7/8

26 1 0
                                    


_________Tunda Muhsin ya koma makaranta ya ke karatu cikin jindaɗi.
Fitowarsu kenan daga lacture shi da abokinsa Ahmad hannunsu ɗauke da paper wacce ta ke jotter ce, Ahmad ya ce "gaskiya yau mun zaunu tun 8:00am sai yanzu 12:03p.m almost good four hours a lacture ɗaya ni fa shiyasa banason professors ɗin nan su shigo wallahi mtswww" ya ƙarasa maganar yana jan tsaki, Muhsin ya kalle shi kawai,ya ci gaba da tafiya dan yunwa yake ji baiyi breakfast ba ya shiga lacture biscuits da drink ya sha, saboda yana son lacture'n prof.Aminu Ibrahim Ɗiso.

Ganin ya yi gaba ya barshi ya sa Ahmad ce wa "kar Allah ya sa ka kulani, Yusuf ya fika mutunci wallahi" shi ka ɗai yake maganarsa, Mubina Aliyu Musa ce ta  biyo su da sauri ta na kiran Ahmad, juyawa yayi  dan ganin ta nufo shi, cikin sanyin jiki ta ƙarasa ta ce" oh may God where is he?" Ahmad ya taɓe baki ya ce" ya wuce hostel wai ke dan Allah ba za ki rabu da guy ɗin nan ba, sai wahala kike akansa idan kin kamu na faɗa miki kawai  ki sanar da ni in shawo miki kansa" hararar wasa ta yi masa ta ce" kai kafiya zolaya kawai inaso ne na zama friend ɗinku amma naga shi sai shareni yake yi ko banyi masa ba ne oho" Ahmad ya gyara tsaiwarsa domin tsara Mubina ya ce "no ba haka ba ne,  kinsan Allah ko ni ba ko da yaushe yake answering na wa ba, haka Allah ya yi shi bayason magana ko a gidansu idan kinga yana magana to kuwa shi da hand-out ne hahhhh"
Muniba ta ce " that's why i like his, but Insha Allah one day he accepting my request" ta juya dan zuwa wajen friends ɗinta su Nabila tasan daman ba jiranta za su yi ba,tunda ta fito da sauri dan zuwa wurin su Muhsin.

Duk yunwan da yake ikirarin yana ji, sai da yayi wanka car key ɗinsa ya ɗauka dan fita restaurant ya ci abinci, Ahmad ne ya shigo ya ce "ni fa gaskiya ba zan iya rayuwar jami'a ba tare da Mata ba, haba don Allah tunda muka zo  nan ƴan mata suke son mu amma ka ɗauki shegiyar aƙida ka ɗorawa kanka, ga wannan yarinyar Mubina ba fa wai sonka ta ca tanayi ba amma sai wulaƙanta ta kake yi,to ni dai zan yi  friends mata aheeee don ba za ka cutar da ni ba abanza"

Muhsin ya ce" to ni na hanaka haba ka dame ni, idan matan school ɗin nan du ka ke so ka je kayi mana waye ya hanaka mtsww" ya fice ya na jin haushin surutun da Ahmad yasa shi yi, da sauri Ahmad ya bi shi dan shima yunwa yake ji idan ya bari Muhsin ya fita shi kaɗai to kuwa sai dai ya siya da kuɗinsa.
Ya na fita yaga Ahmad ya   na niyar ta da mota, aikuwa da sauri ya buɗe front set ya shige yana hura hanci, murmushi kawai Muhsin yayi ya tada motar su ka bar cikin school ɗinsu.



A kwance suka tarar da shi ya na shan sigari har yanzu bai daina jin haushin abinda Musty yayi masa ba, turo ƙofar room ɗin mommy tayi ta na faɗin " ajiye wannan sigarin" ganin Mommy tare da Musty ya sa Yusuf tashi ya na harararsu Musty ya ja stool ya zauna, shima yana cin magani, abun ne ya ba su dariya kamar wasu mahaukata suka fashe da dariya a lokaci ɗaya, Musty ya je ya rungume Yusuf, suna ɗan bubbuga bayan juna alamar kowa yana rarrashin juna, Mommy ta ce " ni nasan ba za ku iya rabuwa da juna ba, ku daina faɗa a cikin jama'a kunji my Children God bless you"  Yusuf ya ce " okay Mommy" fita tayi ta barsu suna shan sigarinsu.

