ta fito daga ɗaki idanunta cike da hawaye tana faɗin "babu wani mutum mai daraja a cikin rayuwata bayan Manzon rahama sai mahaifiyata, sanin darajar iyayena yasa nake kaffa-kaffa da lamuran mutane ina tsare mutumcinsu daidai iyawata domin bana son abunda zai jawo musu zagi ko zargi ta sanadiyata sai dai kash! Yau saboda ke wata yarinya ƙarama da take gadara da girman jikinta da dokiyar mahaifinta ta shigo har cikin gidanmu ta gayawa Mama baƙar magana kana ta yi mana zagi da duk abunda yazo kan harshenta na kalamai. Daga ganin ɗinkin anko kan katifata sai kawai kika ɗauke ba tare da kin san da kayan waye ba. Gyara wata yarinya ta kawo mini, ɗinkin yayi kaɗan; ke kuma kin ɗauka nawane dan ki yi mun abunda kika saba sai ki ka ɗauke.

Na yi ta neman kayan lokacinda aka sake aiko yarinya domin karɓa amma ban gani ba, hakan ya sa wacce ta yo aiken ta zo da yayanta.

Huzaifa shi ne yayanta kuma ya yi alƙawarin zai tsinka ki a gaban jama'a dan ki ɗan-ɗana irin ɗacinda 'yar uwarsa taji duk da na bata nawa ankon dan maye gurbin nata.

Sai dai, mai makon ya cika alwashinsa sai ya fake da baki kulawa a wajen taron, wannan shi ne dalilin da yasa nake muku bahagon kallo a wajen.

Ban tsaya ci-gabada sauraron Ummi ba na wuce ɗaki kai tsaye, da ƙyar nake jan ƙafafuna saboda nauyinda suka mini ga kuma tarin tunanin da ya mamaye ƙwaƙwalwata da zuciyata a lokaci guda. Babban abun takaicin shi ne, rushewar mafarkin soyayyata da shi domin na san ba zai ƙara dawowa ba. Amma zan zo naga wannan yarinyar da tabbas sai na tsinketa da mari; akan matsiyacin ankon biki har za ta yiwa Mama haka!.

Yanke zancen zuci na yi kana na miƙe tsaye na ɗauki buta na yi tsarki na kuma ɗauro alwala dan na yi sallah.

"Idan kin idar da sallan, ki zo ki same ni a ɗakina" Mama ta faɗa tana mai sake murtuƙe fuskarta.

Amsa kiran Mama bayan na aikata laifi ba sabon abu bane a wajena, domin fa ni har yanzu banga aibun a cikin son huta da jin daɗin duniya ba.

Nan na ɗauki hijabina ta sallah na fara jerowa tun daga la'asar har isha'i. Ina gamawa na wuce kai tsaye wajen Mama, ina zuwa na isketa ta kumbura kamar za ta fashe. "Mama gani" na nemi waje na zauna.

"Ba zan gaji da faɗa miki gaskiya ba Amra, waɗannan halaye da ɗabi'u babu inda za su kaiki face ɗakin nadama da ƙuncin rayuwa. Ba wai ina miki mummunar fata bane kawai dai ina nusashsheki game da ɓatawa iyaye ne. Wallahi Amra duk girman mutum, duk azrikinsa, duk maluntarsa, mulki ko sarautarsa ba zai katange shi daga yiwa iyayensa biyayya ba; ballantana ke da baki da komai.

Dalilin son abun duniya mahaifinki ya barmu, ya bi wata Hajiya saudiya tun daga lokacin har yau bai sake tunawa da mu ba yau shekara uku kenan. Saboda haka idan kema ki ka ce za ki bi sawunsa shikkenan ga hanya nan."

Tana faɗin haka naga ƙwalla na sauƙa daga idanunta wanda hakan ya yi sanadiyar narkewan zuciyata. "Ki yi haƙuri Mama in sha Allahu ba zan taɓa barinki ba har abada." Tabbas ba zan bar mahaifiyata saboda kuɗi ba amma kuma ba zan amince da rayuwar talauci ba.

Tashi na yi na koma ɗaki na kwanta sai dai babu alamun bacci a cikin idanuna duk da gajiyar da ta mamaye gaɓoɓina, a hankali na jawo jakar da Huzaifa ya bani, na sa hannu na buɗeta kana na fara ciro ababenda ke ciki kamar haka... Takarda da biro an naɗe su a leda guda, lemo da ruwa, sannan robar abinci cike maƙil da sassan kaza ƙamshinsa kaɗai da ya doki hancina na gane akwai Mimies's spicies a ciki; na kan iya tuna ƙamshinsa yayinda girkin Umm Adam ke ɓararraka a wuta.

Duk da ba'a jin kanmu da kaza amma sai na ji duk jikina a sanyaye bana cikin farin ciki kuma wannan shine karo na farko da nake ji na tamkar ina cikin damuwa ga kuma haushin Ummi da nake ji na nunawa Huzaifa hotona. Rufe kazar na yi na kaiwa Mama dan ta ci, amma abunka da uwa sai ta zaunar da ni tana bani a baki tare da labartamimi yadda take tsananin ƙaunata a cikin ranta.

"Mama na miki alƙawarin ba zan sake ɓata miki rai ba in sha Allahu." Na faɗa har cikin zuciyata ina mai jaddada hakan.

Washe gari da safe misalin ƙarfe takwas (08:00)am, na tashi daga bacci na fito daga ɗaki na iske wani abun mamaki tamkar a mafarki. "Mama waɗannan fa? daga ina? " na tambayi Mama cikin yanayi na mamaki.

"Daga gurin Huzaifa, haka 'yan aiken suke ce; ga kuma takarda yace a baki."

Next in sha Allah.
Thanks for reading. on a user

AMRAWhere stories live. Discover now