Kai ta daga sama ta kalli Namra dake tsaye tana kallon duk abun da yake wakana a kasan murmushi kawai ta yi ta maida kanta kasa ta cigaba tafiyar ta har ta shigo cikin gidan, sai da ta duba ko'ina bata ga Ummi ba sannan ta hau sama ta duba dakin Ummi nan ma bata ciki, sai ta zagaya ta inda yar'uwarta take tsaye tana kallon harabar gidan, tun kamin ta karasa kusa da ita ta ce.
“Ummi bata dawo ba?”
“Suna can gurin case din”
“Kirana fa ta yi wai na dawo gida, ta ji abun da na yi miki”
“Na fada mata komai ai, akan wani banzan saurayi zaki wulakanta ni”
Duk maganar da suke Namra bata juyo ta kalleta ba, ita kuma bata fasa murmushi da mamakin halin yar'uwarta ba.
“Kyakkyawa ne ko ba haka ba? Yana da masifar kyau Namra baki gani ba”
“Kyaun ne matsalarki?”
“Yana da kwarjini, yana da natsuwa yana jin kanshi, samarin dake jin kan su ba su cika kula mata ba, domin gani suke kowace mace ba tsararsu ba ce”
Magana take tana murmushi domin ji take kamar yana a gabanta tsaye tana kallonsa. Namra ta juyo ta kalleta.
“Ke wai tsaya ba dai shi kika bawa motarki ba?”
“Mota kawai kika gani? Ke baki ga alamar zan iya ba shi rayuwata ba ma?”
“Love is stupid....”
Ta fada tana jan tsaki, tsabar haushi ma ya saka ta bar mata gurin, Nimra ta yi murmushi domin ita kadai ta san abun da take ji a game da Ameer.
Bata sauko ba sai da ta hango Shigowar iyayenta tare da Yayanta Maleek da kuma Mahmood, kamin ya zagayo ta sauko har sun shigo cikin falon.“Ummi an kama shi?”
Shi ne abun da ta fara tambaya, Hajiya Zahra ta yaye mayafinta ta zauna saman kujerar da ba a isa a saka a gidan wani karamin mai arziki ba tana fadin.
“Abban ku be bari na shiga ciki ba, a mota suka bar ni ban san ya aka yi ba, sai fada yake min wai miyasa na bi su”
Nimra na kallon Abiey ya dankaro mata harara.
“Daga yau kar mu sake fita akan wani issues irin wannan ki dauki mahaifiyarki ku bi bayanmu”
Nimra ta marairaice fuska try to act innocent.
“Ba laifina ba ne fa, ita ta ce sai mun kaita saboda hankalinta ba zai kwanta idan tana gidan nan ba”
“Na fada miki dai, this should be the last, kuma an rufe case din nan daga yau kar na sake jin maganar mun yi solving da mahaifinsa”
Ummi ta kalleshi da sauri tare da mikewa tsaye Nimra da yar'uwarta ma haka, Mahmood da Maleek da suka san abun da ya faru ne kawai ba su yi mamaki ba, ba ma kamar Maleek da hakan yayi masa dadi.
“Saboda me? Shiyasa ka hana na shiga? Yaron ya fi karfin a hukunta shi ne? Taya mutum zai nemi kashe min yaro kuma kace kun sulhunta Ba sulhu nake so ba, hukunta shi nake son ayi idan ya saba yi ana kyaleshi to yanzu ya kai karshe”
Abiey be ce mata komai ba, ya wuce dakinta sai duk suka bishi da kallon mamaki, har sai da ya shige kofar da zata sada shi da bangarensa. Sannan Ummi ta juyo tana kallon Maleek.
“Waye yaron nan ne? Ya fi karfin kowa a garin nan ne? Waye Ubansa?”
Nimra ta dafata tana kokarin kwantar mata da hankali.
“Ummi, Abiey fa ya fiki son yaya tun da kika ga ya bar maganar nan abun ya fi karfinsa ne please calm down”
“Yaron ba a san inda yake ba Ummi, DSS din da aka tura su kama shi sun ce ba su same shi a gidan ba, kuma step mother dinsa ta zo tana kuka ta yi ta ba mu hakuri, ta ce yanzu haka mahaifinsa ya koreshi ya karbe komai nasa saboda abun da ya aikata, kuma mahaifinsa yana can ya fadi ba lafiya”
YOU ARE READING
WANI GARI
General FictionA wani gari, da al'ummarsa basa hada jini da mutanen wajen garin, akwai wata yarinya da alkalamin kaddara yayi mata zane a garin da bata da kowa ciki kuwa har da masu jin yarenta! Garin da babu masu cin irin abincinta babu ma su kalar addininta ball...