Rahma ce ta shigo ganin motar da Yusuf ya fita da ita ta hau tsalle dan yau wasu friends ɗinta za su zo, ciki kuwa har da Farrah ƴa ga Hon.Tajuddeen Mai akwai, tunda ta ga hotunan Yusuf a wayar Rahma ta ji duk duniya babu wanda take so sai shi, dalilin da ya sa ma ta dage sai sun zo sun gaida Mommy'n su Rahma kenan.
Da gudu ta nufi ɗakin Yayan nasu dan ba su cika tsoronsa kamar yanda suke tsoron Muhsin ba,duk da Yusuf ɗin shi ne first born a gidan.
Banko ƙofar ta yi "bro dan girman Allah yau kar ka fita wasu classmates ɗin mune zasu zo gaishe da Mommy, shine nakeso  ku gaisa please don't say no my bro" ta faɗa cikin shagwaɓa tana lanƙwashe ƙafa,Yusuf ya ce "wow boys or girls?"  Rahma ta ce "both" murmushin gefe ya yi wanda ya bayyana tsantsar kamar da suke da Muhsin ya ce "okay don't mind dear sai sun zo" tsalle ta yi tana rungume Yusuf ta na faɗin  "thank Yaya" Musty da ya ji inama shi Rahma tayi hug, yaƙe yayi ya ce "hi baby" cikin fara'a ta juyo ta ɗaga masa hannu ta ce " lah Ya Musty how far"  ya na mata wani shanyayyen kallo mai ɗauke da many meaning ya ce "fine where's Teemah?" ta ce "she's in the room" Yusuf  ya ce "oya get out" ya tsani yaga Musty na kula ƙannensa sanin mugun ɗan akuya ne, door ya nuna mata yana haɗe rai,  da sauri kuwa ta fice ta na mita, wani lokacin idan yayi abu kamar Yaya Muhsin, wani wai get out mtsww" ta faɗa ta na yin yanda yayi mata.

Mommy ce ta fito sanye cikin lace black ɗinkin bubu sai ƙyalli take hannunta dauke da wata purse mai bala'in kyau, ganin Rahma ta na surutai ya sa ta ce "ke what is wrong with you?" Rahma ta kwashe da dariya ta ce " no thing Mah, where are you going?" Mommy ta ce " gidan Hajiya Rashida zanje kin san election ya matso akwai wasu ƙauyuka da za mu sa a samo mana ƙuri'arsu" Rahma ta ce "good Mommy dole ma His Excellency ta yi alfahari da ku kuna ƙoƙari" Mommy ta ce "kinci gidanku Excellency ko Dad ɗin ku to ni dan Mijina nake yi" cikin dariya Rahma ta ce " a'a su Mommy ana shan love da Dad hahhh" ta kwasa a guje dan tasan yanzu ta kai mata dukan wasa, Mommy ma ta murmusa ta na wucewa stairs dan fita, driver na tsaye jikin mota ganin hamshakiyar ta fito ya ce " barka da fitowa Hajiya" ya buɗe mata back seat cikin takun isa da ƙasaita ta hau, ya rufe ya zaga ya  kunna mota, maigadi ya buɗe gate suka bar gidan.
Waya ta ke tare da Hajiya Rashida akan ta na hanya, cikin mintina kaɗan suka isa bank road inda gidan Hajiya Rashida ya ke, wasu manyan Mata ne su uku manya-manyan Hajiyoyi dagani sun ci sun tada kai da money, Mommy na shiga suka hau shewa haɗi da kirarin da suke mata " sai ta Alhaji G.G ɗaya tamkar da dubu, da kishiyar gida.... Mommy ta ƙarasa musu "gara ta waje hahhh" ita ma ta zauna akan ɗaya daga cikin kujerun parlour'n.
Homemade ce ta kawo musu drinks, ta zubawa kowa ta fita nan Hajiya Rashida ta fara bayani.......

