08

490 26 2
                                    

Fitowa yayi bakin gate din gidansu, ya mike hanyar fita daga road din, ko sau daya be juyo ya kalli gidansu ba, not just gidansu even mahaifinsa ya fice masa a rai a yanzu tufafin dake jikinsa ma ji yake kamar ya cire su ya jefar saboda ya same su ne silar mahaifinsa da ya gama yi masa gori ya kwace komai nasa a yanzu.
Ya daukarwa kansa alkawari ko ba zai taba amfani da Atm dinsa ko mota da duk wani abin da ya san ta hanyar mahaifinsa ya same shi ba. Bacin ransa ya ninku akan Maleek zuciyarsa na raya masa komai akan Maleek akai masa, bayan shiga tsakaninsa da friends dinsa yanzu kuma ya shiga tsakaninsa da mahaifinsa.

“Sai na kashe yaron nan”

Ya furta yana jin kamar ace yana gabansa ya saka bindiga ya halshe kansa. Be taba jin tsanar Maleek irin wannan time din ba, duk wani abun dake shiga tsakaninsu be taba kaiwa kololuwa har haka ba sai tsakanin kwanakin nan ba ma kamar yau, da gangan ya daga tsaddadiyar wayar hannunsa kirar Samsung ya buga a kasa ya bita da kafarsa ta ya taka ya rika gurza ta akan titi ba domin komai ba sai dan ya siyata silar mahaifinsa, yana ayyana cewar sai mahaifinsa ya neme shi tun da har ya wulakanta shi har haka, he can't remember when last yayi tafiyar kafa mai nisa irin wannan har ya kai karshen road din be samu abun hawa ba, gashi ya fasa wayar balle ya kira wani daga cikin abokansa su zo su dauke shi duk da yana kallon haka a matsayin wani abun kunya. Unguwace da karamar mota ma abu ne mai wahala ka gani balle kuma napep ko taxi, shi kanshi ya san ya dauko ruwan dafa kanshi, domin tafiya ce zai ci cibi cibi, gashi be san inda zai je ba, garin zai bari? Ko kasar? Ko kuma wani hotel zai kama ya zauna domin vaya son rabar duk wani abu da mahaifinsa ya mallaka balle ya tafi daya daga cikin gidajen mahaifinsa, ko nasa ko ma kamfaninsa, kuma baya son kusantar yan'uwan mahaifinsa gudun kar a kira mahaifinsa a bashi hakuri.

“Hajiya Jamila...”

Ya furta a ransa, he's father Ex-wife, tana matukar nuna masa kauna a duk lokacin da ya rabe ta ko kuma ita ta rabe shi, wannan ya saka duk girman kansa idan yaje Kano sai yaje inda take, kamar yadda take yawan shigowa Abuja ta duba shi.... Sai dai zuciyarsa na raya masa idan yaje can din ma zata iya kiran mahaifinsa ta yi masa magana ko da ya hana ta, shi a yanzu yana son ya tafi inda be san kowa ba kowa be san shi ba, sai dai ya zai yi ya tafi? Ba tare da ya taba kudin da ya same su ta hanyar mahaifinsa ba? Shi ne abun da ya fi tsaya masa a rai, domin tufafin jikinsa ma ya matsu ya cire su balle kuma har ya sake taba wani abun.

Idonsa na akan titi da gidaje amman hankalinsa da tunaninsa ya tafi wata duniyar, sam be ga motar da ta tsaya a gabansa daman hausawa sun ce hankali ke gani ba ido ba, har Nimra ta kusa karaso kusa da shi jikinsa be bashi akwai mai kallonsa, sai dai kamshin turarenta ya dawo da shi daga duniyar da ya tafi ba dan ya tantance mai kalar kamshi ba sai dan turare ya zama wani bangare na rayuwarsa domin shi ne weak point dinsa no matter what happen.

“Hi Buddy”

Ya kalleta with Angry face kamar ita din ce ta yi masa laifi, a take murmushin daya fadada fuskarta ya bace bat kamar walkiya, cike da nuna damuwa ta lake fuskarsa, gushewar murmushinta ya saka shi jin wani iri domin ta zo gurinsa da farincikinta da gwarin guiwa, this is the first time da yaji yana damuwa akan abun da be takama ya damu da shi ba, kuma yana sakewa da abun da be hadade da haduwa da shi ba.

“Miya faru?”

Ya dan sake fuska sai dai ya kasa boye fushinsa, kuma ya kasa kallonta da idonsa dake bayyana bacin ransa karara.

“Alot”

“Zamu iya yin magana akansu?”

Tunani ya tsaya yi, sai ya ji ba zai iya yi mata garda ma ba, ji yake kamar ya dade tare da ita, kamar wata close friend dinsa haka yake jinta.

“Wait ina motarka ya kake tafiya kasa”

“Na bawa Daddy duk wani abu da na mallaka na shi”

Ta saki baki tana masa kallon mamaki.

WANI GARIWhere stories live. Discover now