___________________Hafiz ya ce "ni ai bana daga cikin ƴan alfarma shekara goma aka ɗiba min" saurayin mai suna Yushe'u ya ce "Allah sarki ai ko shekara nawa ne indai laifin ba na kisa ba ne ai ka iya fita" Hafiz ya ce "an kamani ne da laifin yin fyaɗen da ba ni ne nayi ba" cike da mamaki Yushe'u ya ce "kamar ya ba kaine kayi ba, bayan ka ce anyanke maka hukunci kaga ai anyi shari'a kenan"
Hafiz ya ce "eh anyi shari'a amma ba bisa gaskiya ba kuma anyanke min hukunci shima bi sa zalunci" hawaye ne ya zubu masa .Yushe'u ya ce " ni dai an kamani ne da motar giya, wacce muka ɗauko tun daga Lagos bansan giya ce a cikiba, ƴan Hisba suka kamani, kuma masu gidana sun gudu, shine aka kawo ni nan ajiya, amma nasan da zarar an danƙosu zan fita , dafa kafaɗar Hafiz yayi ya ce "nayi alƙawarin zan taimake ka, akwai wani lawyer Barrister Sadeeq Hussain Magwan, expert lawyer ne idan ka amince zamu taimaka maka, insha Allah za'a fitar da kai indai kana da gaskiya" wani ganduroba ne ya daka musu tsawa "ba za kuyi mana shiru anan ba, ana magana kuna surutun banza" kallon banza yayi wa Hafiz ya ce " ɗan iska mai hakkewa ƴaƴan mutane kalleka kamar mutumin kirki amma ka kasa riƙe sha'awarka mtswww" sunkuyar da kai Hafiz yayi yana mai jin ciwon kalaman da ake jifansa da su,
shiru suka yi, Yushe'u ya so sanin tarihin Hafiz, aka katse musu hira.Shugaban gidan yarin ya ƙara yi musu nasiha akan su zauna lafiya da junansu.
Sallamarsu akayi kowa ya koma harkarsa.
Hafiz ya miƙe hanyar ɗakinsu jin ana kiransa da "malam, malam!" da sauri Yushe'u ya biyo shi dan jin labarin Hafiz ko zai iya taimaka masa ya fita daga gidan, ganin saurayin ɗazu ne yasa Hafiz tsayawa, cikin sakin fuska Yushe'u ya ce "ɗazu muna magana ba mu ƙarasa ba shine na biyo ka dan mu ƙarasa" take Hafiz ya sauya fuska ya ce "nagode da kulawarka amma ba na buƙatar taimakon kowa" ya wuce ya bar shi tsaye, Yushe'u ya kuma binsa dan ƙara jarraba sa'arsa, ganin ya nufi hanyar da ake ajiye manyan criminals Yushe'u ya ce " ko baka amince da ni ba inaso ka sanar da ni address ɗin ka" kallon baka da hankali Hafiz yayi masa a zuciyarsa ya na zargin ko dai wani planing ɗin ake shirya wa su Baffa aka turo wannan saurayin?
Hannuwansa ya haɗe alamar roƙo ya ce" dan Allah bawan Allah ka rabu da ni kaje kawai ina godiya da nuna damuwanka akaina Allah ya saka da alkhairi" daga nan ya ƙara sauri ya wuce, cikin sanyin jiki Yushe'u ya koma.Bayan kwana biyu da faruwar hakan Hafiz ya saba da gidan yarin hakama maganganun da ake yaɓa masa tun suna masa ciwo a rai har ya saba da su.
Hafiz ne tsaye yana ta bugo ruwa daga borhole ɗin gidan, jiniyar motocin governor suka ji, alamar mai girma His Excellency Muhammad Bature ya kawo ziyara.
Ihu prisoners ɗin suka farayi na ganin tawagar governor sun iso, duk da akwai tazara tsakanin office ɗin shugaban gidan da inda masu laifi suke.
Cikin rawar jiki aka sauki mai girma gwamna da muƙarrabansa ciki har da Honorable Murtala G.G, daga nesa aka tara masu laifukan tun daga nesa Hafiz ya gano Hon.Murtala G.G ji yayi tsanar mutumin ta dawo sabuwa a ransa, dan shine yayi ruwa da tsaki ganin an yankewa Hafiz hukunci, duk wata shaida da hujjoji lawyernsa ne yake kawowa,kuɗi kuwa kamar banza yake ajiyewa ƴan sanda, shi ya ce dole akai kotu dan ya zama izina ga samarin da suke da al'adar yin fyaɗe.Ana ganin shi ne ya tsaya dan kare haƙƙin Jawahir a hukunta Hafiz, daga gwamnan har Hon.G.G duk Hafiz ya tsane su.
Sulalewa yayi ya koma gefe ya dinga kuka yana Allah ya saka masa, masu ƙananan laifuka aka yafewa duk an sallame su, ciki har da Yushe'u wanda yanzu an gano ba shi da laifi, sallamarsu akayi.
Hon.G.G ya manta da wani Hafiz a gidan dan shi ya saba irin haka duk inda yaga anga wani wanda ake zargi indai yaji labari to fa baya bari ayi wani binciken kirki zai shiga gaba domin a yanke hukunci dan so yake ya zama gwamna nan gaba, shiyasa yake ta tara masoya ta hanyar farantawa wasu ya ke kuma ɓata wasu daga cikin talakawa.
YOU ARE READING
Ƙaddarata ce
RomanceKowanne ɗan Adam akwai irin tashi jarabawar da Allah yake masa. Malamin addini ne mai tsoron Allah da bin dokokinsa, kaddara ta faɗa masa. Ɗaliba ce a islamiyyarsu, kaddara ta faɗa mata, wannan kaddarar ita ce sanadin shigarsu cikin bakin ciki har t...