19/20

39 0 2
                                    


Last free page

___________________

Gurin da ake register'n Jamb Jawahir ta je, ba mutane sosai yawanci ɗalibai ne  masu son shiga jami'a duk sun zo domin cike form  ɗin jamb ta web site, babu wanda ta kula dan tana gefe ita kaɗai a zaune, "Hajiya me za'ayi miki"ma'aikacin cafe ɗin ya tambayeta ganin ta ware ita kaɗai, " Jamb form nazo a cike min" Jawahir ta faɗa tana tasowa.

"okay 1k ne" ya faɗa ya na nuna mata inda zata zauna, file ɗinta ya karɓa ya na dubawa yana ciccike mata komai, sai da ya gama ya bata ya ce " za'a turo miki da  date da  center'n da zaki je kiyi" ta ce "to nagode kuɗinsa ta ba shi ta tafi.

"To ni zan fita" Baba ya faɗa yana gyara babbar rigarsa wacce ta ɗan kwana biyu, Umma ta ce" to a dawo lafiya Malam" ya fara tafiya kenan Umma ta ce "au na manta Malam gari ya ƙare hakama sabulun wanki" Baba ya ce " haba Aisha meyasa ba za ki canza ba, na sha sanar da ke idan abu ya kusa ƙarewa ki dinga sanar da ni amma sai ki ƙi, to ni yanzu ba ni da kuɗi, sai Allah ya kawo na siyo"
Umma ta ce " a yi haƙuri"
Jawahir ce ta shigo, sakin fuska iyayen nata sukayi Baba  ya ce "har an gama abun?" Jawahir ta ce "eh Baba yanzu ance in saurari ranar da zamuje muyi jarabawar da gurin da zamuyi"
Umma ta ce " to waye zai faɗa miki, ku da kuka gama makarantar kuma?" murmushi ta yi tana cewa "ai ta waya za'a turo" canjin 1k ta ɗauko ta ce "ga canjin" ta na miƙawa Baba.

Baba ya ce "a'a auta ki riƙe ko zaki sayi wani abun kinji"Jawahir ta ce "babu abinda zan siya Baba" Umma ta ce " eh dake Mahaifinki ne kina mai da masa da kuɗinsa,ina jiya kika ce min audigarki(pads) ta ƙare, a siya miki wata?" Baba ya ce " zan tawo da ita wannan kuɗin ki sai duk abinda kike so ki ci kinji auta Allah yayi miki albarka" Jawahir ta ce "nagode Baba a dawo lafiya"
Umma ma ta ce "Allah ya ba da sa'a a dawo lafiya"
Jawahir ta ce "ungo kuɗin Umma ni babu abinda zan yi da su"
Kallonta kawai Umma tayi tana tuno baya kafin wannan abun ya faru da ita, son kuɗi ne da ita ga siyayya kamar me, ita ce siyan madara, aya, kantu, kwakwa, awara, waina, rake dasauran kayan kwaɗayi dai haka.Amma yanzu komai ya fita aranta.

Umma ta ce " a'a ki kashe abinki" ta faɗa a hankali cikin sanyin jiki, Jawahir ta ce " to nagode"ta wuce ɗakinta.
Tun jiya take kiran wayar Zainab amma a kashe,
Tanason sanar da ita zata koma karatu, yanzu ma riƙe take da wayar sai ƙara trying take, amma still dai wayan akashe "ko wayar ta lalace ne" ta faɗa ta na tagumi.

"Assalamu alaikum" wata mata ta shigo gidan tana ta sallama, Umma da ke cikin banɗaki ta yi gyaran murya, matar da ka ganta kaga masifaffiya ta zauna akan kujerar katakon da ke tsakar gidan, Jawahir da ta taso dan ganin waye, taga Hajiya ce, gabanta ne ya faɗi sanin a hannunta Baba ya siyawa Zainab katifa, "wa'alekissalam sannu da zuwa ina wuni"
Lafiya lau,ina Baban naku , tun shekaran jiya ya ce zai zo ya kawo sauran kuɗin amma shiru, ni nace ya aurar da ƴarsa da haƙƙin marayu, magada suna jiran kuɗinsu za'a raba musu gado iyee to ba zan amince ba" ta faɗa ta na watsa hannuwa.

Umma ta fito ta na faɗin maraba sannu da zuwa Hajiya.Haɗe rai matar tayi tana cin magani, ta ce "yauwa ki sanar da shi  idan ba zai iya biya ba, ya dawo min da katifata" Umma ta ce " kiyi haƙuri Hajiya insha Allahu zai kawo"
Tashi tayi ta ce "ki sanar da shi na baku nan da kwana biyu" ta ta shi ta fice.

Jigum-jigum su Umma sukayi Jawahir ta ce " daman Baba bai kaiwa wannan matar kuɗinsu ba?" Umma ta ce" nima wallahi bansan bai kai mata gaba ɗaya ba, sai da na ce wa Malam ayi amfani da sadakinta ya ce a'a hakkinta ne,  ba ita za'a kashewa ba yanzu me ne amfanin haka anzo ana ci mana mutunci akan dubu talatin"

Jawahir da idonta ya ciko da hawaye ta ce "Umma meyasa baku faɗawa Zainab ba, nasan  babu abinda zatayi da sadakinta a yanzu ko inje in karɓo dubu talatin ɗin abar mata ashiri?" da sauri Umma ta ce "a'a ki bari ya dawo sai muji abinda  zai ce" 
Shiru sukayi suna fatan Allah ya rufa musu asiri.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jan 14, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

Ƙaddarata ceWhere stories live. Discover now