*Allah ka sa yanda na fara lafiya,na gamashi cikin koshin lafiya*
*BANYI DAN CIN ZARAFIN WATA KO WANI BA, IDAN KINGA YAYI KAMA DA NAKI RAYUWAR TO ARASHI NE*
''' na sadaukar da wannan labari ga dukkan masoyana,Allah ya bar ƙauna one love my fans❤️'''
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*وصلى الله عل النبي الکريم*
01\01\2023*F~ PAGE 1/2*
__________________
Hada-hadarsu suke a babban gidan yarin da ke cikin garin Kano, wani kyakkyawan saurayi ne ɗauke da gudumar bugun dutse, HAFIZ kenan wanda ƙaddara ta kawo shi prison ɗin da ke unguwar Kurmawa a garin Kano.
Zama ya yi yana sharce gumin da ya yi, a kan wani babban dutse dan hutawa, "Ustazu ya dai?" Killer ya faɗa ya na dafa kafaɗar Hafiz, cikin gajiya ya ce "Ibrahim i'm felling thirsty (ina jin ƙishirwa) wanda ake kira da killer ya juya yana son ganin wana ganduroban ne a kusa, ganin, Usman ne ke nufo inda suke da zabgegiyar bulala a hannunsa, "kai su waye anan su ka zauna" ganduroban ya faɗa ya na muzurai, killer ya ɓata rai,ya na juyowa, Ganduroba Usman ya ce " killer ya haka? kar oga ya ganku a zaune ku ci gaba da fasa dutsen mana kun san dai ance dole sai an gama da wannan a yau ko?"
Cikin nuna tsan-tsan iskanci da ƙwarewa killer ya ce " ruwa za mu sha"ganduroba ya juya yaga kowa ya na ta aikinsa da sauri ya ce" nawa za ka ba ni in kawo muku?" Killer ya ce" ba ka da matsala idan mun koma zan sa a baka 2k" da sauri ganduruba Usman ya juya, Hafiz da ya ke tunanin rayuwar da ya tsinci kan shi a ciki, wacce bai taɓa zata ko tsammani ba, hawaye ne ya gangaro daga idanunsa ya na tuno Innarsa da sauran ƴan'uwansa.Killer zai yi magana kenan sai ga Usman ɗauke da ruwa pure-water har guda huɗu, ya miƙawa Killer da sauri ya karɓa ya na faɗin "ustazu ga shi"
"nagode" Hafiz ya faɗa ya na bismillah haɗi da shan ruwan, sai da ya sha guda biyu sannan ya ji daɗi, ya saɓi gudumarsa ya ci gaba da fasan dutse,killer kuma ya juya dan komawa nasa ɓangaren,haka nan ya ji yana son Hafiz tun zuwansa gidan yarin.
wata ƙararrawa aka buga wacce ta ke alama ce ta aje a karɓi kokon safe,
Ganduroba Isya ne ya ke faɗin "minti goma kuje ku karya wallahi idan ku ka wuce sai jikinku ya gaya muku, riga-rigan saukowa daga dutsen suke don zuwa karɓar kokon kar ya ƙare, dan indai baka samu ba dole ka haƙura sai ƙarfe uku na rana kuma.
Cikin nutsuwa Hafiz ya sauko tare da sauran fursinonin da aka yanka musu aiki mai tsanani, su ka nufi ciki.
Rana ya kallah ganin takwas ta wuce ya san lokacin sallar walha ya yi, idan ya ce zai bi layi dan karɓar abun kari ba zai samu damar yin sallar ba, hakan ya sa ya nufi ƙaton drum ɗin da ake ajiye musu ruwa, ruwan jajir da shi duk ƙasa wata molallaliyar bottle ya gani a ƙasa ya ɗauka ya ɗauraye ya zuba ruwan,"kai! kai!! kwashe ruwan za ka yi ɗan iskan mazinaci a haka kamar na Allah nan kuwa shegen fajiri ne" mai kula da su ya faɗa, ya na hararar Hafiz. Mai da ruwan da zai ƙara a jarkar ya yi, ya na matsawa gefe ya fara alwala, anan ya tayar da sallah ya na idarwa ya ɗaga hannunsa ya na addu'a "Ya Ubangijin sammai da ƙassai, ya ubangijin Annabi Muhammadu(S.A.W)Allah ka bayyanar da gaskiya,ya ubangiji na san wannan ƘADDARATA CE, ina godiya a gare ka ya Allah ka san ba ni nayi ba,Allah ka bayyana gaskiya a cikin wannan al'amari, ka wanke ni daga zargin da ake min ya Allah" ya shafa ya na mai tashi, Sani wanda ake kira da kure da kuma killer ne suka zo, ɗauke da koko cikin kofi baƙiƙirin da shi, da wasu manyan ƙosai masu kama da dutse tsabar tauri, a roba su ka ce "Ustazu ga naka"
da Murmushi Hafiz ya ce " ku zauna to mu ci" wanda ake kira da killer ya girgiza kai ya na ɗauko wata ƴar kwallah a cikin wandonsa na ciki,dan duk blue ɗin kaya ne a jikinsu ya buɗe ya shanye abun ciki ya na bubbuga kansa ya ce "ni na ƙoshi Ustazu" ya bar wajen, kure ya zauna dan ganin Hafiz ya ci wani abu, tun da aka kawo shi cikinsu, suka san shi ba fashi ya ke ba, ganin yanda ya ke cikin damuwa, sun so ya sanar da su dalilin da ya kawi shi gidan yari sai dai ya ce "KADDARATA CE"
duk da ba su da imani dan killer bai san komai ba sai kisa,kashe mutum ba komai ba ne a wajensa, ɗaurin rai da rai aka yanke musu, su uku ne a cikin ɗakin duhun da suke aka kawo musu Hafiz, kwarjinsa da cikar haibarsa ya sa suka kasa cutar da shi, ƙauna ce tsakaninsu.
Hafiz da ya ga yanda Kure ya kafe shi da ido ya na ta tunani ya ajiye kokon ya ce "Sani lafiya dai?"ajiyar zuciya kure ya sauke ya ce "Ustazu me ya kawo ka gidan nan, mutane nawa ka kashe da aka kawo ka cikin mu, yau shekararmu biyu a gidan nan babu mahaluƙin da ake haɗamu da shi ba mu aika shi ba,sai kai Ustazu kullum muna son sanin waye kai,am...."
Gudun fursinoni ne ya katse musu hirar lokaci ya yi dan komawa aikin fasa dutse, kamar wasu shanu ana bin su da bulala, kure ya kare Hafiz ya na muzurai dan da a daki Ustazunsu gwara a da ke shi, da sauri Hafiz ya janyo hannun kure su ma su ka hau gudu dan komawa kan aikinsu..........
YOU ARE READING
Ƙaddarata ce
RomanceKowanne ɗan Adam akwai irin tashi jarabawar da Allah yake masa. Malamin addini ne mai tsoron Allah da bin dokokinsa, kaddara ta faɗa masa. Ɗaliba ce a islamiyyarsu, kaddara ta faɗa mata, wannan kaddarar ita ce sanadin shigarsu cikin bakin ciki har t...