__________________
Wani yarrr ta ji ganin handsome ya shigo tare da sallama wacce lips ɗinsa kaɗai ne ya motsa alamar sallama yayi, Farrah ta kuma kwantar da kanta a jikin kafaɗar mahaifiyarta tana jin wani irin shauƙi da soyayyar Yusuf na ratsa jini da tsokan da ke sassan jikinta "bar.....kah.. d..da...zuwa" Hajiya Kursum ta faɗa cikin shacking voice, Yusuf ya zauna yayi balanced akan ɗaya daga cikin royal chairs ɗin dake cikin parlour'n ya ce "barka dai Hajiya kuna lafiya"
Hajiya ta amsa tana sakin fara'a "Alhamdulillah ya su Maman naka, ya kuka sha fama da Farrah"
Yusuf ya sosa ɗan guntun gemunsa brown colour ya yi murmushi ba tare da ya amsa ba.Hajiya Kursum ta ce " kar dai kaima ɗan Honorble ne?" Yusuf ya ce "yes i'm first child of my parent Yusuf Murtala G.G by name"
Mayaudarin murmushi Hajiya Kursum ta saki ta ce "masha Allah, nagode ƙwarai da gaske ai nima inan zuwa mu gaisa da Mommy dan Farrah ba tada magana sai ta Rahma da Ihsan"
Surutun ne ya ishi Yusuf ya miƙe yana yatsina fuska, a tare Farrah da Hajiya suka miƙe, "kai Yaya ba dai tafiya zakayi ba tun yanzu" Farrrah ta faɗa kamar zatayi kuka, Yusuf da yarinyar ta fara hargitsa shi, ya ce "akwai waɗanda suke jiransa ne amma zan dawo wani lokacin"
Hajiya ta ce " humm ko dai budurwarka na jiranka ba, dan da gani zance zaka je" Yusuf ya kuma yatsina fuska ya ce "no Mom ba zance zanje ba, club zamuje so inason in ɗanyi refreshing kaina ne" Hajiya taji daɗi jin da alama Yaron tantiri ne, ba zai yi wahalar shawo kai ba.Da sauri ta ɗauki wayarta ta ce " kayi gaskiya kam, amma sai ka ba ni contact ɗinka, dan idan ka koma in san ka isa lafiya" Farrah ce ta karɓi wayan tana washe baki ta miƙa masa, cikin ƙosawa ya karɓa ya sa number yana fita.
Wani fari Hajiya Kursum tayi tana raya cewar " kifi daga sama gasasshe, irin types ɗin da nake so kenan" Farrah ta ce "Mommy nagaji da yawa"
Da sauri Hajiya Kursum ta ce"ayyah sorry my baby je ki samu rest kinji" Farrah ta nufi sama dan watsa ruwa, bata tare da yunwa dan sunyu dinner a gidansu Rahma.Hajiya Kursum ta hau neman wata number a wayanta, tana sakin murmushi can taji an amsa, ta ce" Hajiya Badi'a albishirinki?"
Wacce ake kira da Hajiya Badi'a ta amsa daga can, nan Hajiya Kursum ta ce "nima na samu wani yaro ɗanyen jini sharaf ingayamiki, sai dai bansaniba ko zai amince"
Hajiya Badi'a da ke cikin parlour'nta tare da wani babban ɗan siyasa mai suna Alhaji Kaita (abokin mijinta,vice ɗin sa) ta sheƙe da dariya ta ce " au yanzu kin yar da makaman wa'azin da ƙalallahu ƙala rasulun kenan?"
Hajiya Kursum ta ce " wallahi Hajiya abun ne na Alhaji ya ishe ni, yau shine waccen ƙasa gobe wancen gari babu abinda yake tsinana mana, ga wannan Yaron yau ɗin nan na fara ganinsa amma duk ya rikitamin lissafi"
Hajiya Badi'a ta ce " ai kawai ki sakar masa masu gidan rana, kinsan naira mai sa ayi dole kiyi ƙoƙarin jan ra'ayinsa da kuɗ.. "ke kinsan irin Yaron kuwa shima iyayensa sun taka leda fa, nasan ba shi da matsalar kuɗi"
Hajiya Badi'a ta ce " haba Hajiya Kursum sai ka ce ba mace ba, ki nuna masa so da kulawa ba Namiji ba ne nan da nan zakiyi ram da shi a tafin hannunki yayi miki yanda kike so, ke yaran nan fa akwai daɗin harka ni babu ruwana da Alhaji ko ya zauna ko kar ya zauna uwarsu ɗaya ubansu ɗaya"
Sun daɗe suna tattaunawa daga ƙarshe sukayi sallama.Farrah da ta gama komai ta hau online, Yusuf tayi wa magana ganin baya kai ya sa ta sauka dan zuwa ga Mommy. Ta fito kenan daga toilet tana shirin bacci ta ji Farrah ta shigo, kallon ƴarta ta tayi cikin riga wacce take iya cibi da wando iya cinya na bacci, masu taushi.
Ta ce " Farrah ba ki yi bacci ba?" Yeah mommy na zo yi miki good night ne" Hajiya Kursum tayi murmushi da shafa kwantaccen gashin ƴarta ta, ta ce " okay bari in shirya in rakaki har bed sweetheart" Farrah ta zauna ta na kallon yanda Maman nata take ta shafe-shafe, kasa shiru tayi ta ce"oh mommy wannan gayu haka, ko dai daddy zai dawo ne cikin daren nan ne?"
Hajiya Kursum ta ɓata rai ta ce " wana daddy'n, kenan ba zan ji yarda kaina ƙamshi ba sai daddy"Farrah da ke dariya ta ce "sorry my mommy kinyi kyau"
Kai kawai Hajiya Kursum ta girgiza ta ce "ta shi muje sarkin magana"
Sai da ta ga Farrah ta kwanta sannan ta ja mata bargo tayi mata good night kiss in her forehead ta ja mata ƙofa ta fita.
YOU ARE READING
Ƙaddarata ce
RomanceKowanne ɗan Adam akwai irin tashi jarabawar da Allah yake masa. Malamin addini ne mai tsoron Allah da bin dokokinsa, kaddara ta faɗa masa. Ɗaliba ce a islamiyyarsu, kaddara ta faɗa mata, wannan kaddarar ita ce sanadin shigarsu cikin bakin ciki har t...