5/6

31 2 0
                                    


_________Walida da ta so bin su Baffa prison ɗin don ganin Hafiz, bacci ya yi mata tsiya dan daren jiya bata samu bacci ba sai bayan sallar asuba, tunda cikinta ya tsufa baccinta ya ragu sai da safe ta ke iyayi, wannan dalilin ne ma ya sa su Inna suka yi tafiyarsu.

Zakiyya da Khadija kuwa sun yi jigum a kan tabarma suna jiran ganin dawowar su Baffa ko za su ji labari mai daɗi akan Yayan nasu, Walida ta kallesu ta ce" Ina su Inna kar dai sun tafi?"
Khadija ta ce" ai tun ƙarfe tara suka tafi"
Cikin rashin jin daɗi ta ce" kai dan Allah sai da fa na ce nima zanje inga Yaya" Zakiyya ta ce "kai aunty ke ma fa kinsan Baba ya ce ba za'a je da mu ba tun jiya ai.

Wanka Walida ta yi sannan ta zauna Khadija ta ɗauko mata ɗanwaken da ta ke ci duk safiyan duniya sai kuma ta sha lipton, kaɗan ta ci ita ma ta zauna ta na jiran su dawo daga prinson ɗin.
Yanzu ta dangana  da Mijin nata, tunda ya iya sakinta akan abinda ya shafi Yayanta ta ce "ni nasan wannan KADDARATA CE, Allah ya ba ni ikon kula da abinda zan haifa"
Zakiyya ta ce "amin Yayarmu" shiru ne ya ratsa.

Sai kusan sha biyu saura su Baffa suka dawo, "Assalamu alaikum" sallamar Baffa ta katse musu zaman jigum ɗin da suke.
"Wa'alekumussalam,sannunku da zuwa" duk suka ta shi dan taro su Baffa, kallon fuskarsu kawai su Walida suke yi, ganin ba wata walwala a fuskar su Inna ya sa jikinsu ya yi sanyi. "yauwa sannunku Yayanku ya na gaishe ku ya ce ku taya shi addu'a insha Allah zai dawo gida" Khadija ta washe baki da murna ta ce" Inna   kin faɗa masa nima ina yi masa addu'ar ko?" kai Inna ta ɗaga, Zakiyya ta miƙe ta na ɗebo wa Baffa ruwa, albarka ya sa mata ya sha, Isma'il ya ce "gaskiya Yayanmu ya na shan wahala aunty ya yi baƙi ya rame" sai ya fashe da kuka, ai kuwa gaba ɗayansu su ka hau salati da kuka, Baffa ya hau Isma'il da faɗa, maƙociyarsu ce, Maman Aminatu ta shigo. Ganin yanda suke kuka ta ce "Subhanallahi lafiya Inna?" Inna ta ce " lafiya lau, Yayansu suke wa kukan nan" kai Maman Aminatu ta girgiza cikin jimanta lamarin ta ce" ku yi haƙuri Allah ya na bayan mai gaskiya,nasan    Mu'allim zai dawo da ikon Allah sai maƙiya sun ji kunya" Insha Allahu kuwa Maman Amina" Zakiyya ta faɗa ta na mai  share hawayen da ke kan fuskarta.

Maman Amina ta ce " daman kinga wallahi aiki ne aka ba wa su Sabir ga shi ni kuma ba iyawa nayi ba, na kasa ganewa shi ne na ce ko in turo su idan sun dawo daga islamiyya sai a nuna musu?" Inna ta ce" haba ke kuwa dan Allah na ce ki daina zuwa tambaya ai su Aminatu ƙannensu ne, ki dinga turosu sai su gwada musu kar ki ƙara zuwa tambayar nan nagayamiki" Inna ta ɓata rai, da murmushi Maman Aminatu ta ce"nagode Allah ya saka da alkhairi"
Kallon Walida tayi ta ce " sannu aunty Walida Allah ya raba lafiya" su Zakiyya suka amsa da amin, sallama tayi musu  tana mai jin tausayin ahalin dan suna cikin jarabawa.

Baffa ne ya fito daga ɗaki ya na mai gyara malum-malum ɗin sa ya ce "to ni zan tafi kasuwa na yi azahar a can" adawo lafiya suka yi masa ya tsaya bakin ƙofar gidan ya yi addu'a sannan ya fita.

Kasan cewar rana ta take sosai duk garin an daɗe babu kowa a haka ya gangara ya fito ya sami adaidaita sahu ya hau.

Daidai traffic light (danja)  ta tsaida su, sautin kiɗa ne ke tashi daga wata mota kusa da su, Yusuf da Musty ne a ciki, inda Musty ke driving Yusuf ya na shan lemon panta, kallo ɗaya Baffa ya yi musu ya girgiza kai ya na faɗin "Allah ya shirya" Mai adaidaitan ya ce "amin ya Allah ai Baba wannan zamani sai addu'a ƴaƴan manya ne fa, kaga wancen wanda ya rina rabin gemunsa ɗan Hon.Murtala G.G ne fa" da sauri Baffa ya juyo ya na mai yiwa yaron kallon tsana dan mahaifinsa ne ya dage akan Hafiz ya faɗi wanda yayi faɗin ko hukuma ta yi aiki akansa, haka aka tilasta masa amsa laifin da ba na sa ba ne.
Aka yanke masa hukuncin shekara goma a gidan yari.
Baffa ya ce " Allah ya shirya ƴaƴan musulmai" aka sake su suka wuce.

Musty ya kalli Yusuf ya ce " Guy kasan yau akwai birthday ɗin Mubarak kuwa?" Yusuf ya yatsina fuska ya na mai ce wa" so what dan yau yake birthday kai ni fa natsani guy nan, tun ranar da muka haɗu da shi a club"
Dariya Musty ya yi ya na mai dukan sitiyarin motar ya ce" kai Wallahi ka fiya riƙo akan Yarinyar nan ka ji haushi kenan?"
Yusuf ya fitar da numfashi mai zafi ta bakinsa ya ce" no ka gane tunda naga babies ɗin sun shigo na tama wa ɗayar kawai yarinyar nan ashe baby'n sa ce mtswww" Musty ya kuma kwashewa da dariya ya na nuna Yusuf da hannu, take ran Yusuf ya ɓaci ya kai wa Musty wani kyakkyawan naushi a gefen cikinsa, ƙara ya sa sitiyarin na neman ƙwacewa a hannunsa.
A hankali ya tsaida motar ya na mai riƙe Yusuf.
"ni za ka dinga yiwa dariya ka mai da ni mahaukaci" Musty ya shake wuyan Yusuf su ka hau rigima, kowa zuciya a kusa daga motar su ka fito suna zage-zage ganin haka mutanen da ke gefen titi suka taso dan rabasu, da ƙyar aka rabasu, Yusuf ya hau motarsa ya tafi, yana sai ya koyawa Musty hankali, Musty ya na goge bakinsa inda Yusuf ya naushe shi gurin ya fashe ya na sai ya rama abinda ya yi masa, nan ya tare napep ya hau ya tafi.

Ƙaddarata ceWhere stories live. Discover now