WG-02

971 46 1
                                    


Sai da ta gama rawar sannan ta shiga cikin gidansu ta zarce bandakin da aka hada manyan itace gurin ginashi, ta saka tokar murhu ta goge jikinta tare da bakin gawayi, sai da ta tabbatar jikinta ya yi tass sannan ta dauki ruwan dake cikin kaskon kasa ta zuba tun daga saman gashin kanta har zuwa kafarta, ta saka talkamin danko ta fito bandaki tana daure da gayen ayaba ta shiga dakinta. Wata brown gown ta dauko doguwar rigar da zata tsaya iya guiwar kafafuwanta ta bayyana farare kuma tsala tsala cinyoyinta. A hankali ta yaryarda gashin kanta ya kwanta bayanta, sannan ta fito waje ta nufi wani itacen fulawa ta tsinke fulawar ta laka a kanta.
Daga gurin ta fara ajujuwa tana dariya har ta isa gurin da ruwan saman da aka yi mai kama da bakin kwarya ya kwanta sai ta leka kanta tana kallon kyakkyawar fuskarta, da yadda furen fulawar ya kawata jikaken gashin kanta. Babu madubin duba fuska a kaf fadin garin, idan mace ko namiji suka yi kwalliya ko suka zo ganin fuskokinsu suna zuwa ne a gurin da ruwa ya wanta irin wanda yake aje a guri daya baya motsi su kalli kansu, wasu kuma suna zuba ruwan ne a wani muhalli na dabam su bar shi a ciki a matsayin madubinsu sai kuma ma su amfani da tsafi su ga fuskarsu. Ta cikin ruwan ta yi arba da Eid yana kallonta fuskarsa da murmushi, a take ta juyowa tana murmushi ta kalli saitin inda yake tsaye, babu shi a zahiri domin ya bata a idonta da duk idon dan'adam mai gani, sai dai tana iya ganinsa a cikin ruwan yana kallonta, kyalkyalewa ta yi da dariya mai matukar dadin sauraro da burgewa ta tsallaka ruwan ta mike hanya tana tafiya sai ya mika hannunsa ya kama nata ya tsayar da ita daga tafiyar da yake, wannan karon ta ganshi ido da ido domin ya so ta ganshi din ne, ba a yau ya saba yi mata haka ba, ya boye mata kansa ta yadda sai ya ga dama zata ganshi, ita ma tana daf ta iya duk wani abu da ake da tsafi da zarar ta cika shekara 20, an bata kambun sarautar da aka aje mata tun gabanin haihuwarta.

“Eid”

“Waira... Kin yi kyau... Irin kyau da ya gagarin duk wata yarinya sa'arki, kyau yana zumudi kamin ya ganshi a fuskarka, kina yi ma kyau kyau Waira ke sarauniya ce ta kyakkyawan matan duniya”

Kwayar idonta yake kallo yana karanto mata baitukan da ke kama da waken da zuciyarsa take rubutawa. Fararen idonta masu tsananin farin da ya haddasa sauyawar kwayar bakin idon zuwa blue na zube a cikin nasa, murmushi ta yi irin murmushin dake kirgita duk wani saurayi mai jini a jika, ta cire hannayenta daga nashi ta yi gaba da fara tafiya tana masa magana da yarensu.

“Idan ban yi wanka ba, kana cewa ina da kyau, idan na yi wanka ma kana cewa ina da kyau, ta ya zan yadda?”

Yayi murmushi yana gyara walkin dake kugunsa.

“Saboda idan ba ki yi wanka ba, kina yi da kyau, idan kuma jikinki ya hadu da wanka yana yi ma wankan kyau”

Ta tsaya cak har sai da ya tararda ita suka jera a tare sannan ta kalleshi.

“Ka koyo karatu?”

“An haramtawa duk wani ďan garin Garuk koyon karatun wasu da ba na kasar ba”

“Kai ba gwani ba ne gurin sarrafa halshe”

“Na koyo ne saboda ke, kin taba fada min kina son sabon abu da ba kowa ya iya ba kin tuna?”

“A ina ka koyo?”

Ta tambaya cike da son sani, sai ya dafa kafadarta suka cigaba da tafiya kai kace masoya ne ba yan'uwa ba.

“Duniya tana da fadi Waira, mutane ko cikinta kuma suna da yawa, kowa yana dauke da baiwa da basira, idan kika yi nisa da garin Garuk zaki hadu da wasu jama'a masu saka tufafi ba irin na mu ba, suna kwalliya da kwana a muhallin da baki taba ganin irinsa ba, suna hawan motoci wasu kuma babura...”

Ta dago kai tana kallonta.

“Outa.. Outar... Ooter”

Haka ta yi ta maimaita kalmar mota amman ta kasa hada harufan a daidai balle ta furta kalmar ta fito yadda a yadda ake fadar ta, saboda ba yarenta ba ne, hasali ma bata taba jin kalmar ba. Dariya ce ta subuce masa ganin ta dage sai ta furta sunan Mota kuma ta kasa.

WANI GARIWhere stories live. Discover now