********
Biki yayi biki a gidan Malam Habib sosai suka fitar da ƴarsu kunya, Shamsiyya babbar ya sai shige da fice take ganin komai ya tafi bisa tsari, Juwairiyya ma ta fito cikin shigar shadda army green wacce take iri ɗaya suka sa su uku har amarya anyi mata simple light make-up wacce sai da amarya ta ce indai Jawahir ba ta yi ba sai ta wanke ta ta, sannan akayi, tayi kyau sosai hakanan ta ɗan saki jiki ana hidima da ita, angwaye ne suka shigo domin gaisawa da ƴan'uwa, ganin haka ya sa Jawahir sulalewa ta koma ɗakin Malam ta yi zamanta.

Tunda suka shiga Kamal abokin ango ya ga wucewar Jawahir ji yayi shima ya sami matar aure,bai taɓa zuwa Kano ba sai jiya, bikin abokinsa  ne ya kawo shi wanda sanadin business online suka haɗu, sai Allah ya sa soyayyar juna tsakaninsu.

Amarya ana ta hotunan tarihi da ango ganin ba ta ga Jawahir ba ya sa taji ba daɗi, ita ma fushi tayi ta ƙyale ta, daman muskila ce tun kafin ayi mata fyaɗe ba ta da hayaniya, yanzu miskilanci sai ya ninka na da.

Da yamma aka shirya kai amarya anan ne Zainab taga tashin hankali ganin da gaske fa gidan za ta bari, ita da Jawahir suka haɗa kai suna ta kuka, sai ga Umma ma nayi haka suka sa wasu ma kuka ana tausayinsu, ganin yanda suka riƙe juna, ya sa aka tafi da Jawahir kai Amarya unguwar janbulu, ƙannen Umma suka saka kowa a gaba dan a dawo, Zainab  da Jawahir anan ma sai da aka yi yaƙi sannan aka raba su, aka dawo gida da Jawahir.
Aka bar Zainab da ƙawayenta cikin kewa.

Bayan an raka ango gidansa, anan akayi addu'o'i da fatan alkhairi ga ma'auratan, sannan aka ɗauki su Amina dan mai da su gida.
Anan ne Kamal yake son sanin wace ce Jawahir, Amina da take zargin ko shima an tsegunta masa abinda ya faru ga Jawahir ɗin ya sa ta ƙi cewa komai, ganin ba type ɗinsu ba ne, a ranta ta na tunanin ƙila irin ƴan iskan ƴaƴan masu kuɗin nan ne dan tun a wajen party taga yanda yake liƙa dollers ta san ba wai irin su Malam Abdullahi ba ne(Mijin Zainab).

"Sai magana nake miki ƙawar amarya kinyi min shiru, ki faɗa min wannan yarinyar da na gani ɗazu ita ma ƙawarku ce ko kuwa?"  cikin ƙunar rai Amina ta ce " dan Allah Malam ka rabu da mu, ko dole sai ka ji ko wace ce, to ƴar'uwatace" Kamal ya yi murmushi ya na juyowa ya ce wa sauran ƙawayen "kunga yanda take min masifa kaina sai da ya sara pls ku ce ta bari" baki su Sadiya suka saki suna kallonsa ganin mugun shagwaɓaɓɓe ne, take Amina ta ƙara yarda da zarginta ba mutumin kirki ba ne (kai Yaya Amina ba'a yanke wa mutum hukunci a haɗuwar farko🤔)

Ganin suna kallonsa ya sa Kamal yayi murmushi gani da shafa fuskarsa, wayar sa ce tayi ringing ganin mahaifiyarsa ce ya sa ya ce"my first love" parking yayi dan amsa wayar, duk abinda yake idan Hajiyansa ta kira shi sai ya bari ya amsa.
Yana yin parking Amina ta fice dan sun shigo unguwarsu da ƙafa za su iya ƙarasawa gida, ganin sun fita ya sa Kamal ya amsa wayarsa, a can Hajiya ta ce "Maddibo ba za ka dawo yau ɗin ba ma?" cikin jindaɗi ya ce " flight ɗin dare zan bi sai 12 zan iso, insha Allah komai dare yau a Abuja zan kwana........

Zinariya ce✍🏻

Ƙaddarata ceWhere stories live. Discover now