19/12/2022
#wattpad🏰🏰🏰🏰🏰🏰🏰🏰🏰🏰🏰🏰🏰🏰🏰🏰🏰🏰🏰🏰🏰🏰🏰🏰🏰🏰🏰🏰🏰🏰
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
Yar sarki 👸🤴💘
1️⃣1️⃣1️⃣
A durkushe suka tarar da momma hannun ta rike a kanta,wani irin mugun ciwo take ji,
Cikin tashin hankali suka karasa inda momma take,
Innalillahi momma meya ke faruwa me yake damun ki?kasa bashi Amsa Tai sai nuna Masa Kai ta ke,
Ciwon Kai?ooh Allah,ku rike ta muje asibiti,...kokarin mikar da ita suka Shiga Yi, Hindu ta dakatar da su.
Karasowa Tai wajan momma tace kina jin jiri? Dakyar momma ta iya ce wa sosai nake ji
Riko hannun mama Tai tace ku zaunar da ita,
Binta sukai da Ido jin abunda tace,
Ranshi amugun bace yace "me kike nufi da mu ajjeta"
Bata ko kula Shiba ta fita waje da gudu, driver dinsu ta kalla tace maza ka bude mun booth,
Bashiri ya bude Mata
Hajiya lafiya de ko,.
Dube duben ta ta cigaba acikin booth din,ya Allah I hope ba wrong car bane.
Aikuwa idanun ta suka fada akai, hamdalah ta saka dakko abun gwajin BP din Tai (Sphygmomanometer) da sethoscope.
Sannan ta koma cikin gidan da gudu,
Karo sukaci ita da shi a bakin kofa,kokarin kauce Masa take Amma ya sake tare ta,
Ke mekike kokarin aikata wa?
Haba mjaay yanzu fa ba lokacin yin fada bane,I have to check on her.
Ke asuwa kenan?
Me as a doctor! Cikin jin haushin shi ta zagaye shi ta wuce ciki da sauri.
Dan dafe kanshi yayi yajaa karamar tsuka oofuuuh Wai fa Ashe itama likita,se yanzu ma na tina, dogon numfashi ya ajjiye mujaheed just focus on your mom ya fadawa kansa sannan shima ya koma ciki.Riko left hand din momma Tai ta nada Mata abun sannan ta maida hankalin ta Kan abun.
Bata wani Jima ba ta cire Mata,cikin Nuna damuwa ta kalli mujaheed jinin ta ya hau sosai pulse inta ma in not stable,
Cikin zallar damuwa yace Shiyasa nace muje asibitikarku damu bawata matsala, tana Shan magani zata samu Sauki,
Zan samu pen da Yar paper?
Miki mata afrah Tai Daman rubutu take abun ya faru,
Ta Karba ta danyi wasu rubuce rubuce,Mika masa Tai,asiyo Mata magunan Nan yanzu ta Sha,
Be Jima ba se gashi ya shigo dasu a hannun sa.Bakin gate din gidan su yayi parking,
Dan numfashi kadan ya sauke,ya sake kallan Wayar hannun sa,tin dazu yake trying Kiran najeeb Amma yakasa samun shi ,gaba daya se yaji hankalin sa ya Dan tashi.
"Jalal"
Seda takira sunan shi sau biyu sannan Adan firgit ya dago yace " na'am"
Tare da kure ta da ido.
Ganin yadda manyan idanunsa suka kureta se gaba daya takasa fadin abun da take son ce masa.
Kina cewa wani Abu?
Emh dama........ sorry Naga ka Dan damu ne, inshaAllah najeeb na Nan lafiya,maybe Sharrin service ne Nima
Tin dazu innai Kira baya Shiga.
Dan daga Kai yayi yace maybe!!
is ohk!
Inna koma Zan neme shi.
Kallan yatsun hannunta yayi da kullin suke Burge shi,sassanyar murmushi ya saka,tare da furta " suna da kyau sosai"
Cikin rashin fahimta tace Mefa?
Yatsun hannun ki! Ya Bata Amsa.Saurin maida hannun Tai cikin mayafi!
dariya abun da Tai ya bashi !Dan Haka har sautin dariyar sa seda taji,
Me yasa Kika boye su?nidin ne bakyaso nagani?
Seeeemaahhhh....cikin narkarkiyar murya wanda yasa ilahirin tsigogin jikin ta mikewa.Sauri Tai takai hannun ta tare da bude kofar motar ta fita,.
Shima fitowa yayi ganin ta fita.Batare da ta jiyo ba ta Fara tinkarar gate dinsu,
Se Kuma ta tsaya,kamar baza ta jiyo ba Kuma seta jiyo,a tsaye ta Ganshi jikin mota ya harder hannun sa biu a kirji!
Kamar baza tace komai ba Kuma se tace prince se anjima!
Ai na zaci baza kimun sallama ba.....
Murmushi Tai ta sake daga Masa hannun alamun bye bye.
Harta juya zata ci gaba da tafiyar ta ya sake Kiran sunan ta da irin muryar dazu,
Saurin lumshe idanunta Tai batare da ta bude su ba kuma ba tare da ta cigaba da tafiya .Matsowa wa yayi so close to her ta bayan ta ba tare da ta sani ba,saitin kunnen ta yace akwai abunda nake son tambayar ki,
a Dan tsorace Tai baya ta Fara tangal tangal kamar xata Fadi saboda batai tsammanin jin muryar sa gab ba,
Saurin taro Ta yayi,watch out...se Kinji wa kanki ciwo.
