BARKA DA SALLAH
Allah ya maimaita mana ya karbi ibadun mu, Ameen.Maleek ya hade carpet din da yayi sallah da shi ya mike tsaye ya juyo ya kalli Mahaifiyarsa dake cikin shirinta na fita.
“Ummi da zaki taimaka ki fita a maganar nan, tsakanina da friends dina ne?”
“Friends...?”
Ummi ta tambaya tana matsowa kusa da shi da wani irin mugun kallo.
“Maleek har kana da karfin halin sake kiran mugayen mutanen nan friends dinka? Maleek kasan abun da abota take nufi? Abota na nufin mutanen da za su tsaya da kai a lokacin da kowa ya guje ka, ku fadi tashi ku tashi tare, ba mutumen da zai cutar da kai ko a hada kai da shi a cutar da kai ba, kamin na haife ka na yi wata ƙawa wanda na gudu da cikina na farko na tafi garinsu na boya, kuma ta bani mafaka a lokacin da nake tsananin bukatar mafakar, na ji ciwo na kwanta asibiti ta kwanta tare da ni da yi jinya ta har na samu sauki, idan na fada mata sirri na ce bana son kowa ya ji ba zata fada ba, wannan ake kira abota, ba mai cutar da kai ba...”
Cikin fada take masa maganar, sai ya jefar da carpet din saman gadonsa ya kalleta.
“Ummi kin taba haihuwa kamin ni?”
A take sai ta ji kamar ta kwancewa kanta zane a kasuwa, tsoron kalar amsar da zata bawa danta Maleek ya maye gurbin bacin ranta.
“Cikinka nake nufi.....”
Ta furta murya na rawa tare da dauke idonta daga barin kallonsa ta juya ta fice daga dakin. Iskar bakinsa ya juya fuskarsa gurin wayarsa dake ringing.
“Dawood”
Ya fada sannan ya karasa ya dauki wayar ya danna picking.
“Hello”
“Maleek ya ne kana lafiya”
Ya fada kansa
“Lfy Kalau for now”
“Muna tare da Abdull zamu zo gidanku yanzu nan”
“No karku zo yanzu, Ummi fada take zan kira ka later”
Be jira cewar Dawood ba ya sauke wayar ya nufo kofar dakin ya bude ya fito, tsaye yayi a stairs din yana kallon mahaifiyarsa dake zaune Namra na rumgume da ita tana kuka.
“Matsalata da ku karamin abu sai ku mayar da shi babba, miye abun kuka a nan kuma?”
Nimra dake tsaye rike da keys din da alamar shigowarta kenan ta watsa masa harara kamar wani sa'anta.
“Ba komai ba ne? A saka maka abun da zai iya zama sanadiyar lalacewar rayuwarka ko ma rasa ran gaba daya? Sannan ka ce ba komai ba ne? Ba laifinka ba ne mu muka da mu da kai”
Ta risina kusa da Ummi ta rika hannunta.
“Ummi dan Allah ki daina zubar da hawayenki a banza, ki daina damuwa da Maleek dan girman Allah, ta so mu je ciki”
Ummi ta mike tsaye Nimra na rike da hannunta ta juyo a hankali ta fara takawa, Maleek kuma ya fara saukowa tare da kawarda fuskarsa daga barin kallon kukan da mahaifiyarsa take yi. Hajiya ta lumshe ido ta hade yawu wannan karon ba kuka take na abun da aka yi ma Maleek ba, kukan marmarin danta Ameer take, ko a wane hali yake ciki a yanzu? Waya yake kula da shi a yanzu? Su waye abokansa? Wacece uwar rikonsa? Tana bashi kulawa kamar yadda danta yake samu? Har yanzu Mr Bashir yana kaunarsa kamar da ko kuma ya sauya? Yana ma raye ko ya mutu?
“Ummi...”
Kamar wacce ta farko daga dogon bachi haka ta bude ido da sauri ta kalli Nimra dake rike da ita, sai ta sake fashewa da kuka ta kwantar da kanta jikin Nimra.
YOU ARE READING
WANI GARI
General FictionA wani gari, da al'ummarsa basa hada jini da mutanen wajen garin, akwai wata yarinya da alkalamin kaddara yayi mata zane a garin da bata da kowa ciki kuwa har da masu jin yarenta! Garin da babu masu cin irin abincinta babu ma su kalar addininta ball...