To bakai kabani tsoro ba..
Nina Baki tsoro?
Umh.
Kama kunnensa yayi yace ohk am sorry!...kin Hakura?
Dan murmushi kadan Tai tace umh!Mee kake son cemun?
Numfashi kadan ya sauke sannan yasa hannunsa daya cikin Aljihu.
Say it jalal...
Kimun Alfarma guda daya?
Wace irin Alfarma kenan?
Just promise me..Inkikai Zan fada Miki koma me nakeso awajan ki.Ohk I promise!
Pinky promise?
Yes Pinky promise.Ina sauraro...?
Kura Masa manyan idanun ta Tai tana son sanin abunda ke tafe dashi...
Shima yasanya nashi cikin nata,yadau seconds kafin ya iya motsa labbarsa...cikin ja Mata Rai da tsoran furta abunda yake son Fadi yace
Seemahh...?
Cikin sauri tace na'am?,
Zaki...Zaki...
Zanyi me?...jalal just say it.
Zaki au..aure...ni?
Cikin bazata taji kalamar a kunnen ta,
Bata tabbatar wa kanta abunda kunnuwan ta suka jiye Mata ba yasa ta sake cewa
Me...me kace?
Sake daura idanunsa yayi cikin anta sannan yasake fadin
ZAKI AURE NI? Da manyan Baki.Cikin shock ta Dan bubbuga fuskar ta Dan tabbatar wa kanta abunda kunnuwan ta suka jiye Mata.
Muryar ta na rawa ta maimaita kalmar...aure...
mood din fuskar gaba daya ya sauya.
Ganin yadda gaba daya ta sauya lokaci daya,
Saurin riko hannunta yayi yace seemah just listen to what am going to say....I know you are confused...Bata Bari ya karasa abunda ze fada ba Ta zame hannunta cikin daure fuska taceLook jalal,banason irin wasan nan
Aure fa...ba abun Wasa bane.
Cikin serious face yace na taba Miki Wasa? Banajin muntaba irin wannan wasan dake
Am serious...
Zaki aure ni?
Wani irin tari ne ya sarke Mata wuya ba tare da ta shirya ba, juyawa Tai da gudu ta shige cikin gida.Kamar walkiyya ya neme ta ya rasa.
Dan Haka yaja kafafuwan sa ya koma cikin mota,hannun yasa ya daki steary motar,cikin jin haushin kansa da rashin sanin abunda ke damun sa ayanzu,
yace I new it... Ni Daman nasan baza ta amunce ba,ita din ba Kamar sauran Yan Mata bane...cikin takaici yace bama ta Bari taji karshen zance ba,tin ba'aje ko Ina ba Tai dumping dina,ba ataba mun wulakanci irin nayau ba,she just walk away...dis is the first time nayi proposing wa mace but what is the result? She dump me and walk away not even a word
najeeb duk lefin Kane.
Kaji Dadi yanzu kajawo mun raini wajan yarinya.Har ya bar unguwar ba abunda yake se uban Mitan da yake ta jero wa Kamar anmasa wahayi dasu.
Najeeb Kamar zeyi hauka Dan bakin ciki,duk motar da suka tsare se ta ki daukan su wasu Kuma suna musu kallan masu rashin gaskiya.
Wani irin haushi da takaicin Amira ne ke ci Masa zuciya da har yake ji Kamar ya shake wuyan ta,ta mutu kowa ya huta.
Cikin harara da tsawa yace kefa na lura ko a gidanku muguwar malalaciya ce ke, ga Dan wahala ki Bari ya tarar Miki mota ki hau,to baze yuyu ba .
Ke Kika kawo mu Nan dan Haka ke Zaki sama Mana mota.
Komawa yayi jikin bishiya ya Dan zauna Wayar sa tin dazu network ya dauke,bubbuga ta yayi ko network ze dawo Amma inaa, gashi ko wallet dinsa be dakko ba.
Amira da gaba daya atsorace take da najeeb tashi Tai ta tsaya bakin titin ta na jiran mota.
Ta Jima tsaye ba mota ba alamun mota,juyawa Tai ta kalli najeeb da yayi kamar bacci yke a shingide.
Dan tabe Baki Tai murya kasa tace nida Kai aga malalaci ai.
Kamar kuwa yaji ta
Yana bude idanu yaga bakinta na Dan motsi,
Keeeeeee me kike cewa
A Dan firkice Amira tace Ni ba abunda nace.
Tsahon minti goma.. Sega motar amalanke dauke da lodin rage,irin motar raken Nan.Saurin tare motar Amira Tai,
Lekowa driver din yayi Ina zuwa Haka?
Malam Dan Allah cikin gari kayi?
Eh
Dan Allah ka taimaka Mana ko Kan kaya ne mu hau.
Cikin mutunci mutumin yace to ku hau muje,Dan wajannan ba lalle ku samu abun Hawa ba
Yatsina fuska najeeb yayi yace muhau Ina kenan?
U mean Ni najeeb...in hau Kan rake the whole najeeb. Kan wannan motar?Comment
Vote
Follow
ShareSorry for the late update 🙏
Like I said the other time...Ina Gama da ciwon Ido so an hanani yawan Danna waya,and my health come first shiyasa bakwa ganin update .Missdynamite7 ✨
YOU ARE READING
yar sarki👑🦋(Book2) King's Daughter
Historical Fictionlove hatred, sacrifice, deception royalty